HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/14/22, 19:05 – Buhainat: Halin Girma

34

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

*******�

Tun da suka dauki hanya babu wani wanda yayi magana a cikin su,
ransa a bace yake matuka. Manne da jikin kofar take, cike da mamakin dalilin
fushin sa haka, a kalla ya tsaya ya fuskanci abinda yake faruwa kafin ya yanke
hukunci haka, abun ma dariya ya so bata, yadda ya jata zuwa cikin motar, lallai
da gaske sojoji akwai su da temper, idan ba haka ba, menene abun tashin hankali
anan? Tana jin sanda suka sauke Musaddik yana masa sai da safe ya amsa da
k’yar, suka ja motar sai gida.

   Motar na gama tsayawa ya balle murfin motar ya
fice ko bi ta kanta be ba, jiki a sanyaye ta fito itama, ta bi bayan sa cike da
mamakin sa. Bata same shi a falo ba, kai tsaye ta wuce bedroom dan rage kayan
jikin ta da suka dame ta, baya dakin kamar yadda tayi tunani, kuma be shigo ba
har ta gama sauya kayan ta fito falon ta zauna tana bud’e wayarta. Ta jima a
zaune a wajen, sannan ya fito sanye da kajaren wando babu riga a jikin sa,
wuceta yayi ya dauki abu a cikin wata drawer a falon ya koma dayan dakin da ya
fito. Ya sake dadewa sosai dan har tayi tunanin ta bishi ta gani sai gashi ya
fito ya doro gajeriyar jallabiya a jikin sa, yana kamshin turaren sa na hugo
boss.

 

“Abincin nan za’a kawo maka ko achan zaka ci?” Ta
tambaye shi bayan ya zauna

 

“No ba zan ci ba.”

 

Sak’alo tayi tana duban sa, yaki ko kallon sashen da take sai ma
fito da waya da yayi yana daddanawa. Tashi tayi ta bar falon ta koma daki cikin
rashin jin dadin abinda yayi mata, wannan ai wulakanci ne, me tayi haka? Ji
tayi hawaye na kokarin zubo mata,  kokarin maida shi tayi tana daga
fuskar ta sama.

   Tana tashi kiran Takawa na shigowa wayar sa, ya
daga yana mikewa tsaye

 

“Barka da wannan lokacin Takawa.”

 

“Barkan ka dai, kuna lafiya ya iyali?”

 

“Alhamdulillah wallahi.”

 

“Toh madallah, alfarma akayi min akan tafiyar da zakuyi,
dalilin da ya saka sunanka ya fito saboda ana bukatar jajirtattun mutane kamar
kai, kuma kai zaka jagoranci tafiyar,  sannan akwai alkwarin karin girma
akan ka bayan an dawo, dan haka nake so ka ajiye komai ka tafi, Allah ya baku
sa’a ku dawo lafiya.”

 

” Amma…” Yace a firgice

 

“A’ah fa! Bana so naji komai Mohd, na jima ina neman
alfarma irin wannan akan ka, komai idan har baka so toh fa an barshi, waya
kawai zan, wannan kuwa takanas ya kira ni mukayi magana na kuma bashi tabbacin
zaka je, toh kayi hakuri kaje.”

 

” Shikenan Nagode Allah ya kara girma, zanyi duk yadda
akace.”

 

” Yawwa, Allah ya taimaka ya baku sa’a, Allah yayi
albarka.”

 

” Amin.”

 

Ya amsa a dunkule zuciyar sa na wani irin suya, wato sai DG ya
riga shi samun Takawa akan maganar ya kuma nemi alfarma yasan Takawa dole ya
amsa masa, me ma ya saka shi wai kin tsayawa yaga Takawan a dazu ya tafi? Ai da
duk haka bata faru ba. Wani abu me ya tokare masa makoshi, ya jefar da wayar a
saman kujerar yana barin falon da sauri zuwa daki.

  Tana zaune a gefen gadon tana tunani ya shigo, ya wuce
wajen da jakar sa take ajiye ya ciro flash din, ya dauki system ya sake barin
dakin. Hada su yayi da dayan na wajen Iman, ya kunna kowanne yayi copying dinsa
akan system din, sannan ya saka su a envelope ya mayar jakar. Tafiyar da zai yi
Itace zata basu kafa wanda har za’a iya samun matsala be samu dukka bayanan da
yake son samu ba, yanzu dai zai damka wa Musaddik flash din guda biyu, ya ajiye
a wajen sa dan sune manyan evidence dinsa idan ya tashi yin abinda ya jima yana
shiryawa.

  Wayar sa da ya jefar dazu ya dauko ya kira Musaddik din,
sukayi magana sannan ya ajiye yana dafe kansa. Zai iya jure komai amma banda
abu biyu, iyayen sa da matarsa, idan har aka samu matsala zai dauki matakin da
ba zai ma kowa dadi ba.

   Tun tana jiran shigowar sa har ta gaji ta hakura,
ta kwanta tana matsar kwalla, bata ga abin fushi ba sam, bata kuma san ta yadda
zata fara bashi hakuri ba, ba wai dan tana ganin ai bata yi laifi ba me yasa
zata bashi hakuri, sai dai ta rasa fuskar da zata iya bashi hakurin.

   Chan cikin dare ta farka bayan bacci ya dauke ta
da k’yar, ta ganshi a gefen gadon yana bacci hankalin sa kwance, ya riga ya
saba mata tun farko tare suke kwanciya, cikin bargo daya amma sai gashi yau,
akan abinda bata da laifi akai,yana fushi da ita. Baccin ne ya kaurace mata
gaba daya, ta dinga tunanin wai dama haka auren yake kenan? Sai wajen asuba
sannan ta samu baccin ya kwanshe ta bayan ta sha kuka ta gode Allah.

   A kanta ya tsaya yana kare mata kallo, yadda ta
kwanta sai ta bashi tausayi sosai, be san me ya hau kansa jiya ba, amma ba wai
haushin ta yake ji ba, bayan ma wayar da yayi da Takawa zai iya cewa ya manta
abinda ya faru, tunanin abinda zai faru idan baya nan shi yafi daga masa hankali
har ya hanashi zuwa ya kwanta sai dare sosai.

  Hannu ya kai ya shafi gefen fuskar ta, ta bud’e idon
tana salati a hankali, ganin shi da tayi a tsaye akanta yana mata murmushi ya
sakata tashi da dan sauri tana gyara jikin ta

 

“Good morning Baby,.”

 

Yace kamar babu wani abu da ya faru, bata amsa ba, sai zuro
kafarta da tayi ta sakko, ta wuce shi zuwa toilet dan ta makara daga ganin
yadda haske ya cika dakin. Hijab ya ciro mata ya shinfid’a mata abun sallah, ya
zauna yana jiran fitowar ta. Ko da ta fito bata kalle shi ba, ta tada sallar
ta, da ta idar ma sai kawai ta kwanta a wajen tana janyo hijab din ta rufe
fuskar ta dashi. Tasowa yayi tsam yayi zaman dirshan a gaban ta, ya janye hijab
din yana dagota, hawayen da ya gani a saman fuskar ta yayi mugun bashi mamaki

 

“Innalillah, kuka? Don’t tell me kuka kikayi tayi the whole
night…”

 

“Ya Salam…Look at your eyes, I’m very sorry, ki yafe min
dan Allah.”

 

Bayan hannun ta tasa tana share hawayen da suka ki tsayawa, ita
kanta bata san na menene ba, kawai tasan she’s weak, tana jin wani irin
weakness a tattare da ita, she can’t take fushin sa a gareta, he’s so nice to
her ko yaya yayi fushi zai bata wahala sosai. Rarrashin ta ya dinga yi da
kalamai masu taushi, har sai da ya tabbatar da kukan ya tsaya, sannan ya
taimaka mata suka bar kasan suka koma saman gado.

 

“Dole zanyi fushi, shi zaman aure dama zo mu zauna ne zo mu
saba, I can equally make mistake, ina da kishi sosai Fatima, ba kuma wai dan
naji a raina wai kin kula shi bane, son da nake miki ya saka, please ki kula
sosai. “

 

” I’m so too. ” Tace bayan ta amsa masa da toh.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button