RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

Hannun ta ya riƙe cikin farin cikin jin tayi magana, dasauri ya maida ita ta zauna, yana faɗin “yunwa ko Baby? To bari in kawo miki abinci, ki zauna kar ki tashi ina zuwa”.

Ya saki hannun ta ya juya da sauri.

      Yana fita itama ta tashi tabiyo bayan sa, be san tana bin sa ba har sanda ya dangana ga kichen ɗin, dasauri ya juyo yana kallon ta

“Baby biyo NI kika yi kuma?”

Gyaɗa masa kai kawai tayi tana ƙarisowa kusa dashi.

     Abincin ya ɗiba mata cikin coolar sannan ya riƙo hannun ta suka fito daga kichen ɗin, a Parlour suka zauna yana bata a baki, ita kuma tana amsa batare da tace mishi uffan ba duk da kuwa maganan da yake mata.

      Itama Farida fitowan ta kenan daga ɗaki ta gan su a parlour’n, tana riƙe da Haneep a hannun ta ta iso wajen su fuskar ta cike da annuri, zama tayi kan two sittern dake Kallon wanda suka zauna, idanun ta akan su tace, “Ƙanwata duk kin ɗaga mana hankali da rashin cin abincin ki, don Allah idan fushi kike yi damu ki dena wasa da cikin ki irin haka kinji? Baki ga yanda muka tashi hankalin mu ba akan rashin mana magana da kika yi”.

Ɗago kai kawai RAUDHA tayi tazuba ma Faridan idanu, batare da tace komi ba dai take amsar abincin da Suhaib ke faman ba ta, yana yi yana shafa kanta tamkar wata ƙwai, ji yake yi kamar ya ɗauke ta ya maida ta ciki sabida ƙaunar ta

Farida dai bata damu da rashin mata magana ba, tunda ta saba da halin ta, girgiza Haneep take faman yi sabida kar ya tashi daga barcin da yake yi.

      Be dena bata abincin ba har sai da ta ture hannun sa, hakan yasa ya janye yana ɗaukan ruwa a Cup ya miƙa mata

Amsa tayi tasha sannan ta ba shi ya’ajiye

Kallon ta kawai yake yi yana zuba mata murmushi, sai kuma ya saka hannu yana gyara mata gashin ta dake zube a gadon bayan ta babu Ribom, tattare mata ya hau yi yana ƙoƙarin ɗaure mata shi

Ita dai tana jin sa batace komi ba, ba wai don ba ta da abun cewa ba, a’a, sai don rashin daɗin da jikin ta ke mata, kamar an zare mata laka haka take ji, ga kanta da be gajiya da mata ciwo ko yaushe.

      Tashi Suhaib yayi ya riƙo mata hannu yana faɗin “tashi muje ki raka Ni Baby”.

Tashi tayi babu musu

Farida ta kalle sa tana cewa, “Husband sai ina kuma?”

Keey ɗin motan sa dake ajiye akan Centre table ya ɗauka yana bata amsa da faɗin “super market zan kai Baby”.

Adawo lafiya tayi musu

Fice wa suka yi ita kuma ta raka su da ido, ajiyan zuciya ta sauke aranta tana tunani daban-daban.

 

              ????????????

     Babu inda suka zarce sai super market, kayan ciye-ciye duk ya jido mata cikin leda, daga nan suka yo gida

Suna shigowa RAUDHA tanufi sama da kayan ta

Shi kuma Suhaib zama yayi akan sofa yana zaro wayan sa dake faman Ring, idanun sa ya kai saman wayan, sai kawai ya saki murmushi idanun sa a waje

Be ɓata time ba ya amsa kiran yana kara wa a kunne

“Wlh Ni nayi fushi ℝ????????, baka san da tuna wa dani ba sai yanzu”. Suhaib ya faɗa hakan har yanzu da kyakkyawar murmushin sa shimfiɗe a face ɗin sa

Daga can wata dakakkiyar murya me tsananin daɗi da sanyi tasoma magana, shima daga ji mamallakin muryan yana a cikin nishaɗi ne

“Afwan ranka ya daɗe tuba nake, kaina bisa wuya Dude”.

Suhaib yace, “Ni dai nayi fushi da kai, kuma ban san wa zai shirya mu ba, nayi ta neman Numban ka but a kashe koda yaushe”.

Murmushi me sauti wanda aka kira da Ray ya saki, kana kuma yace, “Plz Dude I’m so sorry, wlh bansan da bakin da zan yi maka bayani ba, laifi na shine aiki ya mantar dani na bar waya ta a can Bayelsa, kuma na taho nan Nigeria da ninyan in zo har gida but aiki ya riƙe Ni, sai da na sauya waya kuma na tuna ban riƙe sabon Numban ka ba, har ta na Daddy ma ba na samu wlh, yanzu haka na koma gida ne na samu na kira ka”.

Suhaib dariya yayi cike da farin cikin jin Abokin nasa, tare da tsantsan ƙaunar junan su yace, “babu komi Dude na amsa tuban ka, and sai dai ka kiyaye gaba don idan ka sake irin wannan babban laifin tabbas zamu samu matsala”.

Gaba ɗayan su suka yi dariya wannan karon, sai Suhaib yayi saurin cewa, “wai ma tsaya, kar inyi saurin yafe maka, I tot kana Kaduna ne, Right?”

“Yeah Ina Kaduna wlh, wajen Six months kenan yanzu nayi”.

“But I know baka taɓa nema na ba acan?”

“Sorry Dude aiki ne..”

“Eh na sani aiki ne zaka ce dama”. Suhaib ya katse sa da faɗan hakan

Sai kuma suka yi dariya gaba ɗaya kafin su soma gaisa wa cike da kewan junan su, duk kan su farin ciki yalwace a fuskokin su, kai da gani kasan akwai soyayya da shaƙuwa sosai a tsakanin su

Suhaib ya tambayi iyalan gida gaba ɗaya

Ya ba shi amsa da “Alhamadulillah kowa lafiya” sannan shima ya tambayi lafiyan matar shi da ƙanwar shi RAUDHA

Murmushi Suhaib ya saki yace, “I know yanzu Baby ta manta da kai, ko kai ma nasan baza ka gane ta ba yanzu ai”.

Murmushi shima yayi yace, “gaskiya ne, to shekaru sun ja, ina tunanin ma rabo na da ita 14years Ago fa, sa’ilin tana 5years, uhmm yanzu nasan ta girma sosai, ta zama ƴammata”.

Suhaib yace, “really! gashi yanzu har ka zama Daddy yanzu ma”.

“Dude da gaske?”

Murmushi Suhaib ya saki yana ƙara bashi tabbaci, kafin ya faɗa masa abun da aka samu

Sosai ya nuna farin cikin sa, cike da ɗoki yace, “kace zan zo a Sa’a kenan, domin zuwa gobe insha Allahu uwar haka ina nan Abuja, an dawo damu nan zamu yi 3years, so har na ba da cigiyan gida anan, domin ba zan zauna a Barrack ba”.

Shima Suhaib murna ya hau yi, cike da tsantsan farin ciki yace, “ai gidana kawai zaka zo, taya ma zaka zauna a wani waje bayan kana dani, No No hakan ma bazai taɓa yiwu wa ba, ai kawai anan zaka zauna”.

Dariya shi dai yayi, don daman ya san halin abokin nasa, shiyasa be wani ja zancen ba suka ci gaba da hiran su, daga ƙarshe suka yi sallama cike da farin cikin gobe zasu ga juna, tsawon shekaru uku kenan rabon da su ga juna ido da ido, sai a waya, a wayan ma yanzu kusan 7months

Koda aka yi auren Suhaib be halarci bikin ba, lokacin an tura su Jejin sambisa don kawo ƙarshen ƴan boko haram, a time ɗin kusan shekaru biyu suka yi acan suna karan batta, daga ƙarshe ma an yi tunanin sun mutu don tuni an rasa inda suke, an duba su ko ina ba’a same su ba saboda a lokacin an rigada an kashe mutanen su gaba ɗaya, sai su iya goma da suka sha, a wani ƙauye suka zauna tsawon shekara ɗaya da watanni suna a mawuyacin hali, domin duk kan su sun sha harbe-harbe babu kyan gani, sai da aka yi jinyan su har suka gama warke wa, kafin su samu su dawo gida daƙyar, don a hanya ma sai da suka sake cin karo da ƴan boko haram, gashi time ɗin basu da makamen aiki, daƙyar suka sha aka kashe musu mutum uku.

Sai dai sun san juna sosai a waya shi da Farida, don suna yawan gaisa wa akai-akai, har a hoto ma ta san shi tunda tana gani a wayan Suhaib.

      Suhaib ɗin na sauke wayan a kunnen sa, Farida tafito daga ɗakin ta, zama tayi tana tambayan sa “shi da wa yake waya yake ta faman fara’a?”

Lokacin itama RAUDHA ta sauko daga sama, ta ƙariso wajen ta zauna gefen Yayan nata, tana jin duk amsan da Suhaib yake ba wa Farida but bata saka musu baki ba, tunda ita be shafe ta sai tasan ko wanene ba a ganin ta.

       Sosai Farida tayi farin ciki itama da zuwan Ray ɗin, nan suka soma shawaran ɗakin da za’a gyara masa zuwa goben, Suhaib yace, “a gyara masa sama kusa dana RAUDHA, nan zai fi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button