KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 31 to 40

Maryam Obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  75to80

Suka hada ido da salma yace salma nasan wannan yarinyar, tace a ina?? Yace tana yawan zuwa office dina kwanaki daka baya na daina ganinta, tunda na ganta naji kaman tana naiman taimako Amma Allah baisa na taba tsayawa naji mai take nema ba, salma tace Allah sarki komai ai sai Allah ya nufa, Allah ya bata lafiya sai kaji matsalanta inna taimakawa ne a taimaka mata, ya amsa da ameen, nan ya kira driver yace ya kwantar da hankalinshi insha Allah zata tashi babu abunda zai sameta, driver yayi ajiyan zuciya tare da fadin Allah yasa oga hankalina ya tashi sosai ban taba bige ko kaza ba amma na fara da buge mutum, Mahmud yace idan Allah yasa abu zai faru babu mai hanashi, dan haka kayi imani da hakan, yace hakane oga ngd, nan Mahmud ya zaro kudi ya bashi yace ya siyo musu abinci, ya amsa cikin ladabi ya fita,

Mahmud yana tare da salma har driver ya dawo yarinyar bata farka ba, Mahmud ya cire nasu da drinks, sannan yace ya dauka yaba ma matar nan itama, nan ya amsa da to ya fita, Mahmud ya bude fried rice ne, da kaza rabi a ciki, da garden salad, nan ya fara ba salma tana ci harta kochi, sannan shima ya samu yaci, bayan ya Gama ya kalleta yace salma ta amsa da na’am, yace mai yasa kika shiga kitchen bayan nace kar kiyi aikin komai? Tace kayi hakuri Mahmud bayan ka fita ne, nace bari inje inma abinci dan naji jikina da sauki kuma na gaji da zama waje daya, ina cikin aikin…. Tayi shuru yace inaji tace ban San maiya faru ba kuma sai dai na ganni a nan, shuru yayi yana kallonta kaman yana son gano wani abu, can yace salma dan Allah daka yau koda mun koma gida ban son ki kara yin wani abu da kanki, inaso kimin alkawari, Tayi shuru tana kallonshi, tace insha Allah bazan kara yiba, har sai na warke sosai, yace no koda kin warke bana son kiyi komai har sai kin haiyu, ban San matsala, tayi dariya tare da fadin shikenan koda yaushe ni mai bin umarninka ce, yayi murnushi tare taba mata hanci, jin motsin yarinyar nan yasa sukai saurin waigawa da sauri, Mahmud yayi wajanta da sauri ya danna wani abu ja, ko minti biyu ba’ayi ba saiga Dr ya shigo dasauri, nan ya fara dubata ganin numfashinta ya koma normal aka cire mata oxygen din, Dr yace mata ya jikin tace da sauki cikin sanyin murya, yace inane yake miki ciwo? Ta nuna mai kanta, yace kiyi hakuri a hankali zai daina, ya kalli Mahmud yace jikin da sauki sai dai ciwon da taji shine yake damunta, nan Mahmud ya godema Allah ganin ta tashi kuma ance jikin da sauki, Dr yasa a fitar dasu daka emergency asa su cikin wani daki, salma tace a kaisu na mutum biyu ita da yarinyar kar a raba su, hakan koh akayi, lokacin da aka fito dasu za’a kaisu dakin driver da mmn yarinyar suka taso a tsorace ganin yarinyar idonta bude tana dago hannu tana mika ma mmnta yasa driver yaji dadi tare dayi ma Allah godiya, tana rike da hannun mmn sukai dakin, nan mmn ta saki kuka tana fadin ya jikin naki? Ta amsa dasauki, tasa hannu tana share mata hawaye tare da fadin aina warke kin sha naki maganin? Ta amsa da eh nasha, salma taji sun bata tausayi, tace mama kiyi hakuri Dr yace babu komai dake damunta yanzu ciwon jikinta ne kawai, shima insha Allah zai warke da wuri, matar da waigo tana kallon salma tace Allah yasa hakan ita daya gareni sai yasa na shiga damuwa ina tsoran in rasa ta, sai a sannan Mahmud yayi magana yace insha Allah babu abunda zai sameta,

Kwanan su hudu aka sallame su, a dan kwanakin da sukayi salma ta fahimci matar kaman tana da wani ciwo, tana yawan shan magani, in bata shaba yarinyar zatai ta mata magana tasha, gashi bata San shiga cikin dakin wanda ako da yaushe zaka ganta a waje, sai anyi dakyar zata shigo ta rakube wajan gadon yarta, suna hada kaya salma tace mama yanzu dai sai kuxo muje gidan mu, idan kuka kimtsa sai a kaiku gida, nan matar tace a’a babu inda zasu sun gode, saida mahmud ya shigo ta fada mai sannan yayi mata magana shine ta yarda, driver ya dibi matar ya fara tafiya dasu sannan ya dawo ya kwashi su salma, dakin baki driver ya kaisu, koda su salma suka je gida fauxiya bata nan, nan Mahmud ya bada kudi a kawo musu abinci, ba’a dade ba driver ya kawo, ya bashi na matar yace ya kai mata sannan yayi sama dana hannunshi, ya tarar salma bata dakin ya daiji kanshi sabulu a nan ya gane tana toilet, ya xauna bai dade ba ta fito, ido ya kura mata yana kallonta, tayi murmushi tace wannan kallon fah, dariya yayi ya tashi ya kamo ta sannan ya xaunar da ita akan kujeran dake dakin, yace bana hanaki yin komai ba, tace mai nayi yanzu tare da xare ido, yace wa yace kije ki wanka da kanki? Tayi dariya mai sauti tare da fadin ai wannan ba aiki bane, yace to daka yau shima bana so kina yi, ni zan dinga miki, Ta kalleshe suka hada ido, tayi sauri tayi kasa da kanta tana dariya, nan ya tashi ya dauko ledan abincin ya bude sakwara ne da miyan egusi, yaji ganda da dry fish, ga wani kamshi dake tashi, dayan ledan kuma farfesun kayan ciki ne, kafin ya gama budewa harta dauki sakwaran Ta fara ci, dariya yayi tare da fadin babyna yasa bakya wasa da abinci itama dariyar tayi taci gaba daci, har Ta koshi sannan ta ajiye, yaje ya dibo mata ruwa a wani bowl ta wanke hannu, ta kalleshi tace yasu mama suma an kai musu? yace eh tace bari inje in duba su, yace a’a ki zauna ki huta anjima sai kije bata musa ba ta zauna nan ya xauna da ita yana ta bata kulawa har bacci ya dauketa, sannan ya fita. 

Salma sai wajan 4 ta tashi, alwala tayi, sannan tayi sallah, kai tsaye dakin baki tayi taga kofar a bude ta shiga, taga matar da yarta, suna zaune akan kujera sunyi wanka sun sa kayan data basu, da fara’a tace sannunku suka amsa da yauwa nan salma ta tambayi yarinyar miye sunanki mmnki taki fadamin yarinyar tayi dariya tace ai bata fada, tace sunana salamatu, salma tayi dariya tace lah sunan mu daya, yarinyar tace to yanzu xaki sa mamana ta fara jin kunyan ki, salma taci dariya, salma ta kalli mmn da tayi shuru tana musu dariya, tace mama a wani anguwa kuke? Nan tayi shuru, yarinyar tace bamu da gida duk inda muka samu anan muke kwana, salma tace kaman ya? Mmn tace ke ban San surutu, yarinyar tayi shuru salma tayi dan murmushi tare da fadin mm yanzu dai saiku xauna a nan idan ta gama warware sai ku tafi bata musa ba tace babu komai, jin muryan Mahmud yasa ta tashi ta fita dan taji security na mishi sannu da zuwa, ta fito tana mishi murmushi da sauri ya karaso wajanta yayi hugging dinta sannan sukai ciki, a falo suka xauna nan take fada mishi abunda ya faru, shuru yayi na wani lokaci kafin yace inaga mu basu kudi su wuce, salma tace a’a ina so in san ko su waye su, ina son ka taimaka musu, yace salma idan na basu kudi aiya isa, no need ki san kosu su waye, tace dear plz wlh suna ban tausayi kar ka hanani in san labarin su, plz yace owk Allah ya taimaka, fauxiya ta shigo falon babu sallama sai sakin tsakin da tayi tare da fadin mayya, kwadayi dai mabudin wahala, Mahmud cikin fushi yace ke wace irin mara tunani ce, tace eh bani dashi sai waccan yar iskan data dauko cikin wani tace naka ne,yace keee fauxiya kije na sakeki saki daya kuma ki jira takardan kotu akan shegenta min d’a, tace wlh ba…….. Kafin ta karasa magana suka ji muryan hjy binta tana fadin dakyau ya waiga cikin tsoro……. 

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button