KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 31 to 40

Mahmud a ranan salma tace ya kamata yaje office dan ya kwana biyu a gida, bai musa ba yace babu damuwa, yace baya son inya fita tace za tayi wani abu da kanta ta zauna kar baby dina ya samu matsala, tayi murmushi tace shikenan babu damuwa sai ka dawo, ya bata fake sannan ya fita,

Fauziya taje banki ta cire kudi, ta nufi wajan mlm yau ko biya ma mamanta ba tayi ba, ta wuce ita daya, bayan taje ta bashi kudin yace ta koma gida nan da sati daya cikin zai xube cikin murna ta wuce, ba tayi gida ba wajan mamanta tayi, ta sameta tana kallo, ganin fauziya din yasa ta Washe baki tace Tun daxu inata jiranki amma shuru, fauziya tace ai har naje ma daka can nake, tace kaji yar albarka, yanzu ya akayi tace yace nan da sati daya zai xube, hjy zaliha ta washe baki tace yauwa kinga inya xube kowa ya huta, ke naji ma har yanzu shuru ta tabe baki tare da fadin bari in wuce gida, ta fita. 

Salma bayan mahmud ya fita, tayi dariya tare da fadin bari inje in daura mishi abinci tunda naji sauki inna biye mishi babu abunda zan dinga yi, gwara inyi in sami lada, tayi kitchen ta daura abinci, fauziya ta dawo taji kamshi na tashi kai tsaye tayi kitchen din tace munafuka dama kece, salma tayi banza da ita nan ta matsa kusa da ita takai mata duka a ciki nan ta fadi tana wash Allah innalillahi wa inna’ilahira jiun, ganin haka yasa tabar kitchen din tana fadin kadan kika gani, 

Mahmud tunda ya fita yaji gaba daya hankalinshi bai kwanta ba, ya dawo gida Tun daka waje yake jin kauri da sauri ya shiga gidan, yaga hayaki a kitchen yana fitowa da sauri yayi kitchen din ya fara tari ya kashe gas din yaga salma a Kwance nan ya kuma rudewa ya dauketa yai waje da ita, driver ya shiga suka kama hanyar asibiti yana ta fadin yi sauri driver yana ta gudu, tazo zata tsallaka yayin dashi kuma ya kasa tsayar da motar ya bigeta, nan mahmud ya saki Salati, jini gaba daya jikinta, nan matar da suke tare ta saki ihu mahmud yazo yace ta shigo suje asibiti, dakyar ta yarda ta shiga sukai asibiti dukan su emergency akayi dasu, yayin da yarinyar ko numfashi ba tayi ita kuma salma gaba daya ta fita hayyacinta. 

Maryam Obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  70to75

Mahmud ya shiga cikin tashin hankali, har rama yayi na lokaci daya fuskan shi tayi fayau, hada kanshi yayi da bango yayin da zuciyarshi take bugawa, gefe daya kuma ga matar da suka bigema yarinya tana ta faman ihu sun kashe Mata y’a,yayin da driver kuma gaba daya komai nashi ya tsaya dan yana tsoran kar ace yarinyar ta rasu, gaba daya suna cikin tashin hankali, dukansu suna son suga Dr ya fito ya musu bayani,. 

Fauziya tunda ta bige salma tayi d’aki take a tsorace yanxu idan wani abu ya sameta fa? Tace ni na aikata mata hakan nasan Mahmud bazai barni ba, nan ta fito tayi kitchen din amma babu salma babu dalilinta, kai tsaye dakinta tayi shima dai bata ciki, nan ta kuma tsorata tayi waje, tana tambayan security salma ta fita ne? Suka ce eh oga ya dauketa kaman a sume take nasan dai asibiti Suka tafi, nan tayi gida da sauri tare da fadin na shiga uku, nan tayi d’aki ta dauko key din mota tama rasa ina zata sai yawo take a titi, daka karshe ta yanke bari taje gidan hjy binta, nan ta nufa bayan tayi parking ta fito tana kuka, nan hjy binta ta fara tambaya lafiya kuwa Fauziya mai ya faru? Nan ta fara shargo mata karya salma ce tana ta nemana da kokawa naki kulata ganin haka shine tazo zata janyo ni shine ta zame ta sume, ni yanxu ina tsoran ta farfado ta kullamin sheri wajan Mahmud, tace ni na tureta, nan hjy binta ta kumbura tare da fadin wato tana bakin cikin wannan cikin koh tana so ya xube dama naga take takenta bason cikin take ba wlh, nasan magani tayi tasha dan karta dauka yanzu Allah ya kamata ya bata shine take son ta zubar min da jika toh wlh idan cikin nan ya zube wlh saina sa an daure min ita harda iyayenta kaji yarinyar banza mara mutunci, tashi muje asibitin. 

Dr dai shuru har yanzu bai fito bah, Mahmud dai yana nan a tsaye tun dazu ya kasa zama, wani gefen kuma yana tunanin mai yasa salma taki Jin magana na nace kartayi komai amma taki ji, yanzu gashi taja ma kanta matsala wani hawaye ya xuba a idonshi ya furta a hankali salma ina sonki, I can’t live without you, mai yasa kika ki jin magana na why salma??? Jin an taba shi yasa ya waigo hjy binta ce cikin bacin rai amma ganin tilon dan nata na hawaye yasa gaba daya jikinta yayi sanyi, tasa hannu ta share mai tare da kamo shi ta zaunar dashi lokaci daya yasa kanshi a kafadanta yana kuka kaman karamin yaro, nan hjy binta ta tsorata, Fauziya kuma babu abunda zuciyarta keyi sai bugu, hjy binta tace Mahmud mai ya sami salma din? Tace har yanzu Dr bai fito bah mama ina tsoran kar in rasa salma ina sonta, hjy binta tace haba Mahmud kaji ance ma zata mutu ne? Ka daina wannan maganan kaji, yace mama wlh a cikin wani yanayi muka zo asibitin nan, ina cikin tashin hankali, nan taita bashi baki tare da mishi nasiha, ita kuma babu abunda take sai Allah yasa kar cikin ya zube domin tana bala’in son cikin, matar dake gefe itama ta zabga tagumi tana jiran taji lafiyar yar tata,

Wasa2 sai da Dr yayi kusan awa biyu kafin ya fito, gaba daya Suka tashi badda Fauziya da tsoro ya dameta, Mahmud yace Dr ya jikinta? Dr yace muje office nan duka Suka bishi harda driver, bayan Dr ya zauna ya kalli Mahmud yace gaskiya you are very lucky, matarka na abubuwa wanda basu dace damai ciki ba, sai dana fada maka karta dinga yin abu mai wuya amma Ka barta tana yi, hjy binta ta katse shi da fadin yanzu maiya sami cikin? Yace cikin na nan, sai dai kuyi mata addu’a ta haiyu lafiya, hjy binta tayi ajiyar zuciya tare da furta alhamdulillah, Fauziya jin haka taji kaman ta shake hjy binta dan takaici dan taga yanda take wani zakewa akan cikin, Mahmud yace Dr yarinyar nan fah? Hjy binta Tace wace yarinyar nan ya bata labari Dr yace eh munyi iya kokarinmu sai kuyi addu’a domin har yanzu bata farka ba, nan matar nan ta saki kuka tare da fadin nashiga uku sun kasheta, hjy binta Tace haba baiwar Allah ki daina fadin haka miye amfanin kukan addu’a xaki mata, ta kalli Dr Tace zamu iya shiga yace eh, nan sukai emergency din, salma tana kwance amma idonta biyu tana kallon sealing, yayinda yarinyar ita kuma ansa mata oxygen, saman kanta ansa plaster da kafanta na hagu, alaman ciwo taji a wajan, Mahmud wajan salma ya nufa, ya kira sunanta a hankali tare da rike mata hannu, hawaye ya zuba a idonta, yace ya jikin? Ta amsa cikin sanyin murya dasauki, nan ta hango Fauziya da hjy binta gabanta ya fadi, hjy binta ta matso tare da fadin kinci sa’a cikin bai xube ba da wlh sai kinje freezing keda iyayenki Mahmud yace haba mama bakya ganin halinda take ciki, tace yimin shuru, kana nan tana maidaka wawa baka San abunda kake ba, taso ta zubar da cikin ne Allah ya nuna mata iyakar ta, nan salma ta saki kuka, tace kaji makira koh, ai baki kuka ba sai kinyi kuskure kin zubar da cikin nan sannan zaki kuka, tayi tsaki ta fita Fauziya ma tabi bayanta, nan Mahmud ya zauna yana ta bata hakuri tare da fada mata wata rana sai labari, ta kara hakuri akan duk abunda mama zata mata, tayi dan murmurshi tare da fadin nasha fada maka, komai mama tamin babu komai mahaifiyata ce, ta isa tamin komai, yayi murmurshi yace nagode salma Allah ya saka miki da alkairi, nan ya tashi yaje kan yarinyar nan yana dubata yana fadama salma abunda ya faru lokaci daya yayi shuru tare da kara kurama fuskan yarinyar ido yana tuna inda ya Santa, salma dake kwance gaba daya idonta na kanshi tana mmkin irin kallon da yake ma yarinyar gashi yana mata magana yayi shuru, lokaci daya yayi murmushi, ya dago kai sai a sannan ya tuna salma na wajan kuma yaga tana kallon shi……. 

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button