HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

“Bani takardar yata.”

 

“Ban gane ba Mama?”

 

“Eh ina nufin ka sauwake mata kaddareren auren ka dan ba
zata koma ba ku karasa kashe ta kai da tsohuwar  matar ka.”

 

” Amma Mama Zeenat tana so na, nima Ina son ta, kiyi hakuri
dai ta fito mu tafi.”

 

“Wanne so? Bayan yaudarar da kayi har kana tunanin tana son
ka?”

 

“Toh ni dai nasan auren soyayya mukayi da ita, kiyi hakuri
ki bimu da addu’a kawai.”

 

“Ba zan hakurin ba, Malam takardar ‘yata kawai nake so ba
dogon surutu ba.”

 

“Ba zan iya sakin ta ba gaskiya, kiyi hakuri kawai.”

 

Sai ya juya ya haye napep din,da sauri ta bishi tana kiran sa,
me napep yaja suka bar kofar gidan. Tana juyowa da nufin komawa gida sai ga
Abba a tsaye a bayanta, ya harde hannayen sa yana kallon ta ransa a matukar
bace, bacin rai da be taba yin irin sa ba tun da aka fara hayaniyar auren
Zeenatun, tsoro ne ya shige ta, dan yadda taga bacin rai a fuskar sa zai iya
aikata komai.

 

“Dan Girman Allah…”

 

Daga mata hannu yayi

 

“Babu abinda zaki ce min, bana son naji komai!

 

Jikin ta ne ya hau rawa, yayi ciki ta bishi tana son yi masa
bayani, ba zai tsaya jin komai ba, ba kuma zai dauki maganar da sauki ba wannan
karon, tayi abinda ba zai mata uzuri ba. A zafafe ya shiga falon yana k’wala
kiran zeenatu, ta tashi jikin ta na rawa har tana yar da dan kwalin kanta da
yake hannun ta,

 

“Me kike yi har yanzu baki tafi ba.”

 

“Uhm.. uhm.. dama…”

 

“Karya kike yi, munafuka!”

 

“Minti biyar kachal na baki, ki fice ki koma gidan mijin
ki, na fad’a miki!”

 

Be jira ya sake jin ta bakin ta ba, ba kuma zai saurari magiyar
da Mama take masa akan dalilin da ya saka tayi abinda tayi ba, yayi gaba kawai
ya shige dakin sa ya rufo.

    Kuka Zeenat ta fashe dashi, da gaske bata son
komawa gidan Bashir, ya zatayi yanzu? Gashi taga wani irin fushi a fuskar Abban
da bata taba gani ba,dama mama so tayi bayan ta kori Bashir din idan Abban yazo
tace shi Bashir din ne yace Zeenat din ta zauna a gida zai yi tafiya ya dawo, daga
nan sai suyi ta matsa mata har ya sake ta, shikenan Abban ba zai zargi komai
ba, amma sai gashi komai ya lalace tun ba’a kai ko ina ba.

 

“Kina da number Bashir ko?”

 

Girgiza kai tayi

 

“Dan ubanki baki haddace number sa ba? Yanzu ya kike so
muyi? Dole ya dawo ya dauki ki ku tafi kafin nasan abinda zanyi akai.”

 

“Mama ni ba zan koma ba.”

 

“Aikuwa sai kin koma, baki ga fuskar babanku ba? So kike
yace na tafi gida shikenan ki rasa wanda zai tsaya miki? Tashi maza ki kira
bashir ga wyata kice ya dawo, idan yaso sai mu san abinda zamuyi.”

 

Kuka ta cigaba da rerawa a hankali, ta karbi wayar ta saka
number tasa ta kira, tayi ta ringing amma be daga ba, ta cigaba da jera masa
kira amma babu alamun zai dauka. Rasa yadda zasuyi sukayi, har goma saura gashi
bata san gidan ba balle idan tafiya zatayi da kanta ta gane. Suna nan a falon
ya fito, ya kalle su sannan ya fice  gaba daya.

 

***Bayan tafiyar sa sai taji gidan yayi mata girma da fadi, ta
kwanta a saman kujerar falon tayi lamo tana jin cikin ta na juyawa sama-sama.
Bacci ne ya dauke ta a wajen bata tashi farkawa ba sai da rana tayi. Sallah ta
fara yi taci abinci sannan ta zauna ta dauko littafan ta na islamiya ta shiga
duba su, tana muraji’ar na baya, tana so ta cigaba da karatun ta ko ita da
kanta ne ta dinga karawa kanta, zatayi amfani da damar duk da sun koma boko
amma ba zata kyale na islamiyya ba, akwai wasu littattafi da take son koya
wanda dole sai dai ta samu manyan malamai su koya mata, amma bata san yadda
zatayi ba. Tana nan zaune yayi mata text message, tayi masa reply sannan ta
cigaba da abinda take har zuwa la’asar, gaba daya sai taji ta rasa ma me
zatayi, sai kawai ta zagaya baya wajen ma’aikatan gidan ta same su suna hira,
suka tashi da sauri suna tambayar ta abinda take so, murmushi kawai cike da
mamakin yadda suke girmama ta take ta zauna a wata kujerar roba, tace zuwa tayi
zaman cikin ya ishe ta, nan fa suka hau murna suka cigaba da hirar tana
sauraren su, a kalla sun debe mata kewa dan bata dawo ciki ba sai bayan da aka
kira sallar magriba.

 

    Washegari ta tashi da murnar zuwa school bayan
tsawon lokacin da sukayi a gida, jin ta take tamkar sabuwar shiga dan wasu
abubuwan ma ta mance su, tasan da yawa duk yau zasu koma saboda dai kowa ya
gaji da zaman gidan. A tsanake ta shirya tsaf, sannan tasaka madaidaicin mayafi
akan doguwar rigar atamfar da ta saka brown da touches din blue, ta dauki jaka
da takalmi da suka shiga sosai ta saka, tayi shigarta ta mutunci ta fito ta
nufi kitchen in da ta hanyar ne ake bi zuwa bq, a kitchen ta tarar da Ummimi,
tana karasa hada breakfast dinta, ta russuna har k’asa ta gaishe ta, ta amsa a
sake tana dudduba aikin.

 

“Zan je school ba jimawa zan ba, idan an gama komai sai a
jera a dining, zanyi bakuwa anjima da rana.”

 

“Allah ya dawo dake lafiya gimbiya, idan kina bukatar abu
ba sai kin zo ba, kira kawai zakiyi ranki ya dade.”

 

“Babu komai karki damu.”

 

“A dawo lafiya, Allah ya bada sa’a.”

 

“Amin.”

 

Tace ta juya ta fita, ta samu driver ya gyara motar, sai kawai
ta fad’a baya tana tuna rayuwa yadda take a shekarun baya, shekarun da basu
gaza biyu ba. Tun da suka isa makarantar duk in da suka wuce sai an kalle su, a
department dinsu kuwa kamar an ga nama ko wata sabuwar halitta, dama labari ya
riga ya karad’e ko ina amma dama ance gani ya kori ji, wasu takanas suke zuwa
su tabbatar da gaskiyar abinda suka ji. Tayi ta zuba ido ko zata ga Zeenat amma
ko me kama da ita bata gani ba, har suka gama abinda zasuyi suka koma gida.

   Tun daga ranar kullum sai taje school din ta
dawo, sai zaman gidan ya zama mata kad’an, duk dare kuma suke shafewa suna
magana da shi a waya, ba wani sosai take jin kadai ta ba, sannan kuma duk sanda
take free da rana ko ta dawo da wuri tana zama ta koya wa masu aikin karantun
al’qurani da ta lura kusan rabin su basu iya ba, kawai rayuwar su sun taso ne
akan hidimtawa gidan sarautar, tun iyaye da kakanni suke a haka har zuwa yanzu
babu wani sauyi da ya samu rayuwar su. Hakan ba karamin dadi yake mata ba, a
kalla ita ma zata samu lada me dinbin yawa.

   Wasa wasa sai gashi yayi sati uku cif da tafiya,
duk sanda ta tambaye shi yaushe zai dawo sai yace mata surprise zai mata kawai,
haka take hakura ta kyale shi, kullum cikin shiri take dan tasan zai iya zuwa
mata bakatatan, wasu magunguna da momma ta bata wanda yawancin su na fruits ne
da madara su take ta faman sha, dan sosai suke mata dadi har ta kanyi mamakin
kanta a lokacin da Mamman ta bata , bata wani ji dadin su kamar yanzu ba.

   Wata rana a cikin ranakun da take zuwa school ta
kai yamma, ta tashi duk jikin ta babu dadi, ciwo take amma bata san takamainai
me yake mata ciwo ba, kamar kar taje school din amma sai ta daure dai, ta
shirya ta kira Ummimi ta rakata, tunda dama sai da yace lallai ta dinga tafiya
da masu rakata amma bata tafiya dasu. Tare suka tafi yau haka nan taji bata son
tafiya ita kadai, suka jirata tayi lecture ta fito wajen biyar na yamma, a
gajiye likis gashi ko ruwa bata saka ma cikin ta ba, kaidar tace bata cin abu a
school tun da ma, sai dai idan zata dade irin haka taci ko snacks ne shima ba ko
yaushe ba, dan mafiya yawancin lokuta rage kudin da Abba yake bata Mama take ta
bata kadan, shiyasa ta koyi yadda zata yi karatun haka,sai kawai ya zame mata
jiki ko yanzu da take da komai bata damu taci din ba

   Da sauri Ummimi ta karbi Jakarta da kayan hannun
ta, ta tayata bud’e mata motar ta zauna sannan ta zagaya ta shiga bangaren ta,
bata lura da su biyu ne a gaba ba, har da wani sai da ya gaishe ta

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button