RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

Ɗan kallon sa tayi taɗauke kai tana sake lafe wa akan kujeran tace “bana jin zan je yau bana jindaɗin jikina”.

“No Babe yakamata ki je, nasan ke mayyan rawa ne I have surprise for you”.

Murmushi tayi tana kallon sa kafin kuma tagyaɗa kanta tace “ok zan zo”.

“Yeees ko ke fa Babe”. Yafaɗa cike da murna

Daga nan hira suka ci gaba dayi, inda Zen ɗin ne ke bata labarin birthday ɗin yana ƙara ƙawata mata abun don yashiga ranta sosai.

      Suna shiga school ɗin RAUDHA tafito daga motan tawuce class, yayinda su kuma suka fice a school ɗin har da Rash da tace baza ta shiga Lecture ɗin ba.

       ????????????????????

Direct gida RAUDHA ta wuce da suka gama Lecture, babu kowa a Parlour lokacin da tashiga sai tawuce ɗakin ta, tana shiga tafaɗa kan gado sai barci don shine a idanun ta ga kuma gajiya da take ji sosai a jikin ta

Sai 06:30pm. Tatashi daga barcin, wanka tayi tasaka ƙaramar riga shimi kalan sararin samaniya sannan tafito Parlour

Suhaib na zaune yana aiki da computer’n sa taƙariso wajen sa tazauna tana ɗaura kanta saman kafaɗan sa

Kallon ta yayi yana shafa fuskar ta da hannu ɗaya yace “Baby kin tashi? Na shigo naga kina barci”.

Gyaɗa masa kai tayi tana lumshe idanun ta

Shima be sake cewa komi ba sai yamaida hankalin sa kan aikin sa yaci gaba dayi

Can kamar shuɗewar mintuna biyar tace “Yaya har yanzu Daddy shiru yaƙi kiran mu”.

“Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu nasan babu wata matsala sai kira mu da yardan Allah, idan kuma hakan be faru ba zan je har can ɗin in dubo sa”.

Kallon sa tayi tana riƙo damtsen hannun sa da duk ka hannayen ta, cikin marairaice fuska tace “yaya nima kaje dani?”

“Baby school ɗin ki fa?”

Turo baki gaba tayi tace “a’a Ni dai kaje dani”.

Shafa kanta yayi alamun rarrashi yace “to shikenan zamu tafi tare duk sanda na tashi tafiya, akwai aiki a Office sosai ga kuma Wifey bata jin daɗin jikin ta that’s why bazan je yanzu ba”.

Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana jin kewar Daddyn nata na ƙara shiga zuciyarta, sosai take buƙatan sa a kusa da ita but yayi mata nisa, tana ji a ranta tamkar wani abun ne yasame sa tunda gashi an shafe tsawon lokaci babu labarin sa bare wayan sa tashiga

Maganar Suhaib ɗin ne yadawo da ita hayyacin ta

“Baby ɗaga Ni zan je sallah gashi can an soma kira, kema kije kiyi kinji?”

Bata ce masa komi ba illa miƙewa da tayi tanufi sama, tana shiga takwanta abunta bata ƙara motsi ba, sai da wayan ta tasoma ringing kafin tatashi ta ɗauka tayi peacking, lumshe idanun ta tayi tana saka hannu saman goshin ta tare da matse gashin kanta ta tattare shi zuwa baya, da alamun dai tana sauraron me maganar ne ta cikin wayan, sai kuma ta yamutsa fuska cike da sanyin murya sosai tace

“Ok I will”.

Daga haka bata sake magana ba har sanda tagama wayan tacire a kunne tana ajiye wa, miƙe wa tayi tashige Toilet tasillo wanka tafito sanye da towel iya cinyan ta, kan stool tazauna tasoma shafe-shafen ta, duk abinda take yi a hankali take yin sa kamar baza ta yi ba, sosai idan kakalle ta zaka ga damuwa aranta, ko kaɗan bata jindaɗin jikin ta, ta rasa kuma meke mata daɗi ga dai tanan ne

Bayan ta gama tashirya cikin guntun wando Light blue, sai tasaka riga da yatsaya mata iya setting wandon me dogon hannu tamkar na sanyi sai dai be da wani nauyi sosai, kalan ruwan ƙasa ne sai siraran zane da aka zana guda uku daga ƙirjinta da Red colour, hill shoes tasaka red sannan ta tufke gashin ta a ƙasan ƙeyan ta da jelan gashin, turare tafesa taɗau HangBag ɗin ta tafito Parlour

Yanzun ma Suhaib ne zaune shi kaɗai saman dainning yana cin abinci

“Baby Ina zaki je kuma baki yi dinner ba?”

Wajen sa taƙarisa takwanto da jikin ta saman bayan sa tare da zagayo da hannayen ta a wuyan sa, batace komi ba illa tusa kanta da tayi a wuyan sa tana shaƙar ƙamshin jikin sa idanunta a rufe

Hannu yasaka Suhaib ɗin yazagayo da ita ta gaban sa yaɗaura ta saman cinyan sa, sai tasake shigewa jikin nasa still idanun ta a rufe

Numfashi ya ɗan ja yana shafa tattausan gashin kanta, sosai yake tausayin ƙanwar tasa tare da wani irin mahaukacin ƙaunar ta a ransa

Tsawon lokaci suna a haka, sai da wayan ta yayi ƙara sannan Suhaib ɗin yaɗago ta don ita taƙi motsawa ko kaɗan

“Sweetheart ana kiran wayan ki”.

Bakin ta takai kan nashi tasakar masa kiss ???? kafin tamiƙe tana kallon sa da shanyayyun idanuwan ta tace “Yaya sai na dawo”.

Be iya ce mata komi ba illa bin ta da kallo da yake yi har takai bakin ƙofa tafice

Numfashi yasauke cike da tausayin ta, sosai yaga damuwa a fuskarta kuma yasan RAUDHA ko kaɗan ba ta faɗa ma kowa damuwar ta, koda kuwa ya tambaye ta ne kafin tafaɗa masa aiki ne, tana da zurfin ciki ga duk abinda ke damunta, ko kaɗan baya jindaɗin fitan daren nan da take yi duk da kuwa yasan inda take zuwa, sai dai babu yanda zai yi sabida idan yace zai hana ta ba sauraron sa take yi ba, yanzu sai abun ma yajuye yakasa gane mata, tabbas yasan ƙanwar tasa tayi mugun sauya wa fiye da tunanin mutum

“Amma meke damun ta me yasauya ta?” Shine amsar da yakasa samowa har yanzu.

     ????????????????

RAUDHA na fita kanta tsaye tayi bakin Gate

Me gadi na hango ta yatashi yabuɗe mata small Door tafice

Motan Zen na waje suna jiran fitowar ta, shi yafito yabuɗe mata murfin motan tashiga

Tunda suka kama hanya ko magana ta kasa musu har suka dan gana ga kyakykyawar club ɗin, tunda tashiga tasamu wuri tazauna bata sake motsa wa ba, tambayan duniya sun yi mata ko akwai abinda ke damun ta amma taƙi yin musu magana illa idanu kawai da tazuba musu

Lokacin da aka sake cika maƙil a wajen sai tamiƙe tafito waje sabida hayaniyan mutanen sosai yake damun ta, hakan har ya soma haddasa mata ciwon kai me tsanani

Haraban wajen haske ne tamkar rana, ba ka sanin ma dare ne sai idan kayi nesa da wajen

Tunda tafito tajingina da wani ƙarfe taharɗe hannayen ta a ƙirji tare da kwantar da kanta jikin ƙarfen tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana sauraron sarawan da kanta ke mata, gaba ɗaya jikin ta kamar ana ƙara zare mata kuzari ne a duk sokonni, izuwa yanzu har rawa jikin nata yake yi, leɓen bakin ta kawai take cije wa sabida yanayin dake baƙuntan ta, har ga Allah baza ta iya fahimtar halin da take ciki ba izuwa yanzu, kawai tasan zuciyarta ta bata umarni kuma tabi

Buɗe idanuwan ta tayi tasoma takawa a hankali zuwa waje, ahaka har tafice Gate ɗin, tafiya take yi batare da tasan inda tanufa ba, a lokacin wajen ƙarfe 10:00pm. Hasken motoci ne kawai ke gilma wa da fitilu

Bata yi nisa sosai ba tasami wasu motoci guda biyu an faka su, jingina tayi ajikin ɗaya tare da zame wa ƙasa tana riƙe kanta sosai, izuwa yanzu duniyar ce take juya mata hakan yasa takasa tafiya tazauna nan, tana nan zaune tajiyo motsi sai dai ta kasa motsawa bare ta ɗago kanta da ta ɗaura saman gwiwar ta, bata san meke faruwa ba amma taji an haske ta da fitila me tsananin haske sai kuma tajiyo surutun mutane inda ɗaya ke cewa

“Baaba mun yi kamu fa, ka ga wata cikas anan kuwa…”

Daga nan bata sake fahimtar maganar da suke yi ba illa ji da tayi an ɗago ta an sanya mata wani ƙyalle an rufe mata hanci da baki, daga nan ne talumshe idanuwan ta numfashin ta yaɗauke gaba ɗaya.

      Saka ta suka yi a cikin mota suka ja da gudu suka bar wajen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button