KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 31 to 40

Mahmud yazo zai shiga d’akin salma suka hadu da fauziya tasha wannan kwallin nata, ta fara mai fari da ido, gaba daya ya rikice ya bita, duk da zuciyanshi nason ganin salma din amma ya kasa shiga ya rasa mai yasa, fauziya tabbas ta tsorata da dawowan salma, domin tunda suka dawo ta gansu ta window din d’akin ta, amma abu daya take jin dadi inta tuna cikin salma ya xube, tace yanzu inna bari ta haiyu ta sami namiji aina bani komai ya koma wajanta, tayi dan murmushi tace akan kudi zan iya komai wlh, . 

Har gari ya waye mahmud bai zo wajan salma ba, abun ya dameta sosai amma babu abunda take sai addu’a dan daran jiya batayi bacci ba, sallah take tayi, Sai wajan asuba ta samu tayi bacci, shima mahmud din yana son zuwa wajanta amma ya kasa ya rasa dalili, sun fito suna breakfast shida fauziya amma gaba daya hankalinshi na wajan kofar salma yana son yaga koh zata fito ya ganta, fauziya ta lura da hakan, tace lallai zan dauki mataki gaskiya kafin abu ya lalace, ta kalleshi tace ya kamata yau kaje gidan mama ka gaidata yace toh an gama bari in gama sai inje, hakan koh akayi yana fita, itama ta fita, gidan malaminta tayi babu kowa dan haka kai tsaye ta shiga, fuskanta a daure ta zauna yace lafiya kuwa? Tace ina lafiya abu yana so ya lallace, yace ina zuwa nan ya buga kasa, yace kai karya ne ya kuma bugawa, ya hargitsa tare da fadin ya zaku min haka wannan karya ne, ya hargitsa yakai sau biyar yana fadin karya ne, tace wai mai yake faruwa ne, yace cikin bai zube ba, tace what kar ka raina min wayau mana, kana nufin duk aikin da kayi baiyi ba, toh wlh da sake kullum kasa ina ta faman zuwa duk sati kana tabani da wannan kazamin jikin naka amma kace cikin bai zube ba, ya daka mata tsawa cikin murya mai karfi lokaci daya tayi shuru yace ke yarinya karki fadamin maganan banza wannan cikin ko mai zaki a kanshi bazai fita ba, in kika matsa zaki iya rasa rayuwarki, kuma daka yau karki kara zuwa nan inko kika sake zuwa saina sa aljanu sun illata min ke tunda baki da kunya baki San mutunci ba, duk rashin kunyan fauziya ta tsorata musamman yanda taga kwayar idonshi ya canza daka fari zuwa jaaa, yace fita kiban waje da sauri ta tashi tayi waje kirjinta na dukan uku3,

Mahmud bai dade da fita ba, ya dawo, domin babu abunda yake son ya gani kaman salma, dan ko gidan mama din bai jeba, yana dawowa kai tsaye d’akin salma yayi ya ganta a zaune tana kwalla, lokaci daya yaji jikinshi yayi sanyi, ya kira sunanta cikin sanyin murya, salma, tayi sauri ta waigo sukai ido biyu gaba daya yaji kaman an cire mai wani abu, ya nufeta tare da tsugunnawa a gabanta yana fadin salma nayi miki laifin da ban San da wani kalma Zan baki hakuri ba, dan Allah salma ki yafe min wlh ni kaina ban San abunda yake damuna ba, kwana biyu da suka wuce kullum na kasance cikin kasala, wanda bana iya aikata komai, dan Allah ki yafe min, tayi sauri ta toshe mai baki tare da fadin miye haka, dan Allah ka tashi daka wannan tsugunnan kana sani ina jin wani iri, yace salma bazan tashi ba har sai kin yafe min, tayi dan murmushi tare da fadin baka min komai ba inma kamin na yafe maka, nayi ma kaina alkawari bazan taba yin fushi dakai ba, yayi murmushi tare da tashi yayi hugging dinta, yace Zan iya magana da babyna ta d’aga mai gira alaman eh, yasa kunnenshi akan cikinta yana fadin baby hi, how are you, hope you are ok, talk to dady my baby say hi to dady, dariya salma ta saki, ya taso yana kallon ta cikin so da kauna ganin kallon da yake mata yasa ta rufe fuska yayi murmushi nan suka shiga farantawa juna rai, 

Fauziya tana fita, ta kira hjy zaliha tana kuka tana fada mata abun daya faru tace rabu da dan iskan, kina ina yanzu muje wajan wani malamin gari da yawa tace ki fito bakin titi zanzo in daukeki mu tafi, tace toh nan ta yayibi gyale ta fito, kai tsaye gidan wani mlm suka je, inda yake zaune a wani daji saida suka ajiye mota sukai tafiya mai nisa a kafa, bayan sun karasa babu abunda kake ji sai kukan tsintsaye fauziya tace nifa tsoro nake ji, hjy zaliha tace karki damu babu abunda xai faru, suna tsaye bokan ya bullo, fauziya ta rike hannun mmnta, ya saki dariya yace ya akayi, hjy zaliha zata fara magana yace dakata nasan maiya kawo ku, ya kwashe da dariya yace wannan cikin bazai fita ba,tace toh yanzu miye abun yi? Babu wani hanya? Ya kwashe da dariya yace hanya daya ne shine ki bar maganan wannan cikin, ki nuna kina so komai zai miki zan baki wani abu da zaki dinga murzawa komai kika tambaya zai baki, tace toh nan ya bata wani abu kaman gyad’a guda daya amma yana da dan girma suka wuce, ranan sunyi sunturi gidajan malamai amma ance cikin bazai fita ba sai gidan wani boka da suka je shine yace cikin zai fita amma aikin da xa’a mata akwai tsada tace babu damuwa ko nawa ne zan biya, nan yace zata bada 3 million, tace yanzu babu a hannuna amma gobe zan kawo, nan suka tashi suka wuce da nufin gobe zasu dawo.. Hmmm muje zuwa dan jin ko fauziya za tayi nasara. 

Maryam Obam ????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  65to70

Sai wajan 9 fauziya ta dawo gida, kai tsaye tayi dakinta bata ga mahmud a ciki ba, nan ta kirashi a waya bai dauka ba, tayi shuru tana dan nazari kar dai ace wannan dan iskan ya lallata komai, dana shiga uku, ta kuma doka mai kira yasa mata busy, tace na shiga uku wlh ya bata komai ni yake kashe ma waya, kai tsaye tayi dakin salma tana bugawa, mahmud yazo ya bude cikin bacin rai yace wai ke mahaukaciyar inace? Tace dole ka fadi haka, dama kana nan shine na kiraka kaki daukan waya ko, toh wlh ni nafi karfin wulakanci sai dai kama waccan mara zuciyar, yace keee kisan abunda zaki dinga fadamin inba haka ba wlh ranki zai baci, tace ya baci din mana babu abunda ka isa kamin wlh, yace haka kika fada koh? Tace eh yace ok kije gidanku saina neme ki, ta saki dariya wlh babu inda zani baka isa ba wlh, ai gidan nan na shigo kenan sai dai kai ka fita ka barshi wlh,kuma ina nan kaida kanka zaka kawo kanka yayi murmushi tare da tsaki ya koma dakin salma yasa key ya barta tana ta hauka, salma gaba daya ta tsorata dan bata san tashin hankali ko kadan, ya kalleta yayi murmushi tare da fadin dear ya naga kin canza? Tace dan Allah ka tafi wajenta wlh ban san rigima plx, ya daure fuska, ganin haka yasa tace kayi hakuri ban fadi haka dan in bata maka rai ba, yace toh karki karamin maganan inje wajanta, tace insha Allah babyna, salma gaba daya ta tsorata da kalaman fauziya, tace dole in kara dagewa da addu’a, 

Fauziya tana yin d’aki ta kira hjy binta ta fada mata abunda mahmud ya mata da wanda yayi da wanda baiyi ba duk ta fada mata, dama tana fushi dashi yaki zuwa wajanta wajan sati daya kenan, tace kiyi hakuri gobe zanzo gidan da safe tace toh sai kinzo tana kuka,ranan fauziya bacci gagaranta yayi ta kosa gobe yayi taje wajan mlm a xubar da cikin salma. 

Hjy binta karfe bakwai ta dira gidan mahmud, lokacin basu tashi daka bacci bama dan sai da suka kai asuba suna sallah kafin suka kwanta, fauziya ta fito ta rungumeta tana kuka, tace yi shuru ina mahmud din? Tace yana dakinta basu fito ba, ta haura sama ta fara buga dakin tana Kiran sunan shi, yayi sauri ya farka, yace salma ta canza kaya da sauri dan rigan bacci ne a jikinta tayi sauri tasa jallabiya, sannan ya bude kofar kai tsaye dakin ta shiga tana sakar mishi harara, tace sannu shanyayye, ta kalli salma tace kin shanye min d’a baya ganin kowa sai ke, kin raba ni dashi kwata2 baya zuwa wajena yanzu harta office Kin hanashi zuwa toh wlh baki isa ba, daraja daya kika ci shine kina dauke da jikana a jikin ki da yau wlh baki kwana a gidan nan ba, mahmud yace dan Allah mama kiyi hakuri wlh ba laifin salm…… Dallah yimin shuru karka cemin komai ai dama ita bata laifi, kai da ita Kuna ta wulakanta min y’a toh wlh ka fita daka ido na, gwara ka dawo cikin hayyacinka wlh, tun kafin inyi mugun saba maka, kazo ka makale mata kun bar min y’a ko oho, duk ta rame sai zalintan ta kake wlh mahmud Zan saba maka indai kaci gaba da haka, ta fita fuuuu yabi bayanta yana bata hakuri kun San tsakanin d’a da uwa, tace babu komai fauziya tana nan ta labe tana jin abunda suke fada, tace ya jikin salma din? Yaji dadin tambayan da tayi cikin jin dadi yace da sauki, tace kar dai ka bari ta dinga abubuwa Mai wahala tunda baiyi kwari ba, yace toh mama na gode, ta wuce, Fauziya dake labe tace kambu wlh da sake wato itama tana son cikin dukanku zanyi maganin ku wlh, hjy binta bata dade da fita ba itama fauziya ta fita, 

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button