JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 46

Ad

_____

aure ce… ” Umma tace “To yana da medications ne? I mean is there anything that could be done about it?” Yace “Ehh ba xa a rasa ba Umma, amma akai ko ma wacece asibiti xai fi” Umma tace “Toh Shikenan” Bai kuma cewa komai ba amma can kasan xuciyarsa ya san Jiddah ce Umma ke magana a kai, Umma ta shigo da wata hiran, sun jima suna magana kafin ya mike yace mata xai je gidan Abuturrab don yana gari, Umma tace “Toh sai ka dawo” Yace “Daga can xan tafi gida Umma, sai gobe xan shigo in sha Allah” Tace “To ka gaida Ramlah” Yace “Xata ji in sha Allah” Ahmad na fita wajajen karfe biyar Umma ta sa Jiddah ta shirya suka wuce asibiti, Basu suka dawo

gida ba sai bayan magrib, magunguna kawai aka dora Jiddah a kai, xata wuce daki rike da ledan maganin, Umma da ta xauna parlor bayan ta cire Hijab dinta tace “Baki dai manta dosage din ba ko? Duk da an ma rubuta a jiki ai” Jiddah ta juyo tace “Ban manta ba Umma” Umma tace “Toh kar dai kiyi wasa da shan su, Allah ya sa a dace” Jiddah tace “Nagode Umma” Daga

haka ta wuce dakinsu, Umma ta kashe ya fi dubu talatin a magungunan da aka rubuta ma Jiddah a asibitin da suka je. Washegari asabar tare Ahmad ya shigo gidansu da Abuturrab, babu yanda Ahmad bai yi da Abuturrab su tafi dakin Umma ba don tana ciki amma yaki ya xauna parlor wai xa su gaisa idan ta fito, Ahmad ya wuce dakin Ummar tasa, Maimoon ce ta fito

daga dakinsu da uniform din Islamiyyarta fuskarta kunshe cikin nikab, ganin Abuturrab xaune a parlor tace “Ina yini yaya” Kai kawai ya gyada mata, ta murguda baki daga cikin Nikab din ta nufi kofa, Safiyya ma na fitowa ta gaishesa tayi hanyar kofa, Kallon kofar dakin kawai yake, sai ga Jiddah ta fito tana kokarin daura nata nikab din, suna hada ido tayi turus a inda take, sai kuma ta dauke kanta ta nufi kofa ta fita parlon ta kulle kofar, mikewa Abuturrab yayi ya nufi dakin Umma ya kwankwasa sannan ya bude yayi sallama, bai shiga can cikin dakin ba ya gaisheta da ladabi daga bakin kofar, ta amsa masa tana tambayarsa aiki, yace “Alhmdlh” Umma na kallon Ahmad yace “Yaran nan basu tafi makarantar har yanxu ba ko?” Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, ta mike ganin fita xata yi Abuturrab ya bata hanya ta fita, dubawa tayi ko sun tafi ganin sun tafi din ta dawo, Abuturrab yace “Dama na xo gaisheki ne Umma sai anjima” Tace “Toh

nagode” Yana kallon Ahmad yace “Mu yi waya” Daga haka ya juya ya fita, har su Maimoon sun kai bakin titi da kafa tunda ba driver xai kai su ba, yayi parking a gefe yana kallon Safiyya yace “Ku shigo inyi dropping dinku” Sake baki Maimoon tayi cikin Nikab din, tunda take xata iya cewa bata ta6a shiga motarsa ba, ko a hanya ya ganka da ka hau motarsa gwara ya baka kudin mota ko kuma yayi kamar bai ta6a saninka ba, Ita kanta Safiyya mamaki ya cikata, ta dai bude gaban motar ta shiga, Jiddah dai bata ji dadin shiga motan da yace su yi ba, Maimoon ta fara shiga sannan

ita ma ta shiga, jikin door din motar Jiddah ta makale ko da wasa bata kalli inda yake ba, Yayi breaking silence din motar bayan sunyi nisa yace “Yaushe Siyama xata dawo?” Safiyya tace “Tab, ta fara karatu fa a can yaya” Yace “To maa sha Allah” Maimoon ce tayi masa kwatancen inda makarantar tasu yake, yana isa makarantar yayi parking bakin gate, Safiyya ce ta fara sauka tana masa godiya, Jiddah ta bude side dinta ba tare da ta kallesa ba ta sauka motar ta wuce cikin makaranta ya bi ta da kallo, Maimoon dake masa godiya taga ya bi Jiddah da kallo ta d’an kikkifta ido tana kallonsa, can dai ta sauka motar ta kulle masa ta bi

bayansu Jiddah da sauri, dafe Jiddah tayi bayan sun shiga gate tana xaro ido tace “Jiddoh ya naga Captain ya bi ki da kallo???” Jiddah ta kalleta da sauri tace “Waye haka?” Maimoon ta fashe da dariya tace “Ya Aliyu mana, wllh ina ta ce masa mun gode tsabar yanda ya bi ki da eyes bai ma san ina magana ba Jiddoh” Safiyya dake jin su tayi dariya tace “Kallon godiyan da bata masa ba yake mata, naga ko kallonsa bata yi ba ta sauka abunta ta wuce, kilan abinda ya basa mamaki kenan ya bi ta da kallo” Maimoon tayi shakaf da hannu tace “Habaa… no wonder, I for say, wllh kinga wani kallon da ya bi ki da shi, kuma da gaske ne baki masa godiya ba wllh, next time kar ma kiyi gigin sake shiga motarsa don disgaki xai yi wllh” Jiddah ta ta6e baki tace “Wannan ma banyi niyyar shiga ba” Ahmad yayi ma Umma sallama xai fita tace “Yauwa ina son magana da kai Ahmad, kuma kar kuyi missing train ko?” Ya kalli agogon wrist dinsa ya koma ya

xauna yace “Da d’an sauran time, ina jin ki Umma” Ramlah dake xaune gefen gadon Umma rike da handbag dinta ta tashi xata fita Umma ta kalleta tace “Ina kuma xa ki, dawo kiyi xaman ki” Ramlah tace “Aa Umma xan shiga bandaki ne” Daga haka ta fita, Umma tace “Ji shashasha” Shi dai Ahmad murmushi kawai yayi, Umma tace “Makarantar boarding nake son da a sama ma Jiddah, Cause her capacity is now more than mere lesson, tana da kokari sosai Ahmad fiye da yanda kake tunani, Malamar ma ta bada shawaran kawai ta tafi boko da mates dinta she now have a standard root” Ahmad yace

“Boarding kuma Umma? why not day, ai bata da wasa balle ace taje boarding, sannan gwara day din saboda koyon abubuwan yau da kullum, irinsu girki, da dai sauransu Umma, Jiddah bata da hayaniyar da xata iya xama a boarding school gaskiya” Umma tace “To ai ba sai me hayaniya ke xuwa boarding ba Ahmad” Umma tace “Yanxu dai shawarata kike nema Umma, kuma shawaran da xan baki shine a samar mata day ta fara daga ss1, she can do it” Umma ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Toh shkkn” yace “Yauwa Umma, kinga baxa ayi depriving dinta from full Islamic education ba in jeka ka dawo ne” Umma tace “Kuma haka ne, amma wacce makarantar kake ga xa a saka ta?” Yace “Tunda su Maimoon sun kusa gamawa kawai a nema mata wani daban ita ma, akwai wata makaranta not to far away daga gidana ko a

Ad

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button