HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 5

” Allah sarki… Allah yasa lafiya.”

” Lafiya lou, sai godiya. ”

” Ka baro su lafiya?”

” Alhamdulillah. Nagode da kulawa.”

” Ba komai.” Tace tana wasa da hannun ta. 

Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani irin daukewa yaji ganin sa na neman yi. Iman zaune tare da wani suna hira, a cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen ba, sai ganin mutum sukayi a gaban su.

   Wani kallo Moh yayi masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa

“Yaya sannu da zuwa.” Yace yana mika masa hannu, kin bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb ne suka gaisa, ya daki kafadar Khalil din

” Muje ko?”

” Yi gaba ina zuwa.” Yace masa,

“Ok.” Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye

” Iman shiga gida.” Yace a gadarance, ta dago ta kalle shi da sauri, ya hade girar sama data k’asa tamau irin ba wasa din nan.

“My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa gida ban zo na ganki ba, shiyasa na taho nan kai tsaye, zan kira ki anjima ki ajiye waya a kusa dake kinji?”

Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k’yar tace

“Ka gaida gida.” Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen ya hade fuskar sa sosai.

” Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da uban surutu, ku dama talakawa haka kuke, da kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna so, kai kanka kasan ba sa’ar ka bace, ba sa’ar auren ka bace shishigi dai, toh ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja tsumman kafafunka a koma in da aka fito, ka samu daidai da kai.”

” Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani abu bane face fitina, wadatar zuciya itace mutum…” Ya dan matso gaban sa

” Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses, talaka zai baka mamaki, mamakiin da har ka kare rayuwar ka zaka fita daga cikin sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu.”

” 1,2,3!” Sai na jika.

Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin gidan yana jin yanzu ba sai anjima ba, zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za’a yi a bawa dawa.

**A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace

“Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka.”

“Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye, kana ganin sa kaga mara gaskiya, wa ya sani ma ko dan boko haram ne da wannan uban kasumbar, amma baka damu ba kayi tafiyar ka, hakan ba daidai bane.” 

Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi,

” Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?”

” Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina bansan adadin sa ba, zan iya komai akan na sameta, dan haka ba zan iya jure ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan da ya nuna alamun rashin gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen Gaji ayita ta kare.”

” Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin taka, na rasa dagiya irin taka, bayan maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai taba yiwuwa ba.”

” Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a musulunci da ya haramta min auren ta, na daya ni ba muharraminta bane tunda ita din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan dalili mara tushe?”

” Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma idan har ina numfashi ba zamu hada jini ba wallahi, ga mata nan bila adadin, me yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine daidai da matsayin ta, inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta saka yayana samun yan Uba!.”

” Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan karon zabin raina zan bi, zanje na samu Gaji na sanar da ita, gwara kowa ya sani a san me yakamata ayi.”

” Khalil!”

Ta k’wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa tayi kara, ya tsaya chak jin layin da yake ajiye numbers din manyan mutanen sa ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a wayar, ya daga da sauri yana daidaita numfashin sa

” Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci, za’a neme ka idan bukatar hakan ta taso.” Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya dafe bangon da yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin sa, maganar promotion dinsa ma ake idan har ya kammala wannan assignment din da ya kawo shi Kano, shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?

” Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya shiga coma

????????????????????

*_LAST BONANZA_*

*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*

*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*

*_za’a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*

*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*

*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

SAIKU TURA SHAIDAR BIYA

08184017082

GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU

09134848107

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button