INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

Cikin nutsuwa da kulawa da sanyin murya tace”

Good morning Abbi.

Idanuwanta ya kalla kafin ya dauke idonsa akai anatse Yana cewa”

Morning,
Yaya jikinki?

Complain zatayi umma yaganah ta katseta da cewa”

Yaya jikin Inayah?

Naji sauki umma,
Haj umma Ina kwana?
Umma yaganah good morning.

Zaunawa tayi tana kokarin fara cin abinci Haj umma tace”

Yaya kan?
Yayi sauki ko?

Eh naji sauki alhmdllh.

Fara cin toasted bread tayi tana daukan tea tafarasha.

Itace tafara gamawa ta miqe ta Zata fice Abbinta yace tajira zai ajeta asibitin.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810749
Arewabooks@Mamuhgee
Bai dauki wasu mintinaba ya Gama shima ya goge bakinsa da tissue tareda miqewa yabar dining din
A natse cikin sautin Mara qarfi yace”

Saina dawo umma.

Umma yaganah ya dan kalla itama yace”

Saina dawo.

Kusan atare sukai Masa adduar adawo lfy.

Zaune Inayah take tana chatting sama sama da Neesah dake son Jin labari daga gareta tana ganin ya nufota tafara kokarin saka wayar cikin aljihun skinny jeans din dake jikinta da farar doguwar Riga Mara nauyi wadda gefenta yake yanke daga qasa har gurin qugunta.

Cinyoyinta da wandon ya lafewa ya Dan kalla Yana dauke kai kafin ya dakata daga shiga motar ya juyo cikin fada yace”

Kije kisa native wear.

Kallonsa tayi da sauri tana kallon kayan jikinta….

Me Kuma kayanta yayi?

Sake dagowa tayi ta kallesa taga harya shige motar Yana zaune
Batace komaiba ta juya Takoma cikin gida ta sauya kayanta zuwa Riga da skirt na atampa dark green da qaramin medium chantley veil ta fito riqeda qaramar Chanel handbag.

Gaban motar ta bude tashiga suka wuce.

Suna fara tafiya ahankali ta juyo ta kallesa tareda marairaice fuska ta dafa dayan hannunsa dake gefen datake cikin wata sanyayyar muryar shagwabar data Saba yimasa tace”

Abbi idan nayi lefi Dan Allah kayi hakuri bazan sakeba.

Dan juyowa yayi ahankali ya kalleta da idanuwansa dake sake Jin hawayen shagwaba,
Tace please Abbi Dan Allah bazan sakeba.

Hannunta ta qarasa dorawa kan hannunsa
Ya Dan sake kallonta

Tana ganin ya kalleta ta gangaro da hawayen data Tara a Ido tana qara marairaice Masa.

Rintse idanuwa yayi ya bude ahankali Yana dauke kai daga kallonta….

Besan yaushe Inayah ta iya wainnan abubuwanba na saurin kuka yanzu Musamman idan tanason Abu daga garesa sbd tasan kukanta shine abu na karshe dazai so a duniya.

Ahankali ya sauke boyayyan numfashi cikin kulawa da sanyin lafazinsa yace”

Meyasa kike Wasa da abinci?
Kina aikin lfy kice bakisan ciwo da dama suna shigaba ta hanyar yunwa?

Karna kumajin zaaci abinci kinbada different story daga yau.
Okay?

Gyada Masa Kai tayi tana sake riqe hannunsa cikin nata.

Zare hannun zaiyi tasake riqewa tana cewa”

Nacefa bazan sakeba Abbi,
Ahaka zamu qarasa ai ni matarkace yanzu Ab….

Wani mummunan burki yaja dasu akan hanya Saura kiris motar bayansu ta dakesu.

Kallonsa takeyi da mamaki batareda ta damu da abinda tafadaba cikin kulawa tace”

Are you okay Abbi?

Juyowa kadan yayi Yana zuba Mata manyan fararen idanuwansa dasuka sata Jin gabanta faduwa a Karo na farko sbd Abbin nata Bai taba zuba Mata idoba sosai Yana kallonta.

Koyaushe kallonsa akanta taqaitaccene duk da tsananin kaunar da son dayake Mata amatsayin ubanta.

Sunkuyar da kanta tayi ahankali Jin kallon yayi Mata nauyi da karfi ahankali tace”

Sorry Abbi.

Hannunsa dake cikin nata ya janye ahankali batareda yace komaiba ya ja motar suka wuce.

Shiru bakinta yayi sbd tasan ta zaro zancen da umma ke cewa idan batada abin fada ta ringa yin shiru Dan haka tayi shiru Amma Kuma ai Dagaske shi mijintane kodai Abbinta baya Sonta kenan da auren???

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun” ta furta a fili tareda dagowa ta kallesa tana Jin kaman hankalinta zai tashi da wannan tunanin.

Har suka Isa asibitin Babu Wanda yasake magana
Yana parking motar Dr Abdul na shigowa harabar asibitin.

Fitowa Inayah tayi tana kallon motar Dr Abdul din kafin tadawo da kallonta kan Abbinta.

Bai lurada Hadiza ba dake cikin motar ya sauke glass din motarsa Yana amsa gaisuwar Dr Abdul daya iso cikin girmamawa kaman da can Yana gaidasa.

Ba tsammani sai ganin hadiza yayi tana qarasowa gurinsa.

Inayah ya juya ya kalla itama shi take kallo batareda ta kalli Inda Hadiza ke tahowaba.

Hadiza na isowa cikin Jin kunya da nauyinsa Mai tsanani ta Dan kallesa a sanyaye tace”

Ina kwana Abbin Inayah.

Daga ita data fada har su duka dake gurin tsit sukai cikin jujjuya zancen.

Batareda ya kalletaba cikin nutsuwa ya amsa a taqaice da cewa”

Muntashi lfy¿

A natse Inayah ta gaidata tareda kallon Abbin tace”

Abbi to waye zaizo daukana idan natashi tunda banzo da motaba?

Tada motarsa yayi ya dago ya kalleta cikin kulawarsa da kaunarsa yace”

Dr Abdul nasan zai Zama busy
May be mamansa idan Bata komai Zata iya maidaki gida,

Amma karki biya koina daga asibiti gida direct Zaki koma.

Jan motar yayi yabarsu tsaye Inayah nabin motarsa da kallo
Umma Hadiza kuwa wanin zallar farin ciki da mamakin MAJEED ne yacikata kenan majeed din ya yarda takai Inayah gida sbd kawai ta zanta da ‘yarta….

Tasan bazai iya yafe Mata ko kulata lokaci dayaba Amma ko ahakan ta gode da karamcin.

Inayah rasa abin cewa tayi ta kalli umma Hadiza da farin cikinta Bai boyuba tace”

Zan dauki drop kokuma na Kira Charles idan natashi sbd Zaki wahala zuwa daukana Kuma ki kaini har gida.

No Ayshatouh please kibari nazo na daukeki da kaina
Muna buqatan sanin juna
Damace Abbinki yabani please.

Dan murmushin yaqe tayi tana cewa”

Ok Zan tashi 2 yau Inshallah.

Zanzo kafin 2 Inshallah.

Juyawa tayi ta wuce dama Dr Abdul Bai tsayaba ya wucewarsa.

Bayansu umma Hadizan tabi da kallo tana jin farin ciki Mai tsanani ganin yayanta dukasu biyun likitoci ne.

Duk da Inayah Bata Gama Zama qwararriyaba Amma zuwa gaba itama tasan Zata Zama abin alfahari gurin marasa lfy dasu iyayenta.

Data tuna mahaifiyarta zatazo daukanta saitaji wani iri Amma Kuma ita kanta tanason sanin umman Abdul din.

Qarfe daya da arbain kuwa saiga Hadiza ta iso asibitin Dan haka Inayah ta tattara ta fito suka wuce gida.

A hanya umma Hadizan keta Jan Inayah din da fira da tambayoyi akan rayuwarta Wanda komai ta tambaya sunan abbine amsar,

Anan tasake saddaqarwa MAJEED sbd yariga yayi ginuwar da Babu abinda zai girgizasa Aran Inayah,

Shine ciki da Bai din rayuwarta Dan kuwa da ace wani mijin ta aura bashiba zaiyi wuya mijinta baiyi kishinsaba duk da Yana matsayin ubanta sbd kaunar tayi karfi.

Kaman daga sama ta jeho Mata tambayar

“Ya maganar aurenki da Abbin naki?…

Shiru Inayah tayi cikin rausayar dakai tace”

Bansaniba,
Amma dai Ni aguna tanan bazan taba rabuwa da Abbi ba ko bayason auren nidai inaso yanzu….

Kallon mamaki Hadiza tayiwa Inayar tana tauna zancen,

Lallai majeed yagama shagwaba Inayah ta yanda Babu ruwanta duk maganar datazo Mata fada takeyi.

Tayaya zakiso auren idan shi baisoba ai Babu au……

Karki min Baki a auren please,
Ni inaso Kuma tunda inaso Abbi ma zaiso.

Murmushi Hadiza tayi aranta tana cewa”

Hmm wanna abbin naki Mai taurin Rai bazai taba kallonki mace ba bare matarda zai iya kwanciyar aure da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button