RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

     Lokacin ne Inna Haule tashigo ɗakin tana faɗin “a’ahh Mijina ashe kana nan ne?”

“Eh Inna, na rako RAUDHA ganin Baby ne”.

“To madalla, ai ga ta nan kuwa ta kafa masa idanu amma taƙi ta ɗauke sa”. cewar Inna cike da fara’an ta

Suhaib dariya yayi yana kallon RAUDHAN, kafin yace, “Baby baki gaishe da Inna ba”.

Sai alokacin ma RAUDHA ta kalle ta tun shigowar ta, gaishe ta tayi kamar yanda Suhaib yace mata

Inna Haule kuma ta amsa mata cikin fara’a, itama tana tambayan ta “Ya jikin ta?”

Wannan karon ma Suhaib ne ya amsa mata, don yasan RAUDHA ba sake magana zata yi ba

Inna Haule zama tayi suka hau hira da Suhaib ɗin, don dama sun saba sosai, har aka kira sallan isha’i suna tare kafin ya tashi yafice, itama RAUDHA bin bayan sa tayi takoma ɗakin ta.

      Inna Haule miƙe wa tayi taje ta sako ruwan wankan, kafin tazo ta tashi Farida don tayi mata wankan.

     Bayan tayi mata wankan jegon sannan tayi wa jaririn, sai ta ɗauro alwala tafito, lokacin har Suhaib ya sake shigowa ɗakin ya fice

Babu jimawa Kuku yashigo musu da abinci da kunun me jego.

       RAUDHA kuwa tunda tashige ɗaki kwanciyar ta tayi bayan ta saka ƙwayoyin ta cikin baki tana tsotso, bata jima ba barci ya ɗauke ta

Koda Suhaib yashigo duba ta yaga tayi barci, be tashe ta ba ya gyara mata Bargon da tarufa tare da kashe mata fitilan ɗakin yafice.

????????????????????????????????????

       Ranan suna jaririn ya ci sunan Daddy Mustapha, zasu riƙa kiran sa da Haneep kamar yanda RAUDHA ta saka masa

Ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun hallara bikin sunan, gidan Suhaib ya cika maƙil don shi kansa yayi mamaki da mutanen da suka zo taya sa murnan sunan, har da wasu daga cikin dangin mahaifiyar su da ke Bayelsa sai da suka zo, dayake ita ɗin ƴar can ce, su ma wasu daga cikin dangin Daddy dake aure a gari maban-banta duk sun samu zuwa, duk da su ɗin ba dangin sa na kusa bane, but Daddy mutum ne me kyautatawa ko kaɗan ba ya manta wa dasu wajen taimako shiyasa har yanzu suke zumunci, duk da ƴaƴan sa ba zuwa suke yi ba, amma shi yana zuwa wajen su sosai don jin matsalolin su. Itama Farida ƴar dangi ce, don haka dangin ta masu yawa sun hallara ranan sunan, ga matan abokan Suhaib ɗin duk sun zo, hakan yasa jama’a suka yi yawa, an yi taron girma da arziƙi kowa ya tafi yana yaba wa.

      Ita kanta RAUDHA da ba son mutane tacika yi ba, sai da tashiga cikin su aka yi suna da ita, daga ƙarshe ne ma da kanta ya soma mata ciwo tashige ɗaki ta’afa ƙwayoyin ta sai barci, bata sake sanin me ake yi ba sai dare da ta tashi, lokacin duk an gama watse wa, sai wasu tsirarun mutane ƴan uwan Farida da ƴan Bayelsa suka rage.

      Washe gari su ma duk suka watse aka bar Inna Haule kaɗai dake mata wankan jego. Ita taci gaba da kula da ita har sanda suka yi arba’in, kafin ta tattara ta tafi cike da alhrerai kala-kala da Suhaib ya haɗa ta dasu.

      Zuwa lokacin itama RAUDHA tuni ta koma school ɗin ta, sun sake ɗinke wa da su Rash sai abun da yayi gaba yanzu, sai dai yanzu babu Zen yayi tafiya na sati biyu zuwa asalin tushen su Kwara state, an yi musu mutuwa shine suka tafi gaba ɗaya ahalin su.

        Yanzu RAUDHA, Rash da kuma Man suna tare ko ina tare suke zuwa, babu abinda suka fasa na game da rayuwan su, sai ma sake taɓarɓare wa da suke yi, ta kai ta kawo yanzu RAUDHA wani lokacin ba ta kwana agida, duk inda suka ce zasu tafi bin su take yi.

     Suhaib ya tashi hankalin sa matuƙa da irin wannan sabbin halayen da RAUDHA ta tsiro da su, yana gudun abinda zai faru kamar yanda ya rasa ta kwanakin baya, sosai ya zaunar da ita yayi mata faɗa, but ko sauraron sa bata yi ba, a ranan ma sai da ta kwana biyu bata dawo gidan ba, dole sai shi Suhaib ɗin ya neme ta ya bata haƙuri, gaba ɗaya yanzu ya gama rame wa a tsaye sabida zullumi da tashin hankalin da yake ciki, ga kuma abun tashin hankalin da ya sake riskan su, ciwon Haneep kullum gaba yake yi, yanzu wani tsira ne ya fito masa a ciki, koda yaushe ƙara girma tsiran yake yi, wai ma don suna zuwa asibiti ana magani, dole ya yanke shawaran fita kasar waje don aduba lafiyan sa, daga nan sai yaje inda Daddy yake don sanin halin da yake ciki, tunda har yanzu be sake kiran su ba, duk wasu abokan sa da suke hulɗa sai da Suhaib yabi ya tambaye su ko sun san wani abu agame da Daddyn nasu, but babu wani bayani.

          ????????????

       Yau dayake Saturday ne RAUDHA basu da school, shiyasa take ta sharan barcin ta, jiya a club suka kwana sai da asuba ta dawo, that’s why tunda ta shimfiɗe akan gadon ta take barci tamkar kasa, har zuwa ƙarfe biyu taƙi tashi

Wayan ta dake faman tsiwa tana neman agaji, ita ta tashe ta daga nannauyan barcin da take faman yi, ƙiri-ƙiri ta kasa buɗe idanun ta sabida kumburan da suka yi tsaban barci, haka tayi ta kokawa wajen buɗe idanun suna lumshe wa, daƙyar ta iya buɗe su da suka gama ƙanƙance wa suka yi jazur

Wayan dake kan drower ta jawo, lokacin Three missed Call aka yi mata, but me kiran be gaji ba ya sake kiran na huɗun, tsaki taja wanda ko kaɗan be fita ba, ta sake ware idanu kan wayan don ganin nataccen dake kiran ta

Ai tuni ta wartsake sabida ganin sunan Daddyn ta na yawo a screan ɗin wayan, wani ƙara ta ƙwalla da dusashshiyar muryan ta, jikin ta na rawa ta amsa kiran tana kiran sunan Daddy cikin ihu

Lokacin Suhaib ya turo ƙofan ya shigo, jin RAUDHA na ihu tana faman kiran sunan Daddy, ai tuni ya iso wajen ta shima ya zauna yana son ƙwace wayan da faɗin

“Da gaske kike yi Baby? Daddy ne ya Kira ki?”

Cikin tsagwaron murna ta ciro wayan daga kunnen ta tana nuna masa tana faɗin “eh shine Yaya, ka gani ko wlh shine Daddy ne..”

“To saka a hans free Baby”.

“To”. Ta amsa mishi da sauri tana saka wa

A lokacin ne muryan Daddyn ya bugi kunnen su yana faɗin “Hello kuna ji na?”

“Daddyyyy..” RAUDHA ta sake faɗa tana me fashe wa da kukan jin muryan Daddyn ta

Shima Suhaib ɗin sunan Daddyn yakira ahankali

Daga can Daddy ya amsa musu cikin tsananin kewar yaran nasa, kana yaci gaba da faɗin “Auta na menene kuma na kuka? Ko kin fi son na kashe wayan ne ba kya son jin muryana?”.

Cikin kukan take girgiza kanta tana faɗin “A’a Daddy na dena kukan, ina so Daddy.. Ina so.. nayi kewar ka ne sosai da sosai Daddy, yaushe zaka dawo I miss You so Much”.

Sai tasake fashe wa da kuka tana faɗa wa jikin Suhaib, shine ya amshi wayan daga hannun ta ya riƙe

Daga can Daddy yace, “Very soon zan dawo gare ku Baby, ki dena kuka kin ji?”

Sai kuma yakira sunan Suhaib ɗin yana tambayan sa lafiyan sa da matar sa

“Daddy lafiya lau kowa lafiya, har Wifey ta sauka an yi maka takwara”.

Daga cikin wayan sosai zaka gane Daddy yayi murna da maganar da yaji, nan yayi ta nuna farin cikin shi yana saka musu albarka gaba ɗaya

RAUDHA da take faman share hawaye tace, “to Daddy yaushe zaka dawo?”

Numfashi Daddy yaja kafin yace, “Baby bansan ranan dawowa na ba”.

“Why Daddy?”. Tafaɗa kamar zata yi kuka

“Ƙaddara Sweetheart, ƙaddara ce ta faɗa min, na faɗa muku kaya na sun sami matsala, bansan ya aka yi ba aka samu Cocaine cikin kayan mu, to har yanzu ana kan bincike ne, dole zamu zauna har sanda za’a gama, idan kuma basu gano waɗanda suka saka ba, zasu riƙe mu ne na shekara ɗaya a Jeil, wannan shine dokan su”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button