RAUDHA Page 21 to 30

Tun be ƙarisa zancen ba RAUDHA take kuka sosai
Shi kansa Suhaib tuni idanuwan sa sun kaɗa sun yi jazur sun tara hawaye, rungume RAUDHA yayi cike da tsananin tausayin kansu
Daddy shima daga can hawayen yake ta faman share wa, taya zai iya rayuwa na tsawon shekara batare da ya ga Iyalan sa da suka fi soyuwa a ransa ba? Babu wanda yake tausayi sama da RAUDHA, yasan zata shiga wani mawuyacin hali sabida rashin sa, daɗin sa ma da akwai Suhaib, da be san ya zai yi da rayuwan sa ba
Shanye hawayen sa yayi, cikin jarumtan muryan sa yahau rarrashin su gaba ɗaya, yana faɗa musu kalamai masu daɗi
RAUDHA dai taƙi yin shiru sai kuka take yi tana kiran sunan Daddy
Ganin lokacin da aka ɗiba masa na yin waya dasu ya kusa ƙare wa, hakan yasa yakira sunan Suhaib ɗin
Murya na rawa Suhaib ya amsa yana share ƙwallan shi da suka zubo saman kuncin sa
“Suhaib ga amana nan na bar maka, kai kaɗai RAUDHA take dashi a yanzu, kai ne kaɗai gatan ta, a yanzu kai kaɗai ne zaka zame mata Uwa, uba, yaya da kowa ma, Ni yanzu addu’ar ku nake buƙata, idan har da rabon gaskiya zai fito zan dawo gare ku nan kusa, idan kuma Allah be nufa ba, ya ƙaddara dole sai nayi zaman Jeil na shekara ɗaya zan ɗau ƙaddara ta, Ni dai fatana a yanzu Suhaib ka kula da ƙanwar ka, ina so in dawo in yi alfahri da ita, ka kula da ita da kyau, kayi haƙuri da duk wani halayen ta, ina son ka kula da tarbiyyan ta”.
Cikin raunin murya Suhaib yace, “insha Allahu Daddy nayi maka alƙawarin kula da Baby, zaka dawo kasha mamaki saboda sauyawan ta, babu abinda zai faru da ita, zan kula da ita sosai”.
Murmushi me sauti Daddy ya saki, kafin yace, “yauwa Allah yayi muku albarka gaba ɗaya, kaci gaba da kula da komi nawa, nasan yanzu ba lallai ku sake ji na ba, domin wannan shine daman da aka bamu na ƙarshe da zamu iya yin waya, yanzu zan kashe wayan”.
Suhaib addu’a ya soma ma mahaifin nasa akan Allah ya bayyana gaskiya, shi kuma yana amsa wa cike da ƙaunar ɗan nasa
Da zasu yi sallama Daddy yana ta kiran sunan RAUDHA, but ƙiri-ƙiri taƙi amsa wa sai kuka take yi, sai da taji ya kashe wayan kafin tayi saurin wawuran wayan tana me sake fashe wa da kuka, tana kiran sunan Daddy kamar wacce zata shiɗe
Sosai Suhaib ya rungume ta ganin yanda take kukan kamar ranta zai fita, sai faman sambatu take yi tana faman kwaɗa wa Daddyn ta kira
Abu kamar wasa Suhaib ya rasa gane kan RAUDHA, yayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, daga baya ma dukan sa tasoma yi sai ya sake ta, kasancewar ya riƙe ta gamm ganin tana bige-bige, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya ɗauke a jikin ta.
[2/26, 1:34 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????????: ✍️
???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓
???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️
????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????
????.????.????????/
.
???????????? ???????????????????????? ___________________________????
???????????????????????? ???????????????????????? ????????????????????
_______???? Farida ce tashigo ɗakin a rikice, sabida ihun RAUDHAN ne ya tashe ta daga barci shine ta hayo saman taga me ke faruwa
Dai-dai lokacin da Suhaib yake ƙoƙarin zuba mata ruwa a fuska, shima ɗin duk a rikece yake hankalin sa duk ya tashi
Da sauri taƙariso wajen gadon tana tambayan sa abinda ke faruwa
Be iya ce mata komi ba saboda hankalin sa na kan RAUDHA da ta kawo numfashi, sai dai bata buɗe idanu ba illa wani irin nannauyan barci da ya kwashe ta
Girgiza ta Suhaib ya soma yi yana kiran sunan ta, sai daga baya shima ya fahimci barci ne ya ɗauke ta, mamaki sosai ya cika sa da barcin nata, da sauri ya sake zuba mata ruwa ko wai zata farka, amma ko motsin kirki taƙi yi, ga dai shi numfashin ta na fita normal irin na masu barci amma taƙi farka wa
Farida dake tsaye kan su itama tana kallon RAUDHAN, duk hankalin ta ya gama tashi, sake tambayan sa tayi
Anan ne ya faɗa mata abinda ke faruwa, har zuwa suman da RAUDHA tayi, kafin yaja numfashi yana saka hannun sa a aljihu don ɗauko wayan sa ya kira doctor, domin dai hankalin sa ya gaza kwanciya da wannan barcin da RAUDHA ta kama a lokaci ƙanƙani
Shaf ya manta ma, yau be yi amfani da wayan sa ba, kuma a kashe ya barta tun jiya, wannan dalilin ne ma Daddy da ya kira sa be same sa ba, sai ya kira RAUDHA
Kallon Farida yayi yace, “Wifey ɗauko min wayana in kira Doctor, sabida hankalina ya gaza kwanciya da wannan barcin da Baby ta hau yi, anya ma barcin take yi?”
Umarnin sa Farida tabi, tafice da sauri taje ta ɗauko masa wayan
Kiran doctor yayi ya sanar masa da halin da ake ciki
Nan yayi masa alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, tunda yau weekend ne yana gida.
Babu jima wa kuwa sai gashi yazo, duba RAUDHA ya hau yi, sai dai shima be gano komi dake damun ta ba illa barcin
Nan ya yi wa Suhaib bayani kafin yayi masa sallama ya fita
Sai alokacin ne hankalin Suhaib ɗin ya ɗan kwanta, rufe ta yayi da bargo sannan suka fito shi da Farida, a Parlour suka zauna zugum duk rai babu daɗi, musamman Suhaib da damuwar suka haɗu sukai mishi yawa, ga matsalan Daddy da be san ma ta ina zai soma ɓullo wa al’amarin ba, ga kuma halin da RAUDHA take ciki.
A haka ranan suka wuni sukuku, har dare RAUDHA bata farka ba, hakan yasa hankalin Suhaib ya sake tashi, dole ya sake kiran wani doctor ɗin ya duba ta, shima ɗin be gano komi ba, barcin dai ya sake faɗa musu shi take yi
Abun da zai basu mamaki shine duk yanda Suhaib yayi ƙoƙarin tashin ta amma ko motsi taƙi yi, ya zuba mata ruwa yayi duk wani dabara taƙi tashi, sai sharɓan barci take yi, dole ya haƙura ya bar wa gobe, idan ma bata farka zuwa goben ba ya yanke shawaran Hospital zai kai ta.
Washe gari ƙarfe 07:39am RAUDHA ta farka
Farin ciki duk ya cika Suhaib sai tambayan ta yake yi “ko akwai abinda ke damun ta?” sai dai kuma taƙi yin magana, juyin duniya Suhaib yayi mata magana but taƙi tanka sa, ga dai shi tana kallon sa amma taƙi ta kula sa, kuma taƙi cin abinci, ga idanuwan ta da suka sauya kala, su ba kore ba su ba ja ba
Sabon tashin hankali Suhaib ya sake shiga, shi da Farida gaba ɗaya sun tsorata da yanayin da RAUDHAN ta tashi
Koda yayi yinƙurin kai ta asibiti, ita RAUDHAN taƙi yarda, sai ma kwanciya da tayi ta juya masa baya taƙi koda kallon sa
A taƙaice dai a ɗakin Suhaib ya wuni yaƙi jirga wa ko nan da can, duk yanda ya kai da lallaɓa ta akan ta tashi koda abinci ne taci, taƙi kula sa, dole ya haƙura ya ƙyale ta ba don ya so ba.
Bayan sallan Asar da yadawo ɗakin ne ya ganta tana ƙoƙarin sauko wa daga gadon, da sauri ya ƙarisa wajen ta jikin sa na rawa yakira sunan ta
Ɗago kai tayi ta kalle sa da idanuwan ta da suka koma fari fatt a yanzu ɗin, ɗan kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace dashi, “Yunwa..”