RAUDHA Page 21 to 30

Daƙyar taci sabida hankalin ta na ga Mijin ta, don Umman taƙi barin ta zuwa wajen sa ne saboda gargaɗin da Doctor yayi musu adena barin ta tana zirga-zirga da yawa Cuz tana buƙatar hutu sosai.
Sai yamma kafin Umma tasoma tafiya, daga baya itama Maryam tawuce da zummar idan ba’a sallame su ba zata aiko musu da abinci.
Lokacin da Suhaib ya farka Farida na wajen sa, tunda yatashi yagansa a asibiti yatashi hankalin sa akan sai an sallame sa, acewar sa bazai zauna anan ƙanwar sa kuma na can cikin wani hali ba be je ya neme ta ba
Daƙyar doctor yashawo kansa har ma yayarda yazauna zuwa safe, gashi dama ko kaɗan bashi da ƙwarin jiki don tun jiya rabon sa da abinci, yaƙi saka komi acikin sa sai ruwa
Yanzu ma daƙyar Farida tashawo kansa yaci abinci doctor yazo yaba sa drugs yasha, baya buƙatar raunin sa a yanzu yafi son kuzarin sa yadawo ta yanda zai fita neman Ƙanwar sa
Kwana yayi a ranan yana waya da Police don jin me ake ciki, har yanzu dai babu labarin ta.
.
_To sai muce Allah yabayyana maka ƙanwar ka Suhaib._
[2/22, 3:59 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON TWENTY TWO*
_______???? RAUDHA bata farka ba har washe gari
Wajen ƙarfe 07:00am. Wani magidanci yazo wuce wa yahange ta, da farko ya ji tsoro sai dai kuma yayi shahada wajen ƙarisawa wajen ta, hannu yakai yana taɓa ta sai dai ko kaɗan babu alamun numfashi a tattare da ita, sai da yasake kai hannun sa setting hancin ta nan ma be ji komi ba, sai yariƙe tsintsiyan hannun ta anan ne yatabbatar tana da sauran rai, ajiye fatanyan sa yayi yaɗago ta yasaɓa a kafaɗa sannan yayi hanyan gida
Kasancewar safiya ne mutane duk suna gida basu kai ga fitowa ba, don haka har yakai gida be haɗu da kowa ba duk da babu nisa sosai da rugan da suke
Yana shiga yasoma ƙwala wa matar sa kira
Da gudu Lantana tafito tana aza ɗankwalin ta kanta at the same time tana amsa mishi da faɗin “Malam lafiya..?”
Sai dai bata iya ƙarisa maganar ba ganin sa saɓe da RAUDHA a kafaɗa
“Tukunna dai ɗauko min Tabarma sai in miki bayani ko?”
Lantana ta’amsa mishi dasauri tana shigewa ɗaki taɗauko tabarman kamar yanda ya umarce ta, shimfiɗa wa tayi sannan yasauke RAUDHAN akan tabarman
“Malam wannan yarinyan daga ina, aina kasamo ta?” Lantana tayi masa tambayan lokacin da tasami waje tazauna tana kallon sa
“To nima dai ga tanan tsintan ta nayi cikin jeji, ganin tana numfashi shine nataimaka nakawo ta nan”.
“To Malam me zai saka kakawo mana ita nan bayan gidan me Gari zaka kai ta? Mu kuma me zamu yi mata?”
Ɗan sauke numfashi Malam Umaru yayi kafin yace, “to nayi tunanin hakan nima ai, sai kuma na tuna ɗazu da asuba da muka yi sallah me Gari ya sanar mana zai yi tafiya a lokacin, har yake neman addu’ar mu shiyasa nayi tunanin kawo ta nan ɗin tunda ko an kaita can babu me kula da ita”.
Lantana da idanun ta suka ƙi ɗauke wa akan RAUDHA tasake cewa, “Malam nifa wlh ina jin tsoro, yarinyan fa ko motsi bata yi yanzu mu wani taimako zamu bata? Kai da ganin yarinyan nan kasan ƴar cikin birni ce, asibiti Ya kamata a kai ta, kar mu zo Garin taimako mu afka cikin matsala, idan ka kaita can sai kayi musu bayanin tsintan ta kayi kaga sai su nemi ƴan uwanta tunda su ƴan birnin sun san yanda zasu yi su same su”.
Kallon Lantanan yayi yace, “ke kina ganin haka kawai zan kai ta asibiti baza su caje Ni kuɗi ba? Dole sai mun biya kuɗi kuma kinsan ban da komi a yanzu, sannan wannan yaron ban san ranan dawowar sa ba da sai yataimaka mana, amma Ni abinda naga ya dace ki je gidan Jummai me magani tazo taduba ta sai aga abunda hali zai yi, kinga idan muka samu tafarfaɗo sai tafaɗa mana inda take mu maida ita, kinsan be kamata mu bar ta bamu taimaka mata ba domin tana buƙatar taimakon, Allah yaga zuciyar mu zai bamu nasara, ko sada ta muka yi da ƴan uwan ta zamu samu lada”.
Ajiyan zuciya Lantana taja cike da sanyin jiki tace, “to shikenan Malam Allah ya bamu ikon taimakon nata, bari inje sai mu taho da Jumman”.
“Amin Amin”. Malam Umaru ya’amsa mata
Sai da tashiga ɗaki tayafo mayafi kafin tafice zuwa gidan Jummai me maganin gargajiya
Har suka dawo ita da Jummai Malam Umaru yana nan zaune a wajen, nan dai yawuce gona yabar Jummai na duba RAUDHA akan bazai daɗe ba zai dawo, in yaso idan yadawo sai yaji meke faruwa.
Buga tagumi Lantana tayi tana kallon Jummai da tazuba kayan magungunan ta tana ta faman duba RAUDHA
Bayan wasu lokuta taɗago tana kallon Lantanan kafin tace, “Iy to matsalan yarinyan nan babba ne domin dai gaskiya yafi ƙarfi na, na kasa gano komi a tattare da ita, amma kuma albishir ɗin da zan iya muku shine zata farka a ɗan ƙanƙanin lokaci, wannan turaren kin ganshi ko?”
Jummai taƙare maganan da ɗago mata turare a ɗan kwalba, sannan ta haɗa mata da wasu saiwan icce taci gaba da faɗin
“Zaki samu garwashin wuta ki murmusa wannan iccen akai, sannan sai ki ɗiga turaren nan a wutan da zaran iccen ya gama ruruwa, zaki kawo garwashin kusa da kanta ki riƙa turare ta a ƙalla sau uku a rana, zata iya farkawa zuwa gobe ko kuma nan da kwana biyu, yanzu zaki fara daga yau ne, sau uku zaki yi mata a yau ɗin kina ji?”.
Gyaɗa kanta Lantana tayi dasauri, sannan tamiƙa hannu ta’amsa tana faɗin, “to iya abinda za’a yi kenan?”
“Eh iya abinda za’a yi mata kenan, idan kuma kwana biyu ya shuɗe bata farka ba sai ki taso ki faɗa min Ni kuma Nasan me zan yi”.
“To mun gode Allah yasaka da alheri, Allah dai yataimake mu ta tashi ɗin”. Cewar Lantana cikin jimami
“Zan wuce idan Mijin naki ya dawo sai ki faɗa masa”.
Lantana tace, “to shikenan Jummai idan yazo ɗin zan kawo miki kuɗin har gida”.
Miƙewa Jummai tayi bayan ta harhaɗa kayan ta, suka sake yin sallama sannan tafice a gidan.
Kamar yanda Jummai ɗin tace mata tayi, hakan kuwa tayi wa RAUDHA
Babu jimawa Malam Umaru yadawo Lantana tafaɗa masa yanda suka yi, kuɗi ya ba ta sadaka kamar yanda ake bata idan har ba faɗan yawan kuɗin tayi ba, Lantana ta’amsa tanufi gidan Jummai me magani takai mata kuɗin ta dawo
Tana dawowa Malam Umaru yace, “Ya kamata ki gyara mata ɗakin Basiru amayar da ita can don be kamata abarta anan ba”.
“To Malam bari inyi”.
Ɗakin Basirun Lantana tashiga da tsintsiya a hannun ta, cikin ƙanƙanin lokaci tashare ta kakkaɓe katifar ɗakin tasauya da wani zanin gadon, sannan tafito ta sanar wa Malam ta gama
Shi ya ɗauki RAUDHA zuwa ɗakin yashigar da ita
Ita kuma Lantana sai tanufi ɗakin ta taɗauko Zani talulluɓe wa RAUDHA jikin ta kasancewar ba wani kayan kirki ne da ita ba, gaba ɗaya santala-santalan ƙafafuwan ta a waje suke, ga gashin kanta shima a buɗe ya wargaje, sai da takama mata gashin taƙulle mata ta yanda bazai dame ta ba sannan tafito daga ɗakin
Anan Malam Umaru yayi mata sallama cewar ya fita zuwa majalisa, tayi masa adawo lafiya sannan tanufi bakin murhu tasoma kaye-kayen ɗaura girkin dare.