RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

Dasauri Basiru yazuƙuna agaban ta yariƙo hannun ta yana cewa “ke ke ke buɗe idon ki mana, mafarki kike yi ne? Halan Ni kika gani ƴar kyakykyawa?”

Ahankali RAUDHAN tabuɗe idanun ta tana tsai dasu kan Basiru dake gaban ta riƙe da hannun ta yana washe mata baki, lumshe idanunta tayi tasake buɗe wa akansa, kamar an tsikare ta kuma tayi zumbur tatashi zaune tana wurwurga idanu cikin ɗakin cike da tsananin tsoro

Bata kai ga tantance inda take ba Basiru yajawo ta jikin sa yana faɗin “sannu kyakykyawa kin tashi daga barcin ko?”

Sai kuma yakalli Lantana dake tsaye tana kallon ikon Allah bata sake cewa komi ba

“Da Allah ki fita kin tsaya min akai, ko so kike yi kiga abinda zan mata?”

“Basiru”. Takira sunan sa cike da rawan baki, domin hankalin ta a yanzu ya tashi sosai musamman da taga Basirun dagaske yake yi don tasan halin sa

RAUDHA dake faman ƙwace jikin ta da yatattakura ya ƙwaƙume ta ƙam yana son kai hannu jikin ta, wani irin ihu taƙwalla tana ture sa, ihu kawai take yi babu ji babu gani tana faman kai masa duka, tsoro ne fal aranta sabida ganin ta a inda bata taɓa tsintan kanta ba

“Ke wlh zan ci uwar ki idan baki tsaya ba, uwar me zan miki? Ina ce zan cire miki rigan ne kisha iska naga kina zufa”.

Ganin ya ɗaga mata riga zai cire mata tariƙe da ƙarfi tana kwantsama ihu me matuƙar firgitar wa

Ita kanta Lantana roƙon sa take yi yasakar musu ƴa amma be ma san tana yi ba

Babu zato babu tsammani sai ga Basiru yayi sama an buga sa da bango, sai gashi can gefe yashe yana ƙwalla ƙaran azaba dafe da ƙeyan sa, wani irin ashar yasaki yana kallon Lantana dake tsaye itama tana kallon sa cike da tsananin mamaki, ko kaɗan bata ga sanda yaje wajen ba sai ganin sa da tayi

RAUDHA tuni ta sume babu ko numfashi a tattare da ita

Cikin azaban zafin da yaziyarce sa yace, “kuttt.. sabida wannan shegiyar yarinyan ce zaki jefo Ni nan Lantana?”

Waro idanu Lantana tayi tace, “da wani ƙarfin zan iya jefa ka nan Basiru? Wlh Ni ban ma san sanda kazo wajen ba sai ganin ka da nayi”.

Shiru yayi yana maida idanun sa kan RAUDHA, mamaki ne fal aransa don shima yasan Lantana bata da ƙarfin da zata iya mishi irin wannan jifan, ko mahaifin sa da yake da ƙarfi bazai iya masa wannan ba bare ita

“To wanene ya jefo Ni nan ɗin?” Yafaɗa afili

Kiran da Malam Umaru yake kwaɗa wa Lantana yasaka tafita dasauri tana amsa wa

A bakin ƙofa suka yi kicibir

“Yauwa Malam gwara da Allah yakawo ka, wlh Basiru ne zai yi wa ƴar mutane ta’asa, mun shiga uku Malam idan asirin mu ya tonu”. Sai tafashe da kuka

Cikin tashin hankali Malam Umaru yatambaye ta “ina Basirun?”

“Yana ciki”.

Wuce ta yayi ya shiga ɗakin tana take masa baya

Basirun na nan a inda yake, sai muzurai yake yi jin muryan Baban sa

Kallo ɗaya Malam Umaru yayi masa yanufi wajen RAUDHA, dasauri yasaka hannu yaɗauke ta yafito da ita zuwa ɗakin su, ajiye ta yayi ya saka Lantana ta ɗibo masa ruwa, amsa yayi bayan ta kawo ya shafa mata a fuska, bata farfaɗo ba sai da ya sake shafa mata wajen sau uku kafin taja numfashi tabuɗe idanun ta da suka shige ciki sukai matuƙar ja, abun zai baka mamaki idan ka kalli idanun RAUDHA

Su kansu Malam da Lantana sai da suka tsorata ganin yanda idanun nata suka sauya kala, har wani kore-kore suke yi sabida tsaban ja

Hankalin su be tashi ba sai da tasaka musu kuka me ban tausayi, wani irin kuka take yi tamkar ta haukace, gaba ɗaya ta firgice musu da kukan nata sun rasa yanda zasu yi da ita, gashi taƙi yin magana duk da kuwa tana son yin maganan, sai dai da zaran ta buɗe baki sai ta kasa sarrafa abinda zata ce illa kuka kaɗai da take iya yi

Daƙyar Malam Umaru ya dage da yin mata addu’a har kukan nata ya lafa, sai kuma ta firgice musu akan dole sai sun kai ta gida

Malam Umaru yace, “baiwar Allah ki nutsu ki kwantar da hankalin ki sai ki faɗa mana inda kike mu maida ke kinji?”

Gyaɗa masa kai tayi tana jan majina, cikin dashashshiyar muryan ta da yaƙara shigewa sosai don daƙyar ake iya jin me take cewa, tafaɗa masa inda take a Asokoro

Dayake Malam Umaru yana shiga birni sosai, kuma yana jin sunan anguwan duk da be taɓa zuwa ba, but idan ya tambaya ai za’a iya kai sa tunda ba ɓoyayyen wuri bane, don haka yasaka RAUDHA tatashi ya kai ta

Abin mamaki ta kasa tafiya domin ƙafar ta ɗaya ya markwaɗe tamkar na kuturwa sai zafi yake mata, kuka tasaka tana komawa tazauna

Cike da tausayi Lantana tace, “Malam yarinyan nan fa baza ta iya tafiya ba, kar dai wani abun ne yasame ta? aje a ɗauko me gyara ya duba ta”.

RAUDHA dake kuka tasake ɓarke musu da kuka “wai sai dai su kai ta gidan su”.

Abun har mamaki yake basu, yarinya sai kace ba mutum ba, ta ishe su da kuka sai kace sun sato ta, su kansu sun san ba ƙaramar taɓararriya bace ita ɗin, tunda gashi duk ta hana su kwanciyar hankali

Sai da Malam Umaru yasake rarrashin ta akan tazauna zai je yasamo me mota sai su tafi, hakan kuwa yafaru be jima ba yadawo da me keke napep, shi ya ɗauke ta ya kai ta har waje cikin keke napep ɗin tunda baza ta iya tafiya ba, sannan suka tafi.

           ????????????

     Sanda suka isa ƙofar gidan Suhaib, wani daɗi ne sosai ya kama RAUDHA, sai dai rashin tafiyar ta ya saka dole sai da tajira Malam Umaru ya sake ɗaukar ta, dayake RAUDHA bata da nauyin jiki ko kaɗan kasancewar ta ba me yawan cin abinci ba, that’s why Malam Umaru idan ya ɗauke ta tamkar ya ɗauko ƴar baby

Itace me buga Gate ɗin gidan, sai dai shiru ba’a zo an buɗe ba

Hakan yasa Malam Umaru yaduƙa yaɗauko dutse yayi amfani dashi wajen buga Gate ɗin

Babu jimawa kuwa me gadin yafito a fusace don ganin me buga musu ƙofa haka, tozali da RAUDHA da yayi a hannun Malam Umaru sai yayi saurin wangale musu ƙaramin Door ɗin da yafito ta ciki yana ma RAUDHA sannu, duk da kuwa mamaki ne fal aransa da al’ajabin ganin ta hannun wannan dattijon

Me gadin biyo su yayi yana nuna wa Malam Umaru inda zai bi, sai kace an saka sa

RAUDHA na jin sa don haka bata yi magana ba ma.

     Suhaib na zaune shi kaɗai a parlour’n lokacin da suka shigo, dasauri ya ɗago kansa idanun sa da suka gama faɗa wa suka sauka kan RAUDHA

Kafin ma yayi magana ta kwaɗa masa kira

Ai tuni yayi zumbur ɗin tashi ya nufo su da mahaukacin sauri, jikin sa na rawa yasaka hannu ya amshe ta yana kiran sunan ta

Ita kuwa kuka ta saka masa tana ƙamƙame sa sosai.

        Hayaniyan su ne yafito da Farida, ganin RAUDHA ba ƙaramin saka ta farin ciki yayi ba, ai tuni itama ta nufo su tana nuna murnan ta

Tsawon mintuna goma Suhaib na rungume da RAUDHA a jikin sa yaƙi sauke ta, faɗan tsantsan farin cikin ma da yake ciki ɓata lokaci ne, domin har da hawayen sa sabida tsaban murna.

     Malam Umaru dai na gefe ya saki baki yana kallon abun mamaki

Sai Farida ne ma da takula dashi tayi masa maganar ya shigo ya zauna

Sai da yazauna kafin shima Suhaib yataho RAUDHA na jikin sa ya zauna

Ganin RAUDHAN ta ƙi dena kuka sai ya soma rarrashin ta, yana share mata hawaye da hannayen sa

“Kinga yi shiru my dear, ai gashi kin dawo ko? Babu abinda zai sake raba mu insha Allahu, yi shiru ki nutsu ki faɗa min waɗanda suke da hannu wajen ɗauke ki, nayi miki alƙawari sai na ɗau babban mataki akan su”.

Sake sakin kuka RAUDHA tayi tana ƙwaƙume shi tamkar zata koma Cikin sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button