INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

Suna Isa gida a gate ta ajiyeta batareda tashiga gidanba ta juya ta komawarta.

Inayah na shigowa gida a Palo ta tadda Dr farhat tazo sunata fira da Haj umma
Umma yaganah Kuma tana kitchen yau da ita ake aikin abincin sbd kwana biyu bataiwa MAJEED abinci da kantaba.

Da mamaki Inayah ke kallon yanda har suka Saba a wuni daya daga zuwan Dr farhat din.

Gaisawa sukai tana tambayar Dr farhat dalilin zuwanta tace Haj umma tasake zuwa gaidawa da Rana sbd jiya darene Basu gaisa da kyauba.

Dakinta ta wuce tayi tube tayi wanka da sallah ta fito sanyeda doguwar chiffon gown Mara nauyi kanta daure da silk scarf.

Tunda ta fito itama kitchen ta nufa gurin umma yaganah acan Tasha cornflakes sbd bata iya cin birabisco ba shi sukai da Rana.

Da ita aka qarasa aikin tasaka hannu duk da bawani aikin ta iyaba bayan wanke plates da cups sai dafa tea shima Dan Abbinta Nasha sosai yasa ta iya Dole.

Daki Takoma ta sauya kayanta sbd batason kamshin girkin dasukeyi.

Har dare Dr farhat na gidan da ita sukai dinner tareda Abbi dashima ya danyi mamakin sabonta da ummansa daga zuwa.

Gurin cin abincinma haka dai umma yaganah da Inayah suka Zama Yan kallo har aka gama kowa ya tashi.

Da Dr farhat Zata tafi har mota ta rakata ta wuce sai yabon Haj umma takeyi itadai Inayah batace Mata komaiba akan aurenta da Kuma Dr farhat din Bata saniba hakama Haj umma Bata Sanar mataba.

Kasa bacci tayi Saida ta fadawa Neesah zuwan Dr farhat sukaita maganar kafin ta kwanta.

Washe gari Abbi Bai tashi da wuriba Dan haka ta wuce
Kuma acan ta tadda umma Hadiza Saida suka gaisa kafin ta wuce.

Yauma tana dawowa Dr farhat na gidan yau Kuma wai BP din Haj umma dinne yahau tazo dubowa.

Haka takuma wuni dasu sai dare ta wuce.

Ahankali ahankali Dr farhat ta maida gidan nasu gurin zuwa fiyeda yanda take zuwa adah,

Tayi sabo da Haj umma sosai ba laifi Dan kuwa Haj umma najin dadin yanda take zuwa duba BP dinta akai akai Wanda Kuma a Yan kwanakin tagano irin son da Dr farhat kewa MAJEED sbd hatta kulawar datakewa Inayah Mai girmace duk sbd MAJEED
Shikuma baimasan tanayiba.

Ta bangare Daya Inayah kwata kwata yanzu Bata wani gane kan Abbinta sbd dukkanin kulawansa Takoma kan Haj umma sbd kwana biyun batajin dadin BP dinta sai hawa yake Yana sauka.

Tun suna mamaki itada umma yaganah harsun koma Yan kallo Danma umma yaganah tana kokari sosai gurin dannarta da hanata magana,.

Duk tabi Takoma sukuku batada walwala koyaushe a sanyaye take Dan yanzu koyaushe idan dai Abbi na gida to Yana tareda Haj umma wadda yanzune tasan tana tareda kaunar danta tunda ya maida hankali sosai akanta.

Ganin hakan yasa Inayah ke dadewa gurin aiki sosai sbd gidan ba Dadi tunda Abbinta baida lokaci sosai.

Hadiza kuwa ganin tana samun ganin Inayah a asibiti yasa kusan duk bayan kwana daya saitaje gurin Inayah asibitin su jima suna magana
Da hakan tafara sabuwa da ‘yarta tunda dama Inayah bamai hayaniya ko riqe Abu bace
Ba jimawa tayi sabo da mutum sbd sanyin halinta.

Ahankali umma Hadiza ta fahimci abinda ke damun inayah na kishin Abbinta da kowa karya fita kusanci dashi
Hakama Sam wannan auren nasu tasan idan akabi ta MAJEED kila ahaka zasu qare amatsayin uba da ‘ya.

Cikin dubara ta bawa Inayah shawaran ta fadawa antynta Hafsat abinda yake faruwa.

Dayake anty Hafsat tayi tafiya jiya tadawo aikuwa da farin ciki ta karbi shawarar.

Tana dawowa gida wanka kawai tayi tayi sallar la’asar tayi zamanta adaki zubbi takawo Mata noodles data saka ta dafa Mata da sausage.

Wayarta ta fidda ta Nemo numbern anty Hafsat ta saka Mata Kira.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/8, 9:55 AM] Sweet sis: 50
Arewabooks@Mamuhgee
Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa”

Dr Inayah majeed Yar gatan Abbinta Kuma amaryar Abbinta..”” ta qarasa zancen da Yar dariya.

Sanyi jikin Inayah yayi tana Jin dadin kirarin Amma Kuma duk wannan yanason kauduwa.

A sanyaye tace”

Anty Hafsat Yaya gida?
Ina my sweet Siyama?

Lfy kalau Inayah,
Ya kike?
Yasu umma yaganah da hajiya?
Ya abbin naki Kuma?

Bata tsaya amsa gaisuwar yasu umma ba tace”

Anty Hafsat Abbina ya canja sosai zuwan Haj umma
Kuma umma yaganah ta Hana nayi magana
Ni gaba daya Abbina yafara Zama kaman na nawaba.

Umman Dr Abdul tace na sauya bangaren Mata
Ni banganeba Anty Hafsat kizo gidan kigan yanda muke yanzu duk ba Dadi,

Ga Haj umma komai nayi saitace shiriritata da shirme kawai na iya.

Yanzu itace Mai kulawa da Abbi fa,
Umma yaganah ma yanzu Takoma Yar kallo abinci kawai take Masa.

Nidai anty Hafsat wlh bazan iyaba
Ina kallo Abbina ya Dena ji Dani kaman da
Bayan umman Abdul tace kamata yayi matsayina ya ninku tunda matsayina biyu agurinsa.

Numfashi anty Hafsat ta sauke tana jinjina zantukan Dan duk da kusan a shagwabe da damuwa Inayah ke fadan zancen idan ta fahimta Haj umma batai na’am ba haryanzu da Inayah a rayuwar AA MAJEED barema ta dauki auren da mahimmanci.

Wani numfashi takuma sakewa tana ajiye ruwan data kawowa CM ta juya ta fice daga palonsu zuwa dakinta Dan bazataso yaji zancen nasuba.

Tana Shiga daki ta zauna bakin gado tana cewa”

To kodai kina Mata abinda baimata bane Inayah?

A sanyaye tace”

Wlh anty Hafsat bana Mata komai
Kuma Ni bandamu data kaunaceniba
Nidai Abbina nakeson ya koma yanda yake kada ya rage ji dani.

Inayah duk wannan abin na tabbata Koda qwayar zarra kaunarki da matsayinki a zuciyar Abbinki Bata raguba
Bama Zata taba raguwaba qaruwa zatayi sbd har Koda yaushe kece kaman strength dinsa.

Kawai dai inaga aurenku ne Bata aminta dashiba sbd ganin kaman bazaki iya kalawa da AA MAJEED dinba kinyi qanqanta….

Aikuwa wlh Ni inason auren yanzu bazaa rabani da Abbi ba,
Ko shima Ni Zan fada Masa inason aurena bazan rabu dashiba.

Da mamaki anty Hafsat tace”

Yanzu Kuma kinason auren kenan?
To kinason auren yanzu harzaki tsaya kina kallo auren na Neman fara rawan tun baigama tsayuwa ba,

Wannan rashin amintar da Haj umma tayi kome zai iya faruwa
Dan kuwa ko auren be rabuba MAJEED Kam zai iya samun matar dazata kular Mata dashi….

Wani mummunan faduwa gaban Inayah yayi ta tashi zaune ahankali dakyau tana cewa”

Sai tasashi yayi wani auren anty Hafsat?
Shima abbin sai yayi wani auren?

Wani mugun sanyi taji Yana shiga qafafunta tayi shiru tana jiran amsar anty Hafsat wadda taji rashin kamatan yin zancen da Inayah Dan haka ta Dan gyara murya cikin nutsuwa da kulawa da rarrashi tace”

Idan kika tsaya shirme nake fada Miki hakan kila zai iya faruwa,
Dan haka yanzu ki nutsu kema ki ringa kulawa da Abbin kaman matarsa sbd wannan right dinki ne dake Zaki bawa kanki.

Kasa cewa komai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa da wani irin tsoro dan kuwa tana fama da zuciyarta akan Haj umma idan Abbi ya auro wata Batasan ya Zata iya dauka.

Ganin ta Dena gane abinda take fada yasa Anty Hafsat yimata sallama da cewan Zata shigo gobe Inshallah.

Aje wayar tayi hannuwanta na Dan rawar data kasa gane Kota menene.

Kasa qarasa cin abincinta tayi ta miqe tareda daukan tray din ta fita zuwa kitchen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button