RAUDHA Page 21 to 30

Ɓata fuska RAUDHA tayi kawai batare da ta tanka su ba
Suhaib ya janyo ta jikin sa yana cewa, “Baby baki ce komi ba, kina jin zamu yi baƙo?”
Baki ta taɓe tace, “to Ni ina ruwana dashi”.
Murmushi Suhaib yayi yace, “ai kuwa ke kike da ruwan ki Baby, Yaron Uncle Hassan ne fa, wanda ada yake siyo miki chaculate time ɗin kina ƴar ƙararrama, sai ki maƙale masa idan yazo gidan mu kice sai kin bi shi, har kin manta sa ko?” Yayi maganar cike da tsokana
Turo baki tayi tace, “Ni Yaya na manta shi, kuma bazan iya tuna shi ba”.
Hancin ta yaja yace, “dama wasa nake miki Babyna, time ɗin ai kinyi ƙarama da yawa, but ina so in faɗa miki zamu je Ƙasar India wajen likita, saboda Haneep, zaki bi Ni Ko zaki zauna ki kula da karatun ki?”
Kallon sa tayi, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin murya tace, “bazan je ba”.
Murmushi Suhaib yayi domin shima yafi son hakan, gwara ta zauna tayi karatun ta har sanda zasu dawo, tunda a ganin sa yanzu yana da wanda zai ba ma amanar ta, hankalin sa kwance zai bar ta yaje ya dawo.
Share this
[ad_2]