HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

” Baki komai ba ai, nasan wacece matata, kawai dai…

 

” Me?”

 

” Ashe dai ana so na… “

 

Duka ta kai masa ya goce

 

” Allah da gaske, naji dadi sosai, zan biya bashin duk
tears din da akayi min asarar su, amma kafin nan, zanyi tafiya, karshen week
din nan. “

 

Da sauri ta kalle shi, sai ya kama hannun ta ya fara yi mata
bayani yadda zata fahimta

 

” Kinsan yanayin aikin mu dama yadda yake, ni dinma dai
kawai dai kawai dai, amma wannan karon ba zan iya kin zuwa ba, dole ne dan
akwai Takawa a cikin maganar. “

 

” Dadewa zakayi? “

 

” Uhmm… Ban dai sani ba, amma in sha Allah ba zamu dade
yadda kike tunani ba. “

 

” Allah ya kaimu, ya bada abinda aka je nema. “

 

” Amin ya Allah, an koma strike, akwai driver da zai dinga
kaiki ya jiraki ya dawo dake, hakan nasan zai debe miki kewa, da ina tunanin ko
a chanja school, amma kuma tunda har kun kai 300lv gwara ki karasa ko? “.

 

” Eh hakan yayi. “

 

” Yawwa my wife, yi min murmushi na gani toh.”

 

Murmushi tayi, sukayi dariya a tare suka bar komai a bayan su,
suka fita domin karya kumallo.

 

***Zaune yake a irin kujerar nan me jujjuyawa, kansa sanye da
cowboy hat, sai bakin glasses da ya rufe kusan rabin fuskar, jujjuya yake akai
yana busa sigari, daga bayan sa yara ne biyu majiya karfi, kowannen su ka kalla
zaka tabbatar da zai iya aikata koma wanne irin aiki ne. Knocking akayi, ya
daga kansa yana duban su, kafin ya gid’a kan nasa alamar eh, wanda yake ta bangaren
kofar ne yaje ya bud’e yana matsawa baya, suka shigo su biyu mace da namiji,
kujerun gaban sa suka zauna, ya cigaba da busa sigarin sa ba tare da yayi musu
magana ba, sai da suka dau wani yan dakiku a wajen sannan ya jefar da sigarin
ya saka kafa ya murje ta.

 

“Kun samo abinda ya kamata ku samo din?”

 

“Za’a samo dai, komai yana tafiya according to plan, gashi
zai yi tafiya.”

 

” Tafiya? ” Yace yana kallon su

 

” Eh zaiyi tafiya karshen satin nan. “

 

” Wonderful, opportunity me kyau, lallai lokaci yayi da
kowa zai samu abinda yake so. “

 

” Menene next? “

 

” Tafiyar sa, let me know when he’s gone.”

 

” Me zakayi?”

 

” Matsala ta ce wannan, bani da matsala da cikin gidan ku,
abu biyu ne suka hada mu zuwa uku, a wannan gabar kowa has to play his on part
dakansa. “

 

“Shikenan. “

 

Zaro wata sigarin yayi ya kunna mata wuta, suka mike suka fita,
ya bi su da kallo kafin yayi murmushi. Moh zai yi tasting abinda yaji a lokacin
da ya raba shi da abinda yafi so, shi abu daya ya raba shi dashi, amma shi zai
raba shi da kusan abubuwa uku zuwa hudu masu matukar muhimmanci a rayuwar sa,
ko zai mutu sai ya dauki fansa akansa, sai ya dandana masa bakin cikin da be
taba dandana irin sa ba.

  Mikewa yayi bayan ya gama zukar sigarin, ya tura kofar
wani daki, ya shiga bayan ya kunne flashlight din wayar sa, saboda tsananin
duhun da dakin yake dashi. A gaban mutumin da yake kwance magashiyan ya
durkusa, yana tallafo kansa, sannan ya haske shi da wayar sa da ta kusan kashe
masa ido

 

“Ka kusa samu yancin ka, bayan na tabbatar da na samu duk
abinda nake so a wajen shi wanda yafi ma hatta iyayen ka, kayi hakuri aiki ne
ya biyo ta kanka, kai kadai ne kafi kowa kusanci dashi, dan haka dole ne kaima
ya sha wahala!”

 

“Gwara kayi ta ajiye ni a bakin dakin nan, akan kayi wani
abu akan sa, wallahi wallahi kaji na rantse ma ko? Kuda idan ka bari ya taba
wani abu na jikin sa, sai ya karar da duk dangin ku!”

 

Dariya ya kece da ita mahaukaciyar dariya, ya saki kansa da ya
tallafo ya bige da simintin wajen

 

” Idan yana takama da mulki ne, ko kuma khakin da yake
jikin sa, toh bari kaji, babu abinda ya isa yayi min dan nayi nisan da bazaka
taba tunani ba, k’asar nan tayi lalacewar da su kansu masu tsaron lafiyar taku
ba tsira sukayi a wajen mu ba, shi karamin kwaro ne.”

 

Soma takawa yayi har ya kai kofa, sannan ya juyo yace

 

” Daga yau zuwa gobe amfanin ka zai kare, zabi na ne, na
barka ka tafi, ko kuma na kare rayuwar ka gaba daya Musaddik Izzeeddin!

 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/14/22, 19:05 – Buhainat: Halin Girma

35

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

*******�

Da wuri Musaddik ya iso gidan, dan basu samu haduwa ba tun ranar
da sukayi waya sai yau din da zai tafi, ya riga ya shirya shi kadai yake jira,
yana zuwa ya dauko envelope din ya damka masa a hannun sa

 

“Ka kula sosai dan Allah, idan har lokacin da ya kamata
yayi, ban dawo ba zan fada maka sai ka damka su a hannun Aji! Dan Allah kar
kayi kuskure, ka kula sosai, kai kadai na yarda dakai da wannan amanar.”

 

“In Sha Allah.” Yace yana rik’e envelope din sosai.

   Ciki ya koma, ya barshi a wajen ya tarar ta gama
hada masa jakar sa waje daya, tana gaban jakar ta zabga tagumi har ga Allah
bata son tafiyar tasa, amma kuma dole zata hakura saukin ta daya fitar da
zatayi school, ga ma’aikata birjik an kara karo wasu ma, gate din ma kuma cike
yake da jami’an tsaro da ba dan haka ba, ba zata iya zama a wannan tafkeken
gidan ba.

   Tashi tayi ganin ya shigo,ya kalle ta ya kalli
jakar sai kawai ya rungume ta

 

“Zanyi missing dinki sosai, take care of yourself for me
dan Allah, idan kina bukatar wani abu, reach out to me, idan baki sameni ba,
Musaddik yana nan, nayi miki saving number dinshi kema zan bashi naki.”

 

” Ai babu ma abinda zan nema, akwai komai.”

 

“In case dai.”

 

” Owk tam, nagode. “

 

” Yawwa, muje ki rakani. ” Ya rik’e hannun ta suka
fito har wajen mota, ta tsaya daga gefe bayan ya shiga ya zauna, yayi mata
murmushin karfafa guiwa itama ta maida masa zuciyar ta na rauni, daga mata
hannu yayi har suka fice daga gidan gaba daya.

 

***Abinda ya faru lokacin da Bashir yazo daukar Zeenat bayan
tafiyar Iman, suna barin kofar gidan yana zuwa, adaidaita sahu yazo dan ya
maida machine din wa maishi, aikawa yayi a kirata, dan babu waya a hannun ta,
Mama na jin sakon kiran ta zira mayafi taje wa Zeenat din tana zuwa, ta je ta
same shi a tsaye yana jira ta fito suna magana da me napep din. Be yi mamakin
ganin Maman ba, dan dama yasan ba za’a yi komai ta sauki ba, gaishe ta yayi
taki amsawa, sai ma cewa da tayi tana bud’e hannun ta

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button