RAUDHA Page 21 to 30

Da dare suna zaune a tsakar gida suna cin abinci, Malam Umaru yakalle Lantana bayan ya kai loman tuwon bakin sa, sai da ya haɗiye sannan yace, “Kin kuwa yiwa yarinyan nan turaren?”
“Eh nayi mata Malam, saura ɗaya ne yanzu idan mun kammala sai inyi mata”.
Gyaɗa kansa yayi be sake cewa komi ba, sai da yagama cin abincin yasha ruwa tare da sakin gyatsa yafurta “alhmadulillah Allah mun gode maka, Allah kakawo mana na kullum”.
Lantana ta’amsa masa da “ameen Ameen Malam”.
“Yanzu haka zamu zuba ido mu bar Basiru yana tafiya gantali sai yayi kwana da kwanaki kafin mu saka sa a idanun mu?”
Tsame hannun ta daga kwanon tuwon Lantana tayi, fuskarta akwai damuwa sosai izuwa yanzu, sai dai kuma ya zasu yi dole sai haƙuri, Kallon sa tayi cike da sanyin murya tace, “to ya zamuyi Malam? Abinda Basiru yazaɓar wa kansa kenan, sai mu bi sa da addu’a Allah shi zai shiryar mana dashi”.
“Hakane to Allah yashirye sa, amma abun na matuƙar damu na, ace ɗa ɗaya ya gagare mu?”.
“Amin, wata rana zai shiryu insha Allahu, rayuwan ne yanzu sai ahankali, domin ba kaɗan ba Abokan banza suna taka muhimmiyar rawa wajen gurɓacewar Yara, Allah yasa mu dace”.
Malam Umaru ya’amsa da “Ameen”. Sannan yaƙara da faɗin, “ya kamata kije kiyi mata siracen nan dare na yi”.
“To Malam”. Lantana tace hakan tana miƙewa bayan ta harhaɗa kwanonin tuwon da suka ci
Kichen takai sannan ta wanke hannun ta tanufi cikin ɗakin ta don ɗauko turaren
Shi kuwa Malam Umaru gyara zaman sa yayi bayan ya gama wanke hannun sa da baki da butan dake ajiye a gaban sa, rediyon sa yajawo yakunna yana karawa a kunne bayan ya jingina da bango ta yanda zai ji daɗi.
Sai da tagama yin mata siracen sannan tarufo ƙofan tadawo wajen Malam tazauna suna ɗan taɓa hira jefi-jefi yana kuma sauraron rediyon sa, ahaka har dare ya tsala kafin su je su kwanta.
Washe gari RAUDHA bata farka ba har dare, wuni Lantana take yi a ɗakin tazauna tasaka ta gaba tana ta kallo, ko kaɗan bata rabo da mamaki aranta, komi zuwan mata arai yake yi game da RAUDHAN, duk da kuwa ɗari bisa ɗari ta yarda da mutum ce ita, amma kuma wani lokacin sai tayi tunanin ko dai ba ƴar nan bace? to daga ina take me yakawo ta nan da har Mijin ta zai tsince ta? Abubuwa dai kala-kala.
The following day bayan Malam Umaru ya tafi aikin gonan shi itama Lantana tashirya don tafiya bikin ƴar ƙanwar baban ta da ake yi a cikin anguwan, rufe ɗakin da RAUDHA take kwance tayi tasaka igiya ta ɗaure sannan tafice agidan bayan ta jawo ƙyauren gidan
Babu me shigo musu gida don haka bata ji ɗar ɗin barin RAUDHA ɗin ita kaɗai ba, duk da bata da tabbacin zata iya farkawa ko kuwa baza ta farka ba.
????????????????????????????????
“Kai Baaba sanƙamo min wayar ka in saka layina ciki don nawan nan ba kanta ƙalau ba, kuma ina tunanin zuwa anjima Master zai kira ni”.
Miƙo masa wayan yayi yana cewa, “to yanzu da ƙarfe nawa zan zo ɗaukar ka?”
Wulla idanun sa Basiru yayi cike da duniyan ci yace, “zuwa dare kazo ka sanƙame Ni sai mu fantsama”.
“Ok ba damuwa”.
Wayan yamiƙa masa yana buɗe motan yafito yana faman gyara wandon sa, sai da yayi dogon hamma yagama miƙar sa kafin yabugo ƙofan motan yarufe, sannan yasaƙalo da kansa cikin motan yana kallon Ƙwaro yace, “Kai Baaba ka biya ku taho tare da Garzali don yau akwai fa zaman meating, kar kace kuma ban faɗa maka ba”.
“Baka da damuwa ai Oga, zan biya mu taho tare”.
Janye kansa Basiru yayi kafin yajuya yanufi gidan su bayan ya ɗaga masa yatsu biyu yana masa umarnin tafiya.
Da fito yashiga gidan yana jan ƙafafu tamkar me koyan tafiya, nan kuwa duk cikin iskancin sa ne, wur-wurga idanu yasoma yi cikin gidan still yana ci gaba da fiton sa, shi dama ba wai damuwar sa bane da ganin iyayen nasa don haka ya hura hanci yanufi ɗakin sa, ganin an ɗaure ɗakin da igiya sai yaja tsaki yana faɗin, “kai wlh Lantana wata iriyan baƙauyiya ce, har yanzu taƙi tafaso gari ta waye, don wulaƙanci da igiya ne zata ɗaure min ɗaki duk da tasan akwai eya ne a ɗakin, wa billahil lazi nashiga naga anyi min wuff da kaya sai na nuna mata asalin kalo na agidan nan”.
Da ƙarfi ya buga ƙofan ɗakin da ƙafan sa yaburma ciki
Ganin mutum kwance a akan katifar sa yayi saurin ja da baya yana ƙara ware idanun sa, sai yanzu ya tabbatar da eh mutum ce a kwance cikin ɗakin sa
“Kutt.. mar uba..” yafaɗa da ƙarfi idanun sa akan RAUDHA
Dasauri yamatsa jikin katifan don yasake tabbatar da zargin sa yasaka hannu ya yaye zanin da aka rufe mata jiki, nan santala-santalan fararen dogayen ƙafafun ta suka bayyana, baki sake yatsaya yana kallon ta batare da ya nuna tsorata ba da ganin ta ɗin, sai kuma yakece da dariya yana faɗin
“Wlh tsuntsu daga sama gashashshe kuttt..”
Yariƙe bakin sa dake buɗe still idanun sa na yawo jikin ta
“Kaii Old man ya iya zaɓi alƙur’an, hhhh wlh na yarda suna son in dawo gida in kintsu tunda suka ajiye min zuƙeƙiyar budurwa haka, yo to aina suka samo ta ne?” Yaƙariƙe maganar nasa yana ɗaga kai alamun tunani????
“Kai anya Old man baya satan yaran Mutane? Daga nace yayi min aure da ƴar birni sai yaje ya sanƙamo ma mutane ƴar su? Yasin wannan babu me yarda yabashi ita, wannan ai ko a yawon duniya na ban taɓa haɗuwa da kyakykyawar yarinya kamar ta ba, anya ma?..”
Sai kuma yayi shiru yana duƙawa gaban ta yasoma shafa ta, jin wani irin taushi da skin ɗin ta ke dashi ai tuni ya soma lanɗe baki
“Na rantse da Allah ko aljana ce yarinyan nan sai na kusance ta, wayyo daɗi”.
Dasauri ya miƙe ya soma cire kayan sa cikin zumuɗi da tsananin sha’awan da yataso masa sakamakon taɓa ta da yayi, har wani rawa-rawa jikin sa ke yi.????
????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️
[2/22, 4:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON TWENTY THREE*
_______???? “Subhanallah.. me kake yi haka Basiru?” Cewar Lantana da tashigo cikin ɗakin tahangi Basiru na ƙoƙarin zuge zip ɗin wandon sa
Cak yatsaya yana juyowa yakalle ta a kaikaice, sai kuma yakwashe da dariya yana nuna ta da yatsa yace “Kinji ki Lantana da wani zance, yo me zan yi kuwa in ba eya ne ba kin gane ai?” Yaƙarike maganar yana ɗage mata gira
Lantana da tagane abinda yake nufi tace “shin Basiru kanka ɗaya kuwa? agidan iyayen ka ko kunyan mu baka ji shine kazo zaka hayayyaƙe wa yarinya haka kawai baka san komi akanta ba”.
“To Lantana Ina ce matar da kuka yi min ne tunda nace muku kuyo min aure?”
Girgiza kanta tayi tace “A’a wannan yarinyan mahaifin ka yatsinto ta acikin jeji, ina mu ina aura maka wannan yarinyan?”
Tsaki yaja yace “to wlh ko ma ƴar uban wacece ta zama nawa, wlh ita zaku aura min don tayi min, ki ware kawai ki bar Ni nashaƙata da ita..”
Be rufe baki ba ƙaran da RAUDHA tasaki yakaraɗe ilahirin gidan baki ɗaya, idanun ta a rufe suke har a time ɗin batare da ta buɗe su ba