INAYAH 41-50

Kayan Inayah ba duka suka basufi kala huduba Dan haka dakin nasu fili fayau ne.
Madara yabata tayi bacci yafara kaida kawon tsakiyar dakin da ita a kafada Yana tunanin yanda zaiyi da ita yanzu.
Zuciyarsa ta qame ta bushe akan Al’amarin mutanen duniya da basusan komaiba sai kansu.
Cikin yardar Allah da zashi masallaci yafito da ita a kafada yana tunanin yanda zaiyi da ita yaje sallah.
Umma yaganah ce ta lura da hakan Kuma tunda ya tare ayau din aka fara tsegumsa tanaji sunayi abinka da gidan haya gulma ba taushe hannu.
Karban Masa ita tayi tace yaje sallar yadawo.
Ba musu yabata sbd Yana buqatan hakan.
Daga masallaci gurin neman aikin qarfi yadan zagaya yi Amma bai samuba sai daya dawo yasamu a anguwar ya samu tsaron shago Amma na idan an siya Kaya yakai mota yace ya amince.
Koda yadawo umma yaganah tayi Mata wanka da ruwan zafi tas ta Goyata sbd itama tanada tsananin sha’awar Yara Amma Allah Bai bataba ga manyanci haryazo.
Godiya yayi tareda bar Mata Inayah din sbd kada a datse mata bacci.
Tun daga ranar renon Inayah yakoma hannun umma yaganah wadda ta fahimci baya tareda uwar Inayah tunda dai shine mahaifinta.
Rayuwa taci gaba da tsananta Masa sbd komai ya qarasa juye Masa,
Aikin tsaran shago da aikin gidan ruwa ya hada biyu yanayi dashi yake daukan dawainiyar Inayah.
Ahaka har lokacin service Dinsu yayi yatafi yabarwa umma yaganah Inayah sati biyu acikin camp ya fito yadawo yafara bautar qasarsa.
Fara service dinsa ya taimake rayuwarsu sosai sbd monthly allowance dinsa dashi yake musu komai.
Kauna sosai ta tsakanin uba da ‘da yakewa Inayah,
Duka a lokacin burinsa na inganta akanta yaqare,
Baida abinda yafi Masa Inayah sbd kaunarta ta taimaka gurin danne Masa radadi da ciwon dake daskare cikin zuciyarsa.
Ahaka yagama yake fita aikinsa na service Yana dawowa kuma ya hada Dana aikin gidan ruwa.
Koda ya kammala service dinsa Inayah tayi wayo sosai tasan mahaifinta wasu lokutan daqyar ma take komawa gurin umma yaganah.
Haduwarsu da yagana yazama wani babban taimako daga Allah dan kuwa badan itaba baisan tayaya zaiyi renon jinjirar ‘ya shikadaiba.
Bayan Gama bautan qasa komai yasake tsananta alokacin ne yafara aikin wahala da qarfi kala kala Dan inganta rayuwar ‘yarsa wadda yanzu a hannunsa take tabar hannun umma yaganah.
Tare suke cin abinci tare suke kwanciya
Wani lokacinma tareda ita yake fita aikinsa na wahala tana zaune cikin inuwa yake aikin yagama sudawo gida.
Ganin kaman sanyin dakin zai Mata yawa yasa yasiya mata karamar katifa shikuma Yana kwanciya a tabarma,
Duk wani abun buqata da Zata buqata baya sanya koda wahala saiya Nemo ya ajiye Mata.
Ita kanta tunda tayi wayo tasan mahaifinta wata irin kauna da shaquwa Mai tsananice ke tsakaninsu,
Batada abinda yafi Mata Abbinta a rayuwarta sai umma yaganah data sani,
Sam Bai taba barin tayi kuka ko kewan rashin uwa ba,
Shine uba Kuma shine ya maye gurbin uwa,
Mata wani irin kallo yake musu na rashin tunani da rashin tausayi da imani shiyasa duk wata mace ta fice Masa arai,
Mahaifiyarsa data qyamacesa sbd wannan qaddarar Bai tabajin ya tsanetaba Amma Kuma yasan tabbas Bata kyautaba Dan batai aiki da ilimin da Allah ya Bata.
Inayah itace tazamo sanyin idanuwansa Kuma qarfin gwiwarsa sbd duka gwagwarmaya dayayi a halin dasuka samu kansu yayisune sbd inganta rayuwarta,
Yayi alqawarin ingata tasa rayuwar da tatane sbd su rayu kaman kowane ‘yaya marayu sbd daga shi har ita marayin Allah ne.
Hadiza bayan barinta gidansu majeed hanya tabi tana Jin kanta na juyawa sosai ga uwa uba tafiyar datakeyi kaman Mai koyan tafiya Dan kuwa gabanta tuni yafara zubarda Jini sosai na yamutsin dayake ciki.
Batai doguwar tafiyaba taji tana Neman haukace tuburan Dan haka ta nema bakin wata hanya ta zauna tana rusa kuka sosai tana tasa Inda ke mata sauki a jikinta.
Kukan datakeyi ne tana yagar jikinta yajawo hankalin mutanen dake kusa suka fara kallonta suna tausaya mata wasu Kuma Mai Mata video sbd ganin haukacewa zatai alokacin da alama asiri akai mata suke zargi.
Kayan jikinta take kokarin yagawa wata Mata dake kokarin Shiga motarta tayi saurin zuwa ta tareta tana masifa da masu Mata video.
Cikin kuka da azaba sosai Hadiza ta bude Baki daqyar tana cewa”
Dan Allah ki taimakeni kikaini asibiti su ciremin gabana wlh azaba,
Ciwo,zafi,radadi duka inaji.
Kallonta matar tayi da mamaki tana sake riqe Dan kareta da handbag dinta masu sbd daukanta.
Da mamaki tace”
Me yake Miki azabar?
Me kikeji?
Kasa magana Hadiza tayi tana sake bubbuga gabanta cikin ficewa hayyaci tace”
Dan Allah ku taimakeni…..
Da sauri matar ta tari taxi ta cewa Hadizan ta shiga batareda ta kamataba sbd tsoro da tsaro.
Tata motar tashiga tacewa taxi driver din yabiyota.
Wani asibiti suka nufa tasa aka shigo da Hadiza wadda ta fice hayyacinta tini bayan gurnanin azaba da wahala Babu abinda take.
Da gaggawa suka karbeta zuwa ciki suka fara dubata.
Gaban nata dataketa duka suka fara budewa suka duba.
Wata qara suka ringa saki cikin tashin hankali da tsoro.
Dayake wadda ta kawota asibitin likitace take suka taru suka gano haihuwa tayi gabanta yasamu matsala.
Cikin gaggawa da tashin hankali suka fara taimakonta.
Dayake gurin ya lalace sosai Saida aka hada da yimata Yar qaramar tiyata.
Bayan taimakon data samu sun Gama Mata komai an maidata dakin dazata kwanta tana bacci batareda tasan waye akantaba.
Dr iklimat itace ta biya komai na Hadizan tukuna ta wuce gida.
Kwananta uku a asibitin kafin yadawo cikakken hayyacinta ta zauna daidai tana Jin komai Yana dawo mata sabo yanda yafaru.
Tashi hankalinta yayi tafara kuka Mai tsanani na Dana sani da Neman ‘yarta.
Da farko Dr iklimat ta dauka Hadizan nada ciwon qwaqwalwa ne Amma data zaunar da ita ta rarrasheta ta sanar da ita komai sosai hankalin Dr iklimat ya tashi Dan haka Hadizan na samun sauki suka dunguma Neman gidansu MAJEED.
Kasa gane anguwar tayi bare gidan Dan haka suka ringa yawon stations suma Kai report Amma ba wani labari.
Tashin hankalin da Hadizan tashiga yasa take Neman rasa nutsuwa da lafiyarta sbd ahankali yafara taba qwaqwalwarta.
Dr iklimat data fara tsorata da Al’amarin haka ta samu ta lallaba Hadizan takaita Inda tafara ganinta tace tayi tanuni daganan ko Zata iya game gidansu MAJEED din.
Kaman qwaqwalwarta bazata tunaba sai gashi ta tuna suka ringa bin Inda take tunawa har Allah yasa suka Isa kofar gidan.
Basuga tashin hankali ba Saida aka tabbatarda MAJEED da babyn baasan Inda sukeba.
Take agurin Hadiza ta suma,
Haj umma ma Jin maganar dake bakin Hadiza yasata zubewa itama tana dafe kirjinta dake kokarin tashewa da tashin hankali Mai tsanani.
Daqyar su Anty safiyyah da taimakon Dr iklimat ta Dan dawo daidai.
Kuka tafara tana yiwa Hadiza Allah ya Isa akan abinda tayiwa MAJEED ta rabasa da uwarsa akan ‘yarta Mara uba da asali.
Hadiza Kam saidai akai asibiti da ita.
A asibiti tana farfadowa Bata iya kukaba sbd zuciyarta dake barazanar daina bugawa.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902