INAYAH 41-50

Kansa da kirjinsa sun toshe baida tunani komai.
Alwala yayo yafito yayi sallar magriba da aka Kira.
Yana idarwa babyn ta farka ya taso ahankali ya tsaya akanta Yana kallon yanda take motsawa ahankali tana fidda harshe alaman yunwa.
Numfashi ya sauke a sanyaye kafin ya juya gurin jakar kayan madaranta da nurse ta koya Masa yanda zai hada.
A sanyaye ya hada mata madaran da ruwan roba kafin ya debo ruwan dumi ya saka madaran yayi dumi.
Ajewa yayi gefe kafin ya dauki babyn yafara Bata ta karba take tana zuqa ahankali.
Qura Mata fararen idanuwansa dasuka sauya yayi Yana Jin tausayin kansa da ita,
Meyasa iyayensu zasu zabi jefar dasu akan qaddara?
Meyasa iyayensu suka zabi rabuwa dasu akan abinda suma basune suka samarwa kansuba?
Uwa mace da akafi sani da qawa zucin ‘danta Amma su nasu uwayen Mata ne suka fincikesu daga rayuwarsu suka ‘yar batareda nazari ko tunanin halinda zasu shigaba.
Shi tasa uwar data fincikesa daga rayuwarsu ta Yar yanada girman dazai kula da kansa Amma ita wannan babyn me tasani.
Har tagama shan madaran tayi bacci bai saniba sbd nisan dayayi a tunani.
Har lokacin sallar ishai tayi Yana zaune rungume da babyn.
Sallar ishai yayi wadda Yana idarwa ya nema guri yazauna tareda rufe idanuwansa yanajin yanda kansa ke tsananin ciwo.
Babban saukin daya samu babyn bamai rigima bace Dan haka har safe batai Masa rigima ba sai Madara datakesha sosai Dan haka baiyi wani baccin safeba.
Garin na wayewa guraren qarfe goma Dole cikin ma’aikatan hotel din yasamu wata ta sauya Masa kayan babyn ta shirya Masa ita ya dauketa suka sake koma gidansu.
Wannan karon Yana Isa babban tsaro yasamu a gate akan kada abarsa ya Shiga gidan.
Kiran wayar hajiyar ya ringa Yi Amma Sam Bata dauka daga karshe aka kashe.
Numbern anty juwairiyyah yafara kira itama bata dauka.
Ta anty safiyyah yakoma Kira itama Bata dauka.
Anan ya kusan wuni da babyn cikin Rana ganin Zata wahala yasa yakoma hotel din.
Washe gari haka yakoma gidan Amma saiya samu labarin sun wuce Lagos gabaki dayansu gurin ganin likitan hajiya.
Tashi hankalinsa yayi Dan haka ya ringa Kiran wayar hajiyar Bata Shiga qarshe ya Kira anty juwairiyyah.
Kalaman data fada masa sune yaka saddaqar da duk wani sauran burinsa na zama cikin Yan uwansa da mahaifiyarsa.
Ta sanar dashi hajiya umma Bata kaunar jinsa ko ganinsa,
Idan yakuma zuwa ko kiranta Zata iya tsine Masa.
Wainnan kalaman sun girgiza duk wata jarumtarsa da karfin zuciyarsa,
Amma Kuma sun daskarar da zuciyarsa data tarwatse lokaci daya,
Tabbas zaiyi nesa da Inda Haj umma Zata gansa bare yazama sanadin mutuwarta da ‘yan uwansa suke fada.
Yana barin gidan yakoma hotel ya tattara kayansa guri daya,
Yayi wani irin kukan baqin ciki da maraicin rashin mahaifi a duniya,
Yayi kukan rabuwa da uwa wadda yasan itama tana cikin quncin wannan hukuncin nata saidai Kuma bazai taba Zama sanadin ciwonta ba dakuma tsinuwar data ambata garesa.
gari na wayewa ya nufi Tasha yahau motar komawa Yola.
A motar tun agurin Lodi ya sanar masu mahaifiyar ‘yarsa ta rasune zai koma gida gurin danginsa.
Da wannan ya kawarda kallon zargin da ake binsa dashi fa babyn.
Wasu sun yarda wasu Basu yardaba ahaka dai akai tafiyar Amma saida wata dattijuwa ta karban Masa babyn sbd ganin yanda yake fama da babyn.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/4, 11:05 AM] +234 813 979 4675: 42
Arewabooks@Mamuhgee
Wuni cur sukai a hanya kafin suka Isa,
Saida ya sauka mota hankalinsa yayi mummunan tashi sbd baisan yanda zaiyi da babynba,
Baisan wazai tunkara ba,
Baisan tayaya zaiyi rayuwar makaranta da babynba.
Tunanin farko daya fara zuwa kansa shine ya fara Kama hotel na kwanaki sbd bazai iya Zama da ita a gidansaba sbd bashi kadaineba tare yake da friends dinsa ashir da Nuraddeen.
A hotel din daya Kama yakwana da babyn gari na wayeba baida zabi daya wuce yakaita gurin renon marayu sbd bazai iya yawon makaranta da itaba.
Kudin daya bada sosai ne kadai yasa suka karban Masa ita amatsayin ‘yarsa da mahaifiyarta ta rasu gurin haihuwa.
Kwana biyu yayi yana yawo tsakanin makaranta da zuwa duba babyn,
Sabon yanayi ya shiga na rashin sauki fa sukuni,
Hankalinsa ya rarrabu,
Ga damuwa da quncin dake maqale cikin ransa.
Ahaka yayi kusan sati biyu
Take kudadensa sukai qasa sosai.
Babban abinda ya sake basa tsoro da firgici ga halin mutanen duniya shine duk kudi da Madara dayake siya na baby metron kashe kudin takeyi Bata siya Mata abubuwan buqata
Ko gyaran jiki dayace aringa Mata da wipes sbd asibiti dasukai masa gargadi akan rage yawaita Yimata amfani da ruwa sbd sanyin daya kamata a baya,
Amma sbd rashin tausayi da imani Ashe ruwa suke Mata amfani dashi ko Pampers basa siya maqale kudin sukeyi ko fitsari tayi ruwa suke saka zuba Mata sosai.
Ciwo yafara Neman kama babyn damuwa tasake kamasa sosai gashi bayajin zai iya miqa babyn har abada gidan marayu.
Haka yanaji Yana gani ya bar babyn hannun metron sbd watanni kadan suka rage Masa ya kammala karatun.
Komai nasa yaqare,
Kudin hannu da account dinsa sun qare tas dan haka yafara shiga yanayi sosai.
Babban sauyin daya samesa na rayuwa shine gabaki daya ya rasa walwala da fara’arsa,
Zancen abinda ya samesa tuni ya yadu tsakanin Abokai da jama’ar dasuka sansa Dan haka Ya tsame kansa ya kame daga hulda da kowa yanzu dama can bamai hayaniyar shiga mutanen ne Shiba,
Cikin tsananin hali ya kammala sauran watannin dasuka ragewa karatunsa bayan ya Saida duka agogansa da wayarsa sun qare ga hidimar baby INAYAH wadda yasawa sunan Da karatunsa.
Yana kammalawa ya tattara sauran abinda ya rage Masa ya fita neman hayar dakin dazai zauna ya nema aikin dazai kula da kansa da Inayah.
Wata irin qauna Mai tsanani yakewa Inayah a yanzu daya Gama tabbatarda batada kowa saishi kaman yanda baida kowa sai itan.
Kiransa da metron keyi da abban Inayah yasa kauna da shauqin abin ya shigesa sosai harya sabarwa kansa da amsa sunan.
Gashi Inayah din tayi girma ta warware kaman kowane Lafiyayyan baby.
metron ce tayi Masa tayin gidan hayarsu
Baida zabi haka ya amince duk tsananin qyanqyaminsa da rashin iya Zama cikin mutane.
Ganin yanayin gidan da jama’a sosai yasa ya ringa karbo Inayah wasu ranakun tana wuni hannunsa kafin ya maidata da daddare.
Rayuwa Tai Masa tsanani sosai sbd baida komai baida hanyar koman,
Ga metron tafara gajiya da renon tunda baida abin Bata yanzu saiya samo daqyar.
Rayuwarsa tagama sauyawa tako Ina,
Baya shiga mutane sbd kusan duk Inda yaje zundensa akeyi akan ‘yarsa Inayah wasuma jifansa suke da zargin sai Allah idan ba lalata ‘yar tasa zaiyiba.
Girma da tsananin dacin kalmomin ya sanyashi tashi gidan bayan ya hada kudin hayar daki wani gidan daqyar da aikin wahala.
Dayake yaga alaman metron ma ta gaji da renon Inayah kawai karbota yayi ya dawo sabon gidan daya samu mai dakunan haya birjik a jere
Mai daukeda mutane dabam dabam masu halaye daban daban.
Dagashi sai tabarma da abun rufa yadawo gidan sai yan kayansa na sawa dasuka Gama fita hayyacinsu sbd kodewa.