INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

Ganin yanayinta da irin kallon datake Masa yasashi Dan kame fuska Yana nufan kofa yace”

Tsayuwar me kikeyi kina lattin fita aiki.

Bayansa tabiyo tana cewa”

Good morning Abbi.

Dan juyowa yayi ya kalleta murmushin fuskarta Bai tafiba saima qaruwa da yayi
Da mamaki yace”

Are you okay?
Kinada labari Mai dadine kike Jin dadi.

Ba zato ta riqe hannunsa tana cewa”

Abbi farin ciki nakeyi ganinka kawai.

Dakatawa yayi batareda ya juyoba ganin su haj umma dasu umma yaganah dasuka fito rakiyar anty juwairiyyah da Zata wuce.

Kallonsu kowa keyi sbd umma yaganah batama San ta tashiba harta shirya ta nufi gurin Abbin,

Itakuma Haj umma mamaki takeyi meyasa haryanzu wannan ‘yar batada kunya ko tunani.

Ahankali ya zare hannunsa Yana Dan kokarin basarwa cikin nutsuwa yace”

Harkin shirya kenan anty juwairiyyah?
Muje na ajeki airport din saina wuce.

Haj umma Inayah ta kalla cikeda kulawa asake tace”

Ina kwana Haj umma?
Anty juwairiyyah Ina kwana?
Tafiya zakiyi yanzu?
Bazaki zaunaba kema kaman haj umma.

Janyota umma yaganah tayi gefenta tana matse hannunta qasa qasa tace”

Kiyi shiru idan bakisan abin fadaba Inayah.

Abbin da duk yabi ya rasa abin fada tayi ganin harda Haj umma zaa ta baro gurin umma yaganah tana cewa”

Abbi zanbiku a ajeni asibiti na kwana akan hannuna ciwo yakeyi bazan iya driving ba.

Da kulawa ya juyo Yana kallonta a natse yace”

Wat?
Shine kike tsaye anan tun dazu kina surutu?
Umma yaganah ta shafa Miki balm kafin kifita
ki zauna Charles zaizo yakaiki asibitin.

Shiru tayi tana kallonsa Jin bazaije da ita dinba.

Qin kuma kallon Inda take yayi ya nufi kofa Yana cewa su Anty juwairiyyah su fito.

Anty juwairiyyah ce ta kalleta tana cewa”

To saina Kuma dawowa Inayah,
Allah yabada zaman hakuri.

Amin” umma yaganah tace cikeda sakin fuska tana Mata Allah ya kiyaye har kofa.

Suna ficewa tadawo gurin Inayah tana cewa”

Da gaske kike ciwon hannun muje na shafa Miki ko rub kokuwa wani sabon halin kuka samu keda Neesah na hakan?

A dungure tace”

Kaina ne keyi yanzu ba hannunba
Na wuce saina dawo.

Tun su abbin Basu Gama ficewaba itama ta fito da tata motar ta fice da gudu ta wucesu
Yana kallo Bai nuna yaganiba Amma hankalinsa ya rabu da tuqin nata kusan zuciyarsa kasa samun nutsuwa tayi su umma na gani yabi hanyar databi yayi dogon zagaye dasu har Saida yaga isarta asibiti lafiya ya wuce dasu airport batareda yasan da suna lureda uban zagayen dayayi dasuba Dan ganin Yar gaban goshinsa ta Isa aiki lfy.

Suna Isa airport ba wani Bata lokaci anty juwairiyyah ta shige sbd lokacin zasu tashi.

Gida yadawo ya ajiye Haj umma ya wuce aiki.

Gidan yau yaqara yin tsit sbd anty juwairiyyah cema keda Yar hayaniyar wayoyinta da jama’ar kasuwancinta.

Da wuri tadawo yau Dan tare sukaci abincin Rana da ita
Tana Gama cin abincin Rana ta koma daki Dan tanada vid conference call dasu Neesah da wasu abokan karatunta da zasu qarawa juna sani akan aikin nasu Wanda sukeyi akai akai sbd da yawan wasu sunfi wasu qwarewa Musamman su dasuke Dan saka shiriritata itada Neesah.

A daki taqarasa wunin ranar tana conference din da abokanta saidatai sallar magriba ta fito sanyeda kayan Shan Isa gashinta a daure tsakiyar kai kaman wata Yar baby sbd fatarta daketa daukan idon hutu da gyaranta na aure da haryanzu yakeda saura.

Palo ta zauna gurin su Haj umma dake Dan fira sama sama da umma yaganah wadda wadda yanzu Ta Kama kanta a abubuwa da dama gidan sbd Haj umma dake nuna matsayinta na uwar maigidan.

Suna zaune palon Abbi yadawo yashigo idanuwansa akan Inayah datake kwance jikin umma yaganah kaman Mara lafiya.

Gaisawa yayi dasu dukan kafin ya wuce palonsa zuwa bedroom dinsa sbd a gajiye yake.

Wanka yafarayi yayi ya saka pradas na Shan iska ya zauna Yana duba sauran aikinsa acikin iPad Yana Dan amsa waya akai akai.

Lokacin magriba nayi suma duk suka tashi zuwa dakunansu sallah.

Sai qarfe 7 da mintuna suka hallara dining cin abinci.

Yauma kusan Haj umma nunawa tayi baa kulawa da majeed din yanda yakamata Dan haka da kanta taqara Masa salad akan Wanda Inayah ta zuba Masa Kuma ya nuna Jin dadin hakan a taqaice sbd haryanzu yakasa sakewa yakoma yanda yake ada gaban mahaifiyar tasa
itama Bata damuba sbd tasan sai ahankali ko wannan sabo da shaquwar tasu ta dah Zata dawo sbd shekaru kusan ashirin da hudu zuwa da biyar ba wasaba.

Fira taringa jansa cikin kulawa Yana amsawa shima cikin kulawar,

Inayah da umma yaganah Yan kallo da saurare suka koma
Karshe dai haka inayah tagama ta tashi ta komawarta daki sbd ganin yau ko kallonta Abbin nata baiyiba hankalinsa nakan Haj umma.

Umma yaganah ma tariga tashi tabar dining din ganin yau Haj umma Dagaske Jin ‘danta takeyi Dan haka kowa ya silale ya shige yabarsu.

Babu Wanda yasan lokacinda suka Gama harsuka koma Palo suka qarasa firar acan suka shige.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810
[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: 48
Arewabooks@Mamuhgee
Washe gari da wuri ta fita aiki ko Abbi dataje gaidasa bai fitoba wucewa tayi bayan ta kirasa awaya kashe da alama Bai tashiba.

Ko yau ta hadu da umma Hadiza asibiti sbd umman hankalinta Bai kwanta da barin Abdul da Inayah dinba batareda ta rakosa tana sake tunatar dashi illar da shedan ke masaba na maqalar Masa da tunanin Inayah.

Duk da ya tabbatarwa umma Hadizan zai nesanta kansa da duk wani tunanin daban Amma takasa yarda dari bisa dari dashi,

Tasan bazai aikata abinda yafita musulunciba Amma Kuma batason ya shigewa Inayah din sosai sbd ko kadan bazata so a shiga haqqin AA MAJEED ba bayan datasan girmansa da sadaukarwarsa akan Inayah,

Ayanzu ko ita data Haifa Inayah din tayi alqawarin dakatar da kanta daga zuwa gunta matuqar ba MAJEED din ya Basu Daman hakanba.

Yauma kaman baqi haka suka gaisa da juna saidai har umma Hadizan ta fice Inayah na zaune cikin mota tana kallonta.

Fitowa tayi ta nufi ciki tana saka wayarta silent tareda sakawa cikin jaka.

Kaman yanda suka Saba kusan tareda Dr Abdul tayi aikin wunin ranar na duba patients Dan haka tafara Jin sakewa dashi kaman yanda suke can farko.

Sai yamma sosai yau tadawo Dan haka Bata tsaya koinaba sai bedroom dinta tafada wanka.

Tana fitowa sallar magriba tayi tareda saka kayan bacci tayi kwanciyarta a  daki tana Jin ciwon Kai na Dan damunta na gajiya.

Ta Bangare Daya jinta takeyi wani sukuku sbd gabaki daya wunin batai magana da Abbinta ba abinda baitaba Kuma baya faruwa a rayuwarta,

Abbinta shine abokin firarta akoda yaushe kusan da safe da Rana kusanma dai time to time suke waya idan har baya gari
Idan Yana gari kuwa tunda safe saitaga Abbinta take fita hakama kafin tadawo Zata kirasa da darema tare sukecin abinci a dining Kuma tabisa palonsa kafin taje ta kwanta Amma yanzu komai Yana neman canjawa duk sbd auren Nan dakuma zuwan Haj umma.

Da zaaci abincin dare Bayan kowa ya zauna zasu fara baiga tafito Kuma yau duk baijitaba shima.

A natse ya dago ya ‘dan kalli umma yaganah yace”

Inayah Bata dawo daga asibiti bane?

Tadawo,
Batajin dadine kanta na ciwo tun dazu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button