INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

Qamshinta kawai yasa Anty juwairiyyah sake Baki tana kallonta sbd tasan Qamshin Turaren da tsadarsa tunda tana yawon qasashe.

Haj umma kuwa kayan jikin Inayah din da yanda take wani irin Bata fuska kaman zata fasa kuka take kalla cikeda mamaki,

Lallai yarinyar tasamu sake fiyeda yanda suke tunani.

Zama Inayah tayi Kai tsaye batareda ta kalli anty juwairiyyah ba ta gaida haj umma da cewa”

Haj umma Ina wuni?

Ita kadai ta gaida Dan haka kowa yayi tsit,

A natse hajiyar ta amsa itama batareda takuma kallontaba.

Cikin daure fuska umma yaganah tai Mata nuni da juwairiyyah wadda ke juran Inayah din tawi gaidata Tai mata fada tatas ba ruwanta da gatan dataga yayiwa yarinyar yawa.

A hankali ta gaida anty wadda ta haifeta nesa ba kusaba Dan kuwa yarta ta fari ta girma Inayah din sosai.

Wannan auren datakeyi yanzu yayanta biyu Dan haka yayanta uku
Auren ne irin na yayan masu kudi bawani Zama takeyiba kusan koyaushe taso tana gidansu kokuma yawon wata qasar dauko kayan business,

Anty safiyyah ce kawai take Dan Zama gidanta itama sbd aikinta datakeyi Dan haka Bata wani yawo ko tafiya sai wadda ta danganci aiki
Itama yayanta uku bayansu Bata qaraba ko yanzu da Alhaji babbah dakansa ya aiko nemansu Bata samu biyosu Haj umma ba sbd aikinta da Bata Wasa dashi shiyasa sukazo su kadai.

A taqaice anty juwairiyyah ta amsa gaisuwar tana zuba abincin dazataci.

Zubbi Inayah tafara zubawa tuwon semo da vegetables soup dataji Naman rago da ganda da kifi.

Tana Gama zuba Mata ta kawo Mata ruwa Mara sanyi dan ita batashan ruwa Mai sanyi
Yana daya daga cikin koyarwar Abbinta tun tana qarama baya barinta da sanyi kowane iri ne sbd sanyin dayaso shigarta tun tana jaririya.

Da spoon takecin tuwon Dan haka hankalinta ya rabu akan abincin da wayar hannunta.

Dungurar da wayar tayi da qarfi akan dining tana sakin qaramin tsokin rashin samun Abbinta Dan zuwa yanzu hankalinta yafara tashi da rashin jinsa.

Sudai su Haj umma mamakin duniya yagama cikasu da kallon Inayah wadda shagwabar da ita da akayi take a fili…

Budurwar yarinya likita guda Amma duka halayyarta da dabi’unta kaman wata qaramar baby.

Bata Gama cin abincinba ta miqe zatabar gurin umma yaganah ta dakatar da ita cikin kulawa tace”

Inayah Ina zaki bakici komaibafa a abincin?
Meyasa kike Wasa da cin abinci yanzu?

Shi abbin naki idan yaji bakya cin abinci aikinsan fadan dazaiyi.

Ba dazu kika Gama cewa afadawa Abbinki kin daina rashin jiba?

Dawo zauna kici abinci.

Zubbi da sauri tasake matsowa cikin kulawa tana kokarin zuba Mata wani abincin sbd wannan ya huce
Inayah din tace”

Barshi zubbi zanci wannan din ahaka.

Dawowa tayi badan tasoba ta zauna tana tura abincin.

Kasa riqe mamaki anty juwairiyyah tayi tana Satan kallon Haj umma cikin ranta tana cewa”

Akwai matsala kuwa babba Dan haj umma tazo qarshen kishin ‘danta kila Dan wannan yariyar da alama tagama nisa a tabara Mai lasisi gurin MAJEED.

Koda aka gama cin abincin Saida umma yaganah tasa aka hada fruit salad takaiwa Haj umma daki da kanta harya zauna sukai Dan fira duk da bawani fuska sosai gurin Haj umma din.

Danta MAJEED kawai take buqatan yadawo ta rungumi abinta tashafa kansa ta tsiyayar da hawayenta na shakarun rashinsa dake qasan zuciyarta.

Inayah kuwa hankalinta tashi yayi sosai Dan hakan Bata taba faruwa da itaba na rashin Jin Abbi Kuma Bai sanar da itaba Ina yatafi Dan haka hankalinta yayi masifan tashi daqyar taga safiya.

Duk Wanda yake gidan tun qarfe 6 na safe ta tadasu bacci da tashin hankali harsuma duk saitasa hankalin kowa yatashi sbd kowa yakira wayarsa baya samu

Kosu Haj umma dake basuda numbernsa anbasu kowa yayita Kira baa samu.

Kuka da tashin hankali Babu wanda Inayah bata shigaba ba shiri aka nema CM suka Samar dashi.

Baiso sanar musu tafiya AA din yayiba Saida yaga yanda Inayah ta dagawa kowa hankali tukuna ya kwantar musu da hankalin tafiya majeed din yayi Kuma wayarsa da basa samu sbd layin baya Aiki acan ne.

Hankalinsu ya Dan kwanta anty juwairiyyah Saida tayita fadan yanda Inayah ta dagawa mutane hankali Batasan Haj umma nada hawan jini bane Zata kashe musu ita tunda batada asara.

Itadai Inayah batace komaiba sai Haj umman dataje tabawa hakurin daga Mata hankali datai taqara da cewa bazata sake ba.

Har dare ma still abbin bai kirasu ba haka jiki amace Inayah ta kwana,

Washe gari neesah Zata wuce Dan haka itace da kanta takaita airport tareda Safnah suka rakata ta wuce.

Daga airport gidan anty Hafsat suka wuce.

Acanma anty Hafsat rarrashinta tayi tareda Bata qwarin gwiwa akan auren a fakaici Dan kuwa suma basusan yaushe wannan auren zai Zama cikakke ga ma’auratanba Amma dai kam Zata dage gurin ganin ta ingiza Inayah tako Ina tunda baruwan Inayah din ba doguwar Noke Noke ta iyaba
Babbar matsalar da fargaban na gurin AA MAJEED Wanda kwata kwata matan ne basa gabansa bare Inayah dayakewa kallon ‘yar cikinsa.

Sai yamma tadawo gida bayan umma yaganah tayita kiranta tadawo gidan hakanan.

Koda ta dawo anyi sallar magriba Dan haka daki ta wuce Kai tsaye tayi alwawala tayi sallar magriba ta zauna tana sake gwada kiransa Dana Neesah Amm duka Bata samesuba.

Ajiye wayar tayi ta nufi dakin Haj umma ta gaidata kafin ta fito ta wuce dakin umm yaganah ta taddata tana waya da Yan uwanta dake maiduguri.

Zama tayi gefenta tan saurarenta harta Gama tukuna tace”

Umma yaganah ke kisake gwada Kiran Abbi ko zaa samesa.

Bara mugani to”
Nemo numbernsa tayi tasaka Kira Amma Bata shigaba Dole suka hakura.

Fira umman kewa Inayah Mai Kama da nasiha saiga Kiran Hadiza yashigo wayat umman ta kalli Inayah tace”

Ga mahaifiyarki Nan nakirana.

Dauka tayi da sallama suka gaisa Hadizan ta tambaya ko AA MAJEED din yadawo daga tafiya umma ta sanar Mata Bai dawoba.

Inayah ta tambaya cikin sanyin murya da jiki.

Kallon Inayah umma tayi kafin tace”

Lafiyanta kalau gatanan zaune Bata nabata ki gaisa…..

Aa,aa kyaleta tunda naji lafiyartama ya Isa zanci gaba da jira har AA din yadawo kaman yanda nayi alqawari Inshallah Zan jira sai ranarda ya yafemun ya hadani da ita Dan kansa Zan tunkareta.

Tausayin Hadizan yasa umma Dan rintse Ido tana cewa”

MAJEED baida matsala Inshallah idan Anbi komai a hankali zakiga da kansa zai hadaku.

Godiya Hadiza tayi kafin sukai sallama suka aje wayar.

Inayah shiru tayi batace komaiba
Itama umman tana aje wayar batacewa Inayahn komaiba.

Tashi sukai Sakai sallar ishai suna gamawa Inayah tayi dakinta jikinta a mace tanajin wata irin damuwa da tashin hankalin rashin ji daga Abbinta.

Wanka tayi tana fitowa ta sanya D&D off-white Riga da wando masu Dan kauri Amma guntaye Dan wandon Bai Gama kaiwa gwiwarta ba Amma yanda Fadi sosai
Rigar kuwa daidai jikinta ce saidai yau tasaka condom bra.
Kanta farar qaramar wulace akanta data bayyanarda kusan Rabin gashinta dayake sauran gyaran aurenta har lokacin.

Slippersta ziro ta fito qamshinta Mai dadi Yana tashi daga jikinta ahankali.

Tun kan ta iso palon anty juwairiyyah tajiyo Dan qamshinta Dan haka ta waiwayo tana tallon hanyar kofar dakin Inayah din.

Dukkaninsu me zaune a palon har Haj umma da umma yaganah sun Dan zatawa sama sama.

Zuwansa yasa Haj umma kallonta ta dan dauke kai sbd kayan Inayah din kullum Babu na arziki tasaba da rayuwar turai da sakewa a gida ba ruwanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button