RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

[2/22, 3:35 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON TWENTY ONE*

_______???? Direct wani gida suka nufa me kamar kango amma da akwai Gate a gidan, suna shigar da motan suka fito da ita, su uku ne mazan yayinda ɗaya ne yaɗauke ta yasaɓa ta a kafaɗa suka nufi cikin gidan da ko ƙofofi babu sai window

Kamar mintuna biyar da shigan su sai gidan yasoma amsawa da wani irin kuka me ban tsoro haɗe da wani irin gurnani tamkar za’a fasa gidan, kukan sosai yake ƙaruwa sai kuma yahaɗe na mutane da yawa wanda baza ka iya gane na aljanu bane ko na mutane, zuwa can kuma sai kukan yalafa sai ga RAUDHA ta fito tana layi gashin kanta duk ya barbaje ya rufe mata fuska, duk da dare ne but bazai hana ka hango yanda idanuwan ta ke wani irin walƙiya ba tamkar yanda na mage yake yi idan tafito da dare, tafiya kawai take yi har tafice cikin gidan tadoshi cikin daji, duk da dama gidan a wajen gari yake

Sai da tayi tafiya me nisa kafin tafaɗi ƙasa yashe babu alamun numfashi a tattare da ita.

         ????????????????????????????

      Washe gari har Suhaib yashirya zuwa Office yana jiran dawowar RAUDHA amma babu ita, duk da yasan bata kai wa har safiya idan tafita but yayi tunanin ko tana can ɗin ne inda tasaba zuwa, jin shiru bata dawo ba sai yatafi Office

Koda yadawo Farida ta tabbatar masa bata dawo gidan ba sai hankalin sa yayi mugun tashi, wayanta yasoma kira duk da kiran ya shiga but babu answer, sai da yayi Three missed calls kafin Rash taɗaga Kiran, tunda dama a motan Zen RAUDHA tabar jakan ta, su ma sun shiga tashin hankali musamman da suka neme ta suka rasa, daga baya kuma sai suka yi tunanin ta wuce gida ne duk da sun ji haushi sosai Zen da Maan tunda sun yi tanadin ranan sosai akanta, amma tatafi tabar su

Abinda yasoma fita a bakin Suhaib sanda Rash taɗau wayan shine “Baby Ina kika je har yanzu baki dawo gida ba kin ɗaga min hankali sosai?”.

Jin hakan sai Rash ta tabbatar akwai matsala, itama cikin tashin hankali da yanuna a muryan ta tace, “Ba RAUDHA bace ƙawarta ce, ta bar jakarta ne a wajena kuma naga kana kira”.

Suhaib dake zaune be san sanda yayi zumbur yamiƙe ba

“Whattt… Ki kace mene? Ita ina taje ne da tabar wayan a hannun ki?”.

Cikin tsoro Rash tabashi amsa da yanda aka yi su ma suka neme ta suka rasa

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Abinda Suhaib yafaɗa kenan yana me sakin wayan a ƙasa

Lokaci ɗaya zufa ya tsatstsafo masa a saman goshi, ga wani irin jiri da yamamaye sa nan take sabida tsananin tashin hankalin da yaziyarce sa

Farida dake zaune da ciki a gaba tana tambayan sa “meke faruwa?” Be ma san tana yi ba

Sai da yayi good 5 minutes a gushewar tunani kafin yadawo dai-dai, lokacin kuwa tuni hawaye sun ciko masa idanu yakalli Farida da tamiƙe tsaye itama hankalin nata a tashe, cikin raunin murya yace

“RAUDHA .. RAUDHA..”

Abinda yake ta faɗi kenan ya kasa ma yin maganan, sai kuma kamar an tsikare sa yaɗau wayan nasa yasake kiran Numban RAUDHAN, wannan karon akashe wayan yake, ai be jira komi ba yayi waje asukwane yana sake neman layin duk da kuwa ance masa akashe ne

Farida biyo bayan sa tayi duk ta ruɗe yanda taganshi shima aruɗe, lokaci ɗaya ya fita hayyacin sa tamkar zararre, but kafin takai wajen ma tuni yaja motar sa yayi bakin Gate, dole takoma ciki tazauna jiran abinda zai biyo baya, duk da kuwa a matuƙar tashe hankalin ta yake abun ku da me ciki gashi ba lafiya tacika ba a kwanakin.

      Babu inda yazarce sai police station, report yaba da akan ɓatan RAUDHA, abun ku da me shi suna ganin kuɗi nan da nan aka haɗa sa da Police zuwa school ɗin su RAUDHA, wasu kuma suka bazama neman ta

Duk wani bincike sai da aka yi but an tabbatar musu RAUDHA bata zo yau ba, daga ƙarshe aka sanƙamo su Rash zuwa station don amsa tambayoyi, koda aka tambaye su abinda suka sani sun faɗi komi basu ɓoye ba, sai dai anƙi sakin su sabida su ake zargi kasancewar su ne mutanen da RAUDHA tayi rabuwar ƙarshe dasu

Haka ƴan sanda suka dage wajen bincike, har a talabijin an saka hotunan ta ko za’a dace amma babu labarin ta har zuwa dare

Zuwa lokacin Suhaib ya gama fita hayyacin sa, kuka sosai yake yi tamkar mace, ƙiri-ƙiri yaƙi tafiya gida babu inda be yawata ba don neman ta but Allah be sa ya dace ba, sai bayan isha’i sannan yakoma gida

A yanda yadawo ne hankalin Farida yasake tashi fiye da yanda take tun safe, musamman yanda yasaka ta gaba sai rizgan kuka yake yi yana sambatu

Be san ya zai yi da rayuwan sa ba idan ba’a ga RAUDHA ba domin bazai taɓa yafe wa kansa ba, kuma yana ji ajikin sa RAUDHA itace bugun numfashin sa idan babu ita to tabbas babu shine, soyayyar da yake mata ba zai iya juran rasa ta a irin wannan yanayin ba

Sai da Farida tayi dagasken gaske wajen rarrashin sa, nasiha tayi ta masa tana nuna masa girman ƙaddara da tawakkali dashi, tabbas ɓatan RAUDHA ƙaddaran sa ne, idan kuma yajure yamiƙa al’amuran sa zuwa ga Allah to Allah me rangwame ne zai sauƙaƙa masa duk kan lamuran sa

Wannan nasihan da tayi masa ne yasanya Suhaib ya raya daren da roƙon Allah wajen bayyana masa ƙanwar sa, yana yi yana kuka cikin ficewar hayyaci, gaba ɗaya aranan be ko runtsa ba saboda tashin hankalin da yariske sa

Sosai Farida ta tausaya wa mijin ta, tabbas tasan yana cikin wani mawuyacin hali wanda samun kansa sai idan RAUDHA ce tadawo.

        Washe gari da mugun zazzaɓi Suhaib yatashi har baya iya tsayuwa sabida tsananin ciwo, gashi ƙiri-ƙiri yaƙi cin abinci in banda waya da yatasa agaba yana faman kira da kuma jirayen kiran babu abinda yake yi

Daga ƙarshe ma fita yaso yi but ya gaza sai kwasan sa akayi aƙasa domin tuni ya sume

Kuka sosai Farida take yi sabida tsananin tashin hankali, duk yanda take jin ciwon ta be kai yanda take jin tashin hankalin halin da mijin ta yake ciki ba

Waje tafita takira ma’aikatan gidan su biyu da me gadi suka haɗu suka ɗauke sa zuwa mota, drever yaja aka nufi asibiti dashi

Direct emargency aka nufa dashi

Kuka kawai Farida take yi ta kasa zaune ta kasa tsaye ko jin nauyin cikin nata bata yi, wayan Yayan ta takira tafaɗa masa halin da ake ciki, ai kuwa babu jimawa yazo, shine yayi duk wani abinda ake buƙata na jigilan asibitin, daga ƙarshe ma yasaka aduba Farida saboda yanda jikin nata yatashi sai numfarfashi take yi

An bata gado akayi mata alluran barci sabida tasamu hutu don shi take buƙata a halin yanzu.

????????????????????????????????????

A can Station kuwa ba’a saki su Rash ba sai da mahaifin Zen yazo, shine yayi belin su duk da daƙyar aka bashi don shima sai da yasaki bakin aljihu.

       Wajen awanni biyu kafin Farida tafarka, lokacin har mahaifiyar ta da ƙanwarta Maryam wacce akayi musu aure tare sun zo, ita Maryam ɗin ne tazo musu da abinci, don haka Mahaifiyar su wato Umma tace ma Maryam ɗin tazuba ma Farida abinci taci

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button