JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 46

bayansu Jiddah da sauri, dafe Jiddah tayi bayan sun shiga gate tana xaro ido tace “Jiddoh ya naga Captain ya bi ki da kallo???” Jiddah ta kalleta da sauri tace “Waye haka?” Maimoon ta fashe da dariya tace “Ya Aliyu mana, wllh ina ta ce masa mun gode tsabar yanda ya bi ki da eyes bai ma san ina magana ba Jiddoh” Safiyya dake jin su tayi dariya tace “Kallon godiyan da bata masa ba yake mata, naga ko kallonsa bata yi ba ta sauka abunta ta wuce, kilan abinda ya basa mamaki kenan ya bi ta da kallo” Maimoon tayi shakaf da hannu tace “Habaa… no wonder, I for say, wllh kinga wani kallon da ya bi ki da shi, kuma da gaske ne baki masa godiya ba wllh, next time kar ma kiyi gigin sake shiga motarsa don disgaki xai yi wllh” Jiddah ta ta6e baki tace “Wannan ma banyi niyyar shiga ba” Ahmad yayi ma Umma sallama xai fita tace “Yauwa ina son magana da kai Ahmad, kuma kar kuyi missing train ko?” Ya kalli agogon wrist dinsa ya koma ya

xauna yace “Da d’an sauran time, ina jin ki Umma” Ramlah dake xaune gefen gadon Umma rike da handbag dinta ta tashi xata fita Umma ta kalleta tace “Ina kuma xa ki, dawo kiyi xaman ki” Ramlah tace “Aa Umma xan shiga bandaki ne” Daga haka ta fita, Umma tace “Ji shashasha” Shi dai Ahmad murmushi kawai yayi, Umma tace “Makarantar boarding nake son da a sama ma Jiddah, Cause her capacity is now more than mere lesson, tana da kokari sosai Ahmad fiye da yanda kake tunani, Malamar ma ta bada shawaran kawai ta tafi boko da mates dinta she now have a standard root” Ahmad yace

“Boarding kuma Umma? why not day, ai bata da wasa balle ace taje boarding, sannan gwara day din saboda koyon abubuwan yau da kullum, irinsu girki, da dai sauransu Umma, Jiddah bata da hayaniyar da xata iya xama a boarding school gaskiya” Umma tace “To ai ba sai me hayaniya ke xuwa boarding ba Ahmad” Umma tace “Yanxu dai shawarata kike nema Umma, kuma shawaran da xan baki shine a samar mata day ta fara daga ss1, she can do it” Umma ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Toh shkkn” yace “Yauwa Umma, kinga baxa ayi depriving dinta from full Islamic education ba in jeka ka dawo ne” Umma tace “Kuma haka ne, amma wacce makarantar kake ga xa a saka ta?” Yace “Tunda su Maimoon sun kusa gamawa kawai a nema mata wani daban ita ma, akwai wata makaranta not to far away daga gidana ko a

samar mata a can?” Umma tace “Aa gidanka yayi nisa sosai gaskiya” Ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Toh sai ta xauna gidan nawa mana Umma” Wani kallo Umma tayi masa daga sama har kasa kafin tace “Toh baxata xauna ba” Dariya yayi yace “Kema kinsan Ramlah bata da matsala Umma and she can do so many cooking da Jiddah xata iya koya, don ma yanxu bata da lafiya sosai” Umma tace “To ubana nace Aa, daga nan xata dinga xuwa makarantar…” Yace “Toh shkkn Umma, sai driver ya dinga kai ta, idan

xata dawo kuma ta samu abun hawa tunda kinga hanya ce” Umma tace “In dai am samu nan kusa kusa a samar mata admission kawai, don unguwar da kake yyi nisa” Ahmad bai kuma cewa komai ba, can ya mike yace “Toh shkkn Umma, xa mu yi waya kar muyi missing train” Umma tace “Toh Allah ya tsare hanya, ya kiyaye, kuma ku yi addu’a” Yace “In sha Allah” Daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa…..

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button