INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

INAYAH 41-50

Ni har aurenmu ma na karba zanyi
Amma Dan Allah Abbi ka yafemun…..

Hawaye tafara tana riqeda hannunsa cikin yanayi da dana sanin lefin data aikatadin duk da batasan takamaimai akwan wanne daga cikin lefin take fushi da itaba.

Nauyin mahaifiyarsa mai tsanani yakeji Musamman ganin duk sunyi zuru suna kallon ikon Allah Dan Inayah dinnan tafara wuce tunaninsu
Gashi kaman majeed din biye Mata yake da alama shiyasa tabarar tata take yawa.

Zame hannunsa yayi Yana kallon umma yaganah yace”

Kuje ciki zamuyi magana gobe idan na nutsu.

Gangarowa hawayen Inayah sukayi tace”

Abbi gobe?
Nidai bazan iya bacci ba idan baka dena fushi daniba ka yafemun.

A natse ya juyo ya kalli fuskarta cikin kulawa yace”

Bana Hana wannan kukan ba?
Kije ki saka kayan sanyi
Anjima zamuyi mgn.

Ok Abbi” tace muryarta a sanyaye.

Tashi tayi ta wuce umma yaganah tabita suka Basu guri yabisu da kallo kadan sbd yasan Inayah saitayi kukan idan suka Isa daki.

Baki sake Haj umma suke kallonsa
Ya dawo da kallonsa kanta Yana sake Jin farin ciki.

Bata Bari Inayah tashiga damuwarta akan danta ba sbd tasan Babu Wanda zai taba samun matsayi irin nata a zuciya da rayuwar ‘danta.

Anty juwairiyyah Kuma mamaki da tunanin zaman da Haj tace zatai a gurin ‘danta takeyi Dan kuwa akwai matsala.

Haj na kishin ‘danta
Inayah ma da alama batason kowa ya rabi Abbinta sbd ta taso da kaunarsa da kulawarsa akanta ita kadai Bai taba hada kaunarta da kulawarta da komaiba Dan haka a take tagano Inayah ma zatai kishin wani ya rabi Abbin nata Wanda yake mijinta yanzu duk da ba mijin ta daukaba haryanzu a Abbinta yake.

Hmmmnn””ta sauke ajiyar zuciya a fili.

Sun dade a palon sosai suna magana kafin yasamu ya nufi dakinsa.

Akwatinsa daya dawo da ita yafara ajewa closet kafin ya tube ya fada toilet.

Wanka yayi tareda alwala yafito sanyeda bathrobe fara ya nufi gaban mirror yafara tsane jikinsa.

Bawani dogon shiri yayiba yagama ya tada sallar magriba da ishai dake kansa.

Inayah kuwa suna Isa daki ta zauna kan sofa tana kokarin tsaida hawayenta,

Umma yaganah Bata zaunaba tana kallonya daga tsaye tace”

Ki nutsu Inayah kisan yanzu bamu kadai bane a gidan akwai mutane,

Mahaifiyar majeed ake magana bazance kakarkiba yanzu saidai nace uwar mijinki ce,

Bakowane shiga zakina yiba yanzu sbd Bai kamataba,
Dacan dakikeyi baa hanakiba sbd mune kadai a gidan Kuma Kinga wancan lokacin Abbinki mahaifinda ya haifeki muke mgn Amma yanzu hakan zai iya saka wani abin daban Musamman agaban hajiyarsa sbd yanzu Kam mahimmancinta yafi na kowa da komai a gunsa…

Shiru Inayah tayi Jin abinda umman tafada Kuma ya taba zuciyarta sosai dahar take sake Jin zafi da ciwon rashin zamanta jinin Abbin.

Har umma yaganah ta fice shiru take tana kokawa da ‘dacin ranta na cewan yanzu akwai Wanda yafita matsayi gun Abbinta.

Hawaye taji suna neman cika idonta na kishin hakan itama,
Saidai duk matsayin hajiya agunsa batajin nata matsayin itama zai sauka sbd Abbinta ai yanzu harda mijinta ya Zama Dan haka itama matsayinta biyu akansa bazata yarda a qwace Mata matsayinta na Yar gatan Abbinta ba Kuma ai itace sanyin idaniyansa kaman yanda kowa yasani Dole itama Haj umma tayarda da itace Yar lelen Abbi.

Ranta a cunkushe ta dauki wayarta dake ringing taga sunan anty Hafsat ta dauka tana farawa da cewa”

Anty Hafsat Abbi yadawo,
Amma yanzu Haj umma ce…..

Tareta anty Hafsat tayi da cewa”

Ashe tashin hankali yaqare tunda yadawo
Kuma ya tadda hajiyarsa
Fatan dai Kun taru Kun tayasa Murna?

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa”

Eh mun Masa Murna sosai ai tun baima dawoba kinsani.
Sanyi jikinta yayi ahankali tace,

Yanzu anty Hafsat Abbi zaifi son Haj umma akaina ko?

Murmushi Anty Hafsat tayi tana tausasa murya tace”

Inayah mahaifiyarsa cefa,
Tayaya bazaifi Sonta akan kowaba?
Ai uwa ba Wasa bace,
Kema Taki uwar duk abinda tayi haka zakiyi hakuri ki rungumeta sbd itama shedan ne kawai yashiga zuciyarta bawai Dan bata sonkiba.

Banajin haushin umma Hadiza anty Hafsat Amma dai zuciyata tafi kaunar Abbi haryanzu akanta sbd bansantaba,
Bantashi da kauna ko soyayyar uwaba saita uba Wanda kaunarsa ta ginu araina shi kadai tun ina qanqanuwa,
Abbina Ni kadaice tasa Amma yanzu da hajiyarsa tadawo yafi Sonta akaina.

Kasa cigaba da magana tayi Tai sallama da Anty Hafsat din ta jefar da wayar.

Zubbi ce tai knockin tashigo dakin cikin kulawa tace”

Umma yaganah tace kifito zakuci abincin kowa yafito.

Gyada Mata Kai kawai tayi a gundure tace”

Kije am coming.

Bayan fitar zubbi Saida ta dauki mintuna tana danne damuwar zuciyarta kafin ta miqe ta nufi closet dinta ta dauko dogon wandon Burberry kawai ta saka batareda ta sauya rigaba ta fita.

MAMUH

LOVE/ROMANCE/A&I

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810746
Arewabooks@Mamuhgee
Tana fitowa Kai tsaye dining room ta nufa jikinta sanyaye da sabuwar damuwar data saukar mata arai.

Da kallo suka bita data iso sbd ganin Bata sauya kayanba kawai dogon wando ta Sako ta suturta dogayen qafafuwanta dake bude a fili dazu.

Zama tayi ahankali batareda tace komaiba.

Drink din da Umma yaganah tazo dashi daga kitchen ta ajiye kan table tana cewa”

Inayah kije ki sanarda MAJEED table yazama ready.

Tanajin haka ta miqe har lokacin jikinta a sanyaye ta juya Zata tafi saiga qamshinsa yafara isowa take tasan yana hanyar shigowa ta dakata tana kallon kofar.

Reebok hoodie wears ne ajikinsa farare sai black Valentino slippers.

Fuskarsa fresh as usual kaman sabon saurayi ba damuwan komai saidai nutsuwa da sanyinsa daya Riga ya kama rayuwarsa tun barinsa gida Dan haka wannan walwalar da faran faran ba lallai yadawoba.

Inayah ya kalla da fararen idanuwansa take yagano sanyinta.

Ajiyar zuciya ya sauke a Dan takaice kafin ya kalli qafafunta yaga ba safa ga kayanta dai ba wani na arziki bane.

Da kulawa yace”

Menene Kuma yanzu kike Bata fuska?

Ba nace abar kukan hakaba?

Biyosa tayi tana sake marairaice murya tace”

Abbi ni haryanzu Banga ka yafemun bane ai to.

Da nutsuwa yace”

Saikin Dena yawan kukan Nan da Kuma Jin maganar umma yaganah.

Zama sukai a dining Haj umma na kallon ‘danta tana Masa adduar kariya daga mugun Ido da mugun Baki sbd ‘dan nata tubarkallah yakoma Mata tamkar ba itace ta haifesaba fes kaman Dan baqaqen larabawa.

Cikin girmamawa ya sake gaidasu Haj umma kafin suka fara cin abincin.

Inayah ta zuba Masa abincin iya yanda tasan yanaci sai gashi ko farawa baiyiba Haj umma tace”

Majeed ko abinci bakaci sosai kenan yanzu?

Murmushi yasake ahankali Yana diban brown rice din yakai bakinsa yace”

Kusan komaiba ya canja umma ai.

Murmushi tayi itama tana cewa”

Duk da hakan Bai kamata kana Wasa da abincinba duk busy din dazaka Zama kuwa,

Yaganah haka kuna kallo yake Wasa da abinci?

Wani rolling da Ido Inayah tayi cikeda mamakin zancen hajiyan tace”

Abbi da daddare ne bayacin abinci sosai Amma ba ranarda Zan bar Abbina da yunwa tun dama can….

Dangwalar cinyarta umma yaganah tayi alaman tayi shiru Amma hakan kawai takejin bazata Bari Haj umma ta nuna tafiya son Abbinta ba.

Cikin nutsuwa da kulawa Abbi yace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button