INAYAH 41-50

MTN card????
0913484810743
Arewabooks@Mamuhgee
Daga gidan Dr iklimat Hadiza sake komawa tayi gidansu hajiyar MAJEED wannan karon tana kuka tana komai Amma irin wulaqanci da tozarcin dasu anty juwairiyyah sukai Mata baisa ta hakuraba haka ta ringa zuwa rokonsu su fada Mata Inda MAJEED ya tafi da yarta.
Tun tana zuwa tana samun ganinsu har takai idan tazo Mai gadi ke yimata korar wulaqanci yana zaginta.
Daga qarshe police suka saka aka kamata daqyar tasamu Dr iklimat ta karbota bayan ta sanar dasu Hadizan nada matsalar qwaqwalwa.
Tun daga lokacin tashiga wani mawuyacin hali na ciwo da nauyi a zuciya.
Gabaki daya bata gane komai batajin komai sai kukan jaririyarta,
Kuka tuninya Dena zuwan Mata ya qafe..
Ta dan samu lokaci ahakan cikin masu aikin gidan Dr iklimat kafin Dr iklimat tafara janta ajiki Dan ta warware tafara dawowa daidai.
Da fari Al’amarin yayi wuya Amma da dr ta dage sosai Kuma lokaci yaja sai gashi tafara sakewa sbd kyautatawa Dr iklimat dataketa dawainiya da ita.
Itama aikin ta dauketa cikin gidan na abinci data iya.
Ganin qwarewarta a iya abinci yasa Dr iklimat ta maidata restaurant dinta sbd taga qaruwar da zatai da Hadizan.
Dayake tasaba aikin restaurant sai Bata wani Sha wuyaba tasaba da aikinta sbd Sam yanzu Babu wani digon farin ciki ko daya a rayuwarta,
Zuciyarta rufe take ruf da tarin baqin ciki da damuwa Amma a fili tana iya kokarinta gurin mu’amala me kyau da mutane.
Dr biyanta albashinta takeyi Mai kyau ba gayya Kuma kullum ta gamo aiki a can da daddare gidanta take dawowa ta kwana Saida sassafe ta koma.
Ahaka yayi fiyeda shekara daya a tareda Dr wadda Takoma tamkar wata babbar yayarta sbd sabo da kulawa,
Fes Takoma tayi fresh abinta sbd nutsuwa da cigaban data samu sosai.
Ana hakan abokin babban yayan Dr wani soldier yaganta yayi shaawan aurenta sbd yafi shaawan auren macenda batada kowa ganin yakeyi tafi maka biyayya hakama Zata riqeka amatsayin kowa nata tabika duk Inda kakeda ra’ayin juyata ko kaita.
Dr iklimat tana duba ribar da Zata samu a komai na rayuwa Dan haka MJ Muhammed na bayyanarda buqatansa na auren Hadiza tasan cigabansu sbd yanada arzikinsa sosai saidai yawan auri saki Amma yanzu kila ya daina tunda ya samu irin wadda yakeso wadda bazata iya Musa Masa komaiba sbd batada kowa.
Hadiza batada ra’ayi ko shaawan aure yanzu ko kadan aranta Dan haka Bata boyewa Dr iklimat ba ya fada mata batada ra’ayi.
Dr batai qasa a gwiwa ba ta ringa lallaba Hadizan tana cusa mata ra’ayin da auren kawai Zata samu sukuni da nutsuwata rayuwa tareda komawa cikin ‘yan uwanta dasuka gujeta,
Aure ne kadai rufin asirinta Kuma shine zai Bata Daman sakin kudi ta nema majeed da ‘yarta duk duniyar daya gudan Mata da ‘ya.
Zancen Ayshatouh da Dr tasaka yayi tasirin sauya Mata raayi Akan yin auren.
Ba bata lokaci kuwa Dr tafara karban kudi sosai gurin MJ Muhammed aka fara gyaran Hadiza daman gata da sauran kuruciyanta.
Gaggawa Dr iklimat tasaka akan auren Wanda yasa Hadizan kejin damuwa Amma Kuma bazata iya fasawaba tunda tabbas batada qarfin dazata nema ‘yarta sai tana tareda Mai qarfi.
Batada ra’ayin komawa gida Amma Dr iklimat ta dage akan suje gidan a daidaita Yan uwanta su daura Mata auren da kansu sbd kaucewa wata fitinar gaba.
Bayan ankai ruwa Rana itada Dr da Yan uwanta suka karbeta Bayan sun tabbatarda Mai kudine sosai Wanda zata aura.
Tunda Hadiza tadawo gida Babu Wanda ya tambayi Inda yarta takeba sai Inna wadda take fushi sosai dasu kabiru tun Bayan barin Hadiza gidan.
Ita kanta hadiza Bayan dawowar tata bayan gaisuwa Babu abinda yake hadata da Yan uwanta da matansu da ‘yayansu,
Ta kebe kanta ta tsame daga cikinsu sbd tasakawa kanta Bayan Inna da Dr iklimat batada kowa a duniya.
Wata biyu tayi da dawowa gida akan daura aurenta da MJ Muhammed ta tattara Takoma Abuja gidanta itada Mai aikinta guda daya.
Tunda akai auren hankalinta baya kan mijinta sai akan Neman ‘yarta wadda idan ciwon rashinta yataso Mata kaman zautuwa takeyi.
Tun mj na daurewa har abin yafara damunsa sosai auren ma yafara fice Masa akai.
Rawa auren yafara tun Bai Gama cika shekara ba
Dr na ganin hakan ta tashi tsaye akan Hadiza da fada sbd idan tayi gangancin rasa auren tayiwa kanta.
Ga rayuwarta tuni ta sauya tasamu wadata da Jin Dadi Amma zuciyarta takasa nutsuwa ta rungumi qaddara.
Inna Dr iklimat ta daukowa Hadizan wadda ta zauna tareda ita tana lurar da ita illar datakeson yiwa rayuwarta idan Bata dauki qaddara ta rungumaba.
Ba kunya hardasu Yaya Umar suka ringa kawo Mata ziyara akai akai suna Mata nasihan riqe aurenta.
Tayi iya kokarinta gurin danne damuwarta cikin ranta tafara kyautatawa mj Wanda yake tsananin kaunarta da Gaskia yanzu.
Rayuwar aurenta ta gyaru sbd ganin yanda dangi da Yan uwa kowa nayi da ita sosai sbd abun duniyar datake dashi yanzu Dan haka saita sake nutsuwa da kulawa da mijinta sbd koba komai auren yazama rufin asirinta dayasa kowa ka binta a Yan uwa.
Duk yanda taso cire damuwar yarta Bata iya cirewa duka Wanda hakan yasa mj ya dauketa daga Abuja Inda take tuna babyn ya maidata Lagos yadawo da uwar gidansa Abuja.
Rayuwarta a Lagos tafi ta abujan kwanciyar hankali da nutsuwa sbd ta rage damuwa sosai ta fuskanci gabanta.
Kaman yanda ake cewa dukiya daban take to kusan ta tabbarda hakan,
Yayunta dasuka fara aibata ‘yarta sundawo sune suke gwagwarmaya sosai gurin bincike da Neman Ayshatouh wadda suka yarda da cewan ba shegiyar bace yanzu idanma da Allah suka yarda ko Dan quncin dasuka luradashi kwance qasan ranta Wanda suka tabbatarda har abada bazai goguba,
Kokuwa Dan kudin datake sakar musu sosai gurin binciken Neman ‘yar ne?
Kwadayi da dukiya sunsaka anbata danta Abdulsamad Wanda tasaka a makarantar kudi anan lagos Yana karatu cikin kwanciyar hankali da wadata,
Yan uwan salisu da dama yanzu zumunci da hulda sukeyi da ita sosai Dan kuwa Babu qyashi a zuciyarta tana musu Alkhairi,
Yaya Umar da Yaya kabiru sune tsundum aduk Dan abinda ke gareta sbd mj ba mai Zama bane shiyasa daga ita har uwar gidansa uwar yayansa dukiya yake musu sosai.
Ahaka rayuwarta ta sauya Babu wani labari ko bayanin ganin Ayshatouh da Abdul majeed.
Shekaru sunja sosai manyanci yazo akan dole ta dangana ta cire ran ganin Ayshatouh har abada a qarshema ta sanyata cikin adduar datakewa salisu dasu mama na Allah yayi musu rahama.
Abdul baitaba sanin yanada ‘yar uwaba sbd zancen da aka rufe gabaki dayansa aka barsa amatsayin qaddarar data wuce.
Dr iklimat tazama uwa kuma ‘yar uwa gareta Dan haka bayan mj yayi retire tadawo abuja da Zama Amma sai zaman lfy na Neman gagararta da uwar gidanta Dole aka rabasu ita Takoma Adamawa nata gidan sbd ta nuna Masa tafi ra’ayin Zama acan sbd Kota koma Lagos din tunda yabar Lagos yakoma Abuja ba wani amfani Dan haka tafison Adamawa.
Da wannan ta tattara tadawo adamwa qaton gidanta da MJ yasiya Mata Mai girma daga ita sai Inna da masu aiki sai Dr Abdul idan yazo sbd aiki dayake a asibitin Dr iklimat dake Abuja.
Yaya Umar da Yaya kabiru ma tuni suka zama cikakkun masu rufin asiri da Yar wadata ta sanadin mijin Hadizan daya sakasu cikin wasu Yan haurkokinsa na business Kuma suna samu sosai aciki Dan haka suka sake tsayawa sosai akan duk wata hidimar Hadiza da iyalinta duk da Bata sake haihuwaba tun tsawon shekarun Wanda Dr iklimat tayi Mata bayanin tasamu matsala tun wancan lokacin data samu matsalar gaba ba lallai takuma haihuwaba shiyasa ta dauki tsananin son duniya ta dorawa Dr Abdulsamad sbd ga dukkan alamu shikadaine Dan dazata samu a duniya.