INAYAH 41-50

Abbi da Haj umma da Anty juwairiyyah ne suka juyo dukkaninsu atare suna kallonta.
Ba damuwar komai tace”
Haj umma Ina wuni?
Ya jiki jiki?
Anty juwairiyyah Ina wuni?
Tare suka amsa kadaran kadahan.
Gun Abbinta ta maida kallonta tareda sakin qayataccen murmushin farin cikin ganinsa tayo gurinsa Kai tsaye tana cewa”
Abbi kana gida ashe yau.
Da sauri Haj umma ke kallonta ganin da gaske gurinsa ta nufo din da shegun kayan dake jikinta Wanda zallan shape dinta suke bayyane Musamman shafaffen cikinta dayasa kirjinta dake cikin push-up bra fitowa dakyau.
Abbin kuwa Jin yayi kunyar ummansa ta kamasa da sauri ya miqe sbd fita da Inayah din saidai Yana miqewa tana qarasowa ba damar dakatawa sbd tariga ta qaraso ba tsammani kirjinsu ya hadu.
MAMUH
LOVE/ROMANCE
AA/AYSHATOUH INAYAH.
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: 47
Arewabooks@Mamuhgee
Firfito da idanuwa Haj umma tayi tana dauke kanta daga kallonsu batareda tasan tayi hakan sbd rudewa.
Anty juwairiyyah ma dauke kan tayi tana shafawa Al’amarin Inayah Ido Kuma daga Nan.
MAJEED Daya riqe balance dinsa da kyau sbd kiris yarage su Fadi har ita
cikin yanayi na kokarin daidaita kansa da ‘dan fada a shaqe yace”
Inayahhh,,,me ke damunki ne?
Ki nutsu mana…
Matsar da ita yayi daga jikinsa batareda ya kalli kowaba yaja hannunta suka fice dakin.
Itama kasa cewa komai tayi sbd Batasan yariga ya tasoba kodata iso idonta nakan Neman Inda Zata ajiye robar ruwan hannunta Dan haka ba zato tajisa ya miqe Bayan tariga ta iso dad dashi.
Suna fitowa Palo su zubbi dake gyaran yamma da sauri suka sauke Kai qasa daga kallonsu.
Umma yaganah data fito lokacin taci Karo dasu Yana gaf da shigewa da ita dakinta tabisu da Ido cikeda mamaki sbd ita kanta Batasan Yana gidaba alokacin.
Tsakiyar bedroom dinta ya tsaya da ita tareda dakinta ahankali ya dago Yana dauke idonsa daga kan jikinta da kayan jikinta suke lafe cikin yanayi na Dan fada yace”
So nawa Zan fada Miki kin girma ki ringa nutsuwa?
So kike Haj umma tayita Miki fada tunda bakya ji ko?
Meye hakan kike sakawa kina yawo cikin gidan bayan akwai mutane yanzu…
Sanyi jikinta yayi shikenan ita yanzu Abbi fada zaita yimata komai tayi tunda Haj umma bataso,
Ta saba yawo da qananun kayanta na Shan iska acikin gida ko yananan Amma yanzu shikenan sbd Haj umma Abbi fada yake Mata.
Zuciyarta taji tayi sanyi har idanuwanta suka nuna hakan
Jiki a sanyaye tace”
Kayi hkr Abbi bazan Kuma ba.
Juyawa yayi zaibar dakin saikuma ya dakata batareda ya juyoba sbd yanajin kukan datakeson yi ajikinsa Dan yasan halinta Sarai.
Ajiyar zuciya yayi Bai juyo dinba sbd tana ganin ya juyon Zata fara hawaye Dan sauya Masa ra’ayi.
Kofa ya nufa ya fice yabarta da kayan jikinta da dakin dasuka Dan dauki kamshinsa.
Hawayen dataso saukewa agabansane suka gangaro Mata zuciyarta na Mata nauyi Dan kuwa komai na sake tabbata Haj umma Zata wargaza duk wani matsayinta agurin Abbinta.
Daqyar ta iya lallaba kanta ta nufi toilet ta tube ta shiga ruwan zafi a bathtub ta lafe tanajin rashin Dadi a ranta.
Tajima a toilet din kafin ta fito daureda towel blue fuskarta ba wata walwala.
Neu Oil kawai ta shafa tareda spray da mist kadan ta saka free doguwar Riga har qasa Mata nauyi da qaramin hannu tayi sallar la’asar tana idarwa ta koma kan gadonta ta kwanta tana Dan dudduba wayarta kafin ta ajiye tana rasa meke Mata Dadi.
Karshe tashi tayi ta nufi dakin umma yaganah acan yayi kwanciyarta tayi baccin yamma na kusan mintuna arbain zuwa awa daya kafin ta tashi.
Sallar magriba tayi ta sauya kayanta zuwa Rigar sweater da wandon jeans ta saka babbar jacket coat da qaramar hijab iya wuya ta fito riqeda wayarta sai key din motarta Zata tafi asibiti Dan tana leqawa wasu lokutan da daddare.
Umma yaganah ce kawai tasan fitarta Dan abbin baya gida Dan haka tana fitowa Kai tsaye ta wuce ta shiga mota ta fice.
Ta Dan samu wasu patients Dr Abdul dayake asibitin shima yanata fama dasu dayar anmata aiki Amma kaman ta jiwa kanta ciwo gurin yunquri Mai qarfi dayan Kuma jininta yayi qasa sosai gashi likitoci da nurses na fama da ita taqi tsayawa a qara Mata jinin.
Wannan aikin yasa ta tsaya asibitin har kusan qarfe goma batareda Tama lura da time ba.
Suna gamawa taje ta wanke hannuwanta ta fito tareda zaro wayarta dake aljihun jeans dinta taga misscalls na Abbi kusan guda shida dana umma yaganah guda biyu sbd wayan a silent take.
Ya Salam” ta furta a gajiye tana saka Kiran Abbi.
Harta Isa mota ta bude Bata samu Kiran yashigaba Dan haka ta ajiye wayar gefenta ta tada mota tabar asibitin.
Tana shiga harabar gidan Abbinta tafara hangowa tsaye Yana waya da alama fita zaiyi sbd harda key din mota a hannunsa.
Jallabiyace milk a jikinsa duk da dare ne tana iya hango yanda jallabiyan tayi Masa kyau kaman wani Dan matashin black Arab.
Duk wadda ta auri Abbinta tasamu the best miji…..
Au itace matansa ko?
Yanzu Abbinta shine mijinta?
Wani murmushin farin ciki tasaki a fili tana cewa”
Koba komai dai tariga ta alaqantu dashi har abada Dan haka Haj umma matsayinta daban nata dabam.
Da farin ciki kan fuskarta kan fuskarta ta fito sbd mood dinta daya sauya take sbd wannan tunanin datai na tuna shi din fa mijintane itace matarsa.
Gurinsa ta nufa tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dako yaushe take cikeda kwarjini da kaunar ‘yarsa akai.
Cikin yanayin shagwaba tace”
Abbi kayi hkr banji kirankaba wayan na silent kuma hankalinmu ya dauki akan wata patient…
I’m sorry Abbi””‘ta qarasa cikin wani yanayi na sangarta.
Kashe wayar dayake yayi batareda ya gamaba sbd can bangaren anajin abinda take fadan.
Kallonta cikin idanuwanta yayi yaga gajiyan dake tareda ita ya sauke numfashi kadan tareda cewa”
Idan ba call duty zakiyiba ki Dena kaiwa dare haka a asibiti
Idanma Yakama kinyi daren ki kirani Zan daukoki da kaina..na soke tuqin dare da fitan daren Nan ke daya.
Murmushi tasake tana kallonsa tace”
Ok Abbi.
Ciki suka nufa tana basa labarin aikin dasukai da daren.
Kaman yanda ta saba suna shiga ta aje wayarta da takalmanta tareda zare Jacket coat dinta ta miqawa zubbi data bude musu kofa.
Kokarin balle maballan rigarta takeyi sbd tanada singlet aciki sukai Ido biyu da Abbi Wanda ya dauke kansa Yana Dan kame fuska yayi gaba batareda yace Mata komaiba.
Tunowa tayi da fadan dayayi Mata dazu akan hakan Dan haka ta fasa cirewa ta nufi dakinta tana karban wayarta da sauran kayanta.
Wanka tayi ta saka kayan bacci masu santsi Riga da wando ta haye gado daga kwance tayi addua sbd ta gaji sosai take bacci ya dauketa.
Washe gari Bata fita aiki da wuriba sbd ciwon Kai data Dan tashi dashi na lattin bacci.
Tana fitowa a shirye palon Abbi ta nufa Kai tsaye.
Shima a shirye ta samesa zai fito sai qamshinsa Mai sanyi yake zubawa ta zubawa fuskarsa idanuwa tana tunani wahalhalun dayasha da gwagwarmaya akansa take taji idanuwanta na cikowa da hawaye zuciyarta na qara cuduwa da kaunarsa Mai girma.
Jin shiru yasanyashi dagowa daga wayarsa dayake dauka ya kalleta a natse.