INAYAH 41-50

WANNAN SHINE ASALIN ABINDA YAFARU.
Tsit kowa yayi Banda kukan Haj umma Dana Hadiza saina umma yaganah Babu abinda yake tashi.
Alhaji babbah da cm dama sauran duka mazan gurin duk jarumtarsu jikinsu saidaya yayi tsananin sanyi.
Cm da umma yaganah ne suka Dora da irin gwagwarmayar wahalar rayuwar dayaSha iya wadda suka sani gurin kulawa da Inayah da sauran wahalhalun har arzikinsa.
Duk Wanda yake gurin ya jinjinawa AA MAJEED da irin karfin zuciyarsa.
Ita kanta hadiza jikinta sanyi yayi tareda sabuwar danasani ga girmansa daya cika Ido da zuciyarta sbd duk Wanda ya riqe ‘Yar dabai hada komai da itaba irin hakan Basu taba tunanin zaa samu Mai wannan zuciyarba.
Tun farko nutsuwar da zuciyarta tayi dashi a ganin farko yasata guduwa tabar Masa ‘yarta batareda tunanin komaiba Amma bataba dauka kyan zuciyarsa da karfin zuciyarsa yakai hakan ba.
Hawayen kunya da damuwar abinda tayi dama na tausayin kanta dana majeed take tsayayowa tana sunkuyar dakanta qasa sbd Babu Kuma wani abun fada daya ragewa kowa.
Hajiya umma tafi kowa shiga baqin ciki da Dana sani sbd ko a bayan da hadiza tadawo neman yarta tafada musu gaskiyar su juwairiyyah Basu Bari hajiyar ta yarda da duk abinda Hadiza ta fadaba shiyasa suka hanata bayyanarda damuwarta akan rashin majeed dinta da karfi da yaji Amma tun daga wancan lokacin Bata Kuma isashiyar lafiya ba sbd ciwone da qunci a dunkule ranta na ‘danta datafi so fiyeda komai da kowa.
Su Yaya Umar kusan sunfi kowa kunya da baqin cikin abinda suka aikata dan kuwa kusan sune sanadin komai Dan tun farko dasun rungumi qaddarar Yar uwarsu da duka baa cutatar da wanda baijiba Bai ganiba aka tarwatsa Masa rayuwa aka rabasa da iyayensa.
Alhaji babbah yaji tausayin MAJEED da Hadiza fiyeda kowa sbd kusan kowa mafita take nema a halin matsuwar dasuka shiga Amma tunda kusan komai yazo qarshe Kuma kowa wahalarsa ta wuce tazama tarihi sai kawai a rungumi qaddara sbd duk wannan Al’amarin idan anduba rabon aurene dake tsakanin majeed da Inayah yasa komai yashigo ta hanyar tsanani.
Anty juwairiyyah kunya da takaicin Hadiza harma Dana ‘yarta ya hanata cewa komai har zaman ya tashi kowa ya watse aka bar Yan gidan kawai sai Haj umma da Babu Inda Zata sai ‘danta yadawo Dan bazata iya sake tafiya tabar majeed dintaba sanyin idanuwanta dayaSha gwagwarmaya da wahalar rayuwar duk tarin arzikinsu.
Ta bangare daya jin tayi zuciyarta na Dan qonuwa da Inayah sbd akanta ‘danta ya zabi ya barta,
Ya bar mahaifiyarsa sbd ita,
Ya fifita kaunarta Mai tsanani da duk duniya tasan da Babu abinda yake kauna sbd ita duk da tayi imanin da kaunarta na qasan ran majeed dinta sbd bazai taba daga so da kaunar wani akantaba.
Amma Kuma duk da hakan ya fifita Inayah akanta qarshe yanzu karshen rashin rabuwa ya aureta Wanda ita Sam batajin danta ya cancanta wannan auren sbd tako Ina danta ya cancanta rayuwar Jin Dadi da farin cikin daya rasa shekaru.
MAMUH
HOT LOVE/ROMANCE
MAJEED/INAYAH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: 44
Arewabooks@Mamuhgee
Inayah da kafafuwanta suka kasa riqeta sbd kukan datake Mai tsanani Mara sauti ahankali ta juya tana dafa bango ta nufi dakinta…
Daqyar ta iya Kai kanta daki sbd ko ganin gabanta batayi sbd kuka hannuwanta na toshe da bakinta.
Tana Isa bakin gafo ta silale Wasa ta zauna tana sake sabon kuka.
Abbinta kawai zuciyarta kewa wannan kukan sbd sam ita batajin tanada wani abun tausayi tun jarinta har yanzu sbd Abbinta bai taba Bari ta Zama abar tausayawaba tun tana cikin zanin goyan da uwarta ta yarda ita ta tafiyarta.
Taji tausayi da kaunar mahaifiyarta saidai Kuma har lokacin kaunar kaunar Abbinta daban take a ranta Musamman yanzu datake qaunar tasa na qara nauyi da cikin ranta Dan kuwa har abada Batajin Zata karbi mahaifiyarta matuqar ba abbin ne ya yafe Mata ba ya hadata da ita.
Neesah ce ta fito toilet taga yanda Inayah din ke kuka ta qaraso tana kallonta cikin mamaki da firgici tace”
Lafiya?
Wani abin yakuma faruwa ne?
Haryanzu Baki samu abbin bane a waya?
Kasa magana tayi ajiyar zuciya datake jerowa idanuwanta sunyi jajir.
Umma yaganah ce tashigo dakin fuskarta jajir da alamar kukan datasha sbd tausayin MAJEED datake Jin itama kaunarsa da girmansa sun ninku a ranta sbd ya tabbata Mai tautasayi da kyakkyawar zuciya duba da yanda itama ya riqeta da Maigidanta kafin ya rasu har zuwa rayuwarta daya Gama ingantawa yazama gatanta Mai kare mutuncinta da martabarsu yabasu suna da mutunci a idon duniya.
Tabbas har abada daga ita har Inayah basuda tamkarsa Kuma zasuci gaba da Zama a qarqashin ikonsa da sunan Daya Basu,
Yazama ubansu gatansu Kuma zaici gaba ra zama hakan har abada da yardar Allah.
Inayah na ganin umma yaganah ta sake fashewa da kuka tana fadawa jikinta tana cewa”
Umma yaganah Abbina nakeson gani kawai yanzu,.bana samun wayarsa Dan Allah ki kirasa yadawo gida na Dena duk wani rashin jin magana,,,
Ni har aurenma na karba zanyi auren dashi Dan Allah kice ya Dena fushi Dani yadawo.
Umma yaganah data kasa cewa komai bayanta kawai take Dan bubbugawa tanajin kaunarsu su dukan duk da Inayah tako ina bata Zama abar tausayiba Dan kuwa rayuwarta tagama samun haske tunda MAJEED ya tsaya Mata.
Umma yaganah Bata sake Jin tsananin kaunar auren MAJEED da Inayah dinba sai yanzu Da komai ya bayyana.
A duniya Babu Wanda ya cancanta da Inayah dai Abbinta majeed Wanda shi wannan auren ya zamarwa dukkaninsu RIBA BIYU.
Rarrashinta umma yaganah tayi tareda Neesah wadda take sauraran maimaicin zancen komai abakin umman wadda ke fadawa Inayah komai batareda tasan taji komai ba.
Sun jima a daki suna rarrashin juna kafin a dakin Inayah din dayafi kowane daki girma da tsaruwa a gidan Banda na Abbinta daya banbanta da nata ta hanyar tsarararren palonsa dake hadeda master bedroom dinsa Wanda shima komai na cikinsa milk ne sbd tsananin tsaftarsa yafison komai me haske bazai bayyanar Masa da komai qaqantar datti Dan ya rabu da ita.
Gidan tsit kaman ba kowa saisu zubbi da Salimat dake aikin kaida kawon abinci da maimaicin tsaftace gidan,
Haj umma da Anty juwairiyyah na daki
Anty juwairiyyah sai kame kame takeyi sbd kunyar kanta data mahaifiyarsu saidai Kuma tana maimaitawa Haj umma girman lefin MAJEED dayaqi waiwayo gida ya zabi ‘yar tsintuwa akan mahaifiyarsa.
Itadai Haj umma Bata tankataba sbd yanzu Babu wani Hadi dazai sake rabata da ‘danta ciki kuwa harda Inayah wadda ta tsaya Mata arai sbd kaunar da aketa maimaita majeed dinta nai Mata.
Sai dare kowa ya fito cin abinci suka hade a dining kowa na kallon dan uwansa Banda Inayah wadda kafin ta fito sai yawon zuwa kiranta tazo taci abinci kowa keyi daga umma yaganah har masu aikin da Neesah.
Saida suka fara cin abincin ta fito sanyeda Gucci Riga da wando gajere Wanda ya bayyanarda fararen qafafunta masu kyau da lafiyar fata.
Rigar batada Fadi sosai Kuma Bata saka bra ba sbd kusan Shirin baccine tayi.
Slippers ne a qafarta da wayarta a hannu tana sake saka Kiran Abbinta Wanda duk yakira bai shigaba sai idonta yacika da hawaye.