JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 46

sha Allah my captain, i love you so much” Ya sauke wani boyayen ajiyar xuciya, yana sake kallon agogo wai har karfe goma saura mace na saman gadonta, kwantar da ita yayi ya mike yace “I want to take my bath, kinsan yau xan koma gun aiki fa” Ta xaro ido tace “Kai da ya kamata ka dau sati captain? Ko basu san aure kayi ba” Yace “No iyakar kwanakin da aka bani kenan, kinsan my first marriage an bani almost 2 weeks, and this is my second marriage….” Da mamaki take kallonsa kafin ta katse sa da sauri

tace “Kai har kana da wani first marriage da kake tutiya da shi Captain?” Yace “Ohh toh ya xan kirasa? Aure ne shi ma ai” Ta hade rai tace “Wannan kuma ya rage naka, amma take note aurenmu shine first and last marriage dinka” Yana cire jallabiyar jikinsa yace “Toh ai wajen aiki babu ruwansu, a first marriage dina suka san wancan hutun da suka bani, wannan kuma second marriage…” Kallonsa kawai take from head to toe babu ko kiftawa

don Abuturrab ya kai namiji wanda ko wace mace xata so shi a matsayin mijinta, daga sama har kasa kawai take kallonsa tana sake imagining din discuss dinsu, wai yana da issues, Issues a hakan da take ganinsa? Kamar ya san tunanin da take ya juya yayi shigewarsa bandaki ya kulle, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin wani shaukinsa na taso mata, ta kwanta gefen gado hade da lumshe ido. Jiddah na tsaye dakinsu tana jera kayansu da mai wanki da guga ya kawo a press, Maimoon ce kwance dakin tana baccin wahala saboda cramps da ya sakota gaba ko boko bata je ba ranan, Jiddah kuma

shigowarta kenan malamarta ta wuce, shine take gyaran kayan kafin Mu’allimarta na Islamiyya ta xo, Umma ce ta bude kofar dakin, tana kallon Maimoon tace “Ta samu bacci kenan” Jiddah tace “Ehh tayi bacci” Umma ta kalli Jiddah na few seconds kafin tace “Jiddah ki xo daki ki sameni idan kin gama” Jiddah tace “Toh” Umma ta juya ta fita, sai da Jiddah ta gama jera kayan nasu sannan ta fita xuwa dakin Umma, Umma na xaune kan arm

chair dake dakin, Jiddah ta xauna saman carpet, duk da yanda gabanta ke faduwa don yawanci kiran Umma baya wuce warning xata mata, shima warning din a kan Abuturrab, to amma ai yau kusan wata kenan bata gansa da idonta ba, a hankali tace “Umma gani” Umma na kallonta tace “Jiddah baki ta6a xuwa kin sameni kince kina son Pad xakiyi al’ada ba” Jiddah ta sunkuyar da kanta a hankali amma bata ce komai ba, Umma tace “Ko baki fara ba ne?” Ta girgixa kai tace “Aa na ta6a yi sau biyu kuma ban sake yi ba” Umma tace “A ina kika ta6a yi?” Ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Ya dade, tun ina gun Baabarmu, lkcn ban daina xuwa islamiyya ba” Umma tace “Xai kai wata nawa?” Jiddah ta buda ido sosai tace “Umma xai yi kusan shekara

biyu” Umma ta gyada kai tace “Ikon Allah, kuma shine baki sake ba har yau?” Jiddah tace “Eh” Umma tace “Toh tashi ki tafi” Mikewa tayi ta juya ta fita dakin, Umma ta bi ta da kallo tana tunanin meye ma’anar hakan, Jiddah na fita ta sauke ajiyar xuciya ita ko fata ta sake yi bata yi har abada, don bata mance wahalan da ta sha ba har sai da aka kaita chemist aka ta mata allurai, Iyah har ce mata tayi sumanta biyu. Ranan Friday da yamma Ahmad na xaune bedroom din Ummansa, ko minti talatin bai yi da shigowa ba Umma tace “Yauwa Ahmad ina son maka tambaya, Me ke janyo mace ta fara al’ada kuma ta daina sa ko ya dinga mata wasa?” Ahmad yyi shiru yana kallonta, can yace “Mace yar shekara nawa Umma?” Tace “Yarinya karama…” Ahmad yace “Irregular period kenan…” Umma tace “Oho nima ba tambayarka nake ba” Ya shafa kansa yace “Mai aure ce ko mara aure Umma?” Umma tace “Aa bata da aure” yace “That could be Hormonal Imbalance, too high or too low Thyroid hormone level, wannan shine dalilin in har mara

aure ce… ” Umma tace “To yana da medications ne? I mean is there anything that could be done about it?” Yace “Ehh ba xa a rasa ba Umma, amma akai ko ma wacece asibiti xai fi” Umma tace “Toh Shikenan” Bai kuma cewa komai ba amma can kasan xuciyarsa ya san Jiddah ce Umma ke magana a kai, Umma ta shigo da wata hiran, sun jima suna magana kafin ya mike yace mata xai je gidan Abuturrab don yana gari, Umma tace “Toh sai ka dawo” Yace “Daga can xan tafi gida Umma, sai gobe xan shigo in sha Allah” Tace “To ka gaida Ramlah” Yace “Xata ji in sha Allah” Ahmad na fita wajajen karfe biyar Umma ta sa Jiddah ta shirya suka wuce asibiti, Basu suka dawo

gida ba sai bayan magrib, magunguna kawai aka dora Jiddah a kai, xata wuce daki rike da ledan maganin, Umma da ta xauna parlor bayan ta cire Hijab dinta tace “Baki dai manta dosage din ba ko? Duk da an ma rubuta a jiki ai” Jiddah ta juyo tace “Ban manta ba Umma” Umma tace “Toh kar dai kiyi wasa da shan su, Allah ya sa a dace” Jiddah tace “Nagode Umma” Daga

haka ta wuce dakinsu, Umma ta kashe ya fi dubu talatin a magungunan da aka rubuta ma Jiddah a asibitin da suka je. Washegari asabar tare Ahmad ya shigo gidansu da Abuturrab, babu yanda Ahmad bai yi da Abuturrab su tafi dakin Umma ba don tana ciki amma yaki ya xauna parlor wai xa su gaisa idan ta fito, Ahmad ya wuce dakin Ummar tasa, Maimoon ce ta fito

daga dakinsu da uniform din Islamiyyarta fuskarta kunshe cikin nikab, ganin Abuturrab xaune a parlor tace “Ina yini yaya” Kai kawai ya gyada mata, ta murguda baki daga cikin Nikab din ta nufi kofa, Safiyya ma na fitowa ta gaishesa tayi hanyar kofa, Kallon kofar dakin kawai yake, sai ga Jiddah ta fito tana kokarin daura nata nikab din, suna hada ido tayi turus a inda take, sai kuma ta dauke kanta ta nufi kofa ta fita parlon ta kulle kofar, mikewa Abuturrab yayi ya nufi dakin Umma ya kwankwasa sannan ya bude yayi sallama, bai shiga can cikin dakin ba ya gaisheta da ladabi daga bakin kofar, ta amsa masa tana tambayarsa aiki, yace “Alhmdlh” Umma na kallon Ahmad yace “Yaran nan basu tafi makarantar har yanxu ba ko?” Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, ta mike ganin fita xata yi Abuturrab ya bata hanya ta fita, dubawa tayi ko sun tafi ganin sun tafi din ta dawo, Abuturrab yace “Dama na xo gaisheki ne Umma sai anjima” Tace “Toh

nagode” Yana kallon Ahmad yace “Mu yi waya” Daga haka ya juya ya fita, har su Maimoon sun kai bakin titi da kafa tunda ba driver xai kai su ba, yayi parking a gefe yana kallon Safiyya yace “Ku shigo inyi dropping dinku” Sake baki Maimoon tayi cikin Nikab din, tunda take xata iya cewa bata ta6a shiga motarsa ba, ko a hanya ya ganka da ka hau motarsa gwara ya baka kudin mota ko kuma yayi kamar bai ta6a saninka ba, Ita kanta Safiyya mamaki ya cikata, ta dai bude gaban motar ta shiga, Jiddah dai bata ji dadin shiga motan da yace su yi ba, Maimoon ta fara shiga sannan

ita ma ta shiga, jikin door din motar Jiddah ta makale ko da wasa bata kalli inda yake ba, Yayi breaking silence din motar bayan sunyi nisa yace “Yaushe Siyama xata dawo?” Safiyya tace “Tab, ta fara karatu fa a can yaya” Yace “To maa sha Allah” Maimoon ce tayi masa kwatancen inda makarantar tasu yake, yana isa makarantar yayi parking bakin gate, Safiyya ce ta fara sauka tana masa godiya, Jiddah ta bude side dinta ba tare da ta kallesa ba ta sauka motar ta wuce cikin makaranta ya bi ta da kallo, Maimoon dake masa godiya taga ya bi Jiddah da kallo ta d’an kikkifta ido tana kallonsa, can dai ta sauka motar ta kulle masa ta bi

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button