RAUDHA Page 21 to 30

Idanun Suhaib jazur ya ɗago kansa yana kallon Malam Umaru ya ce, “Malam menene haɗin ka da ƙanwata? Ya akayi tazo hannun ka?”.
Malam Umaru duk jikin sa ya yi sanyi, daƙyar ya iya cewa, “wlh nima yallaɓai tsintan ta nayi a wani jeji, shine na taimake ta”.
Daga nan ya soma faɗa musu komai tiryan-tiryan
Sosai hankalin Suhaib ya sake tashi da jin ƙanwar sa a jeji aka tsince ta, kuma cikin mawuyacin hali, Allah kaɗai yasa da rabon zata sake rayuwa har su gana, da tuni Dabbobin daji sun cinye masa ƙanwa
Ɗago kanta yayi yana kallon ta cike da tsantsan tausayawa, kana ya kalli ƙafan nata, ai kuwa sai da hawaye suka cika masa idanu sabida ganin ƙafan a nanƙwaye, saurin saka hannu yayi ya taɓa
Sai ta callara ƙara sabida azaban da ya ziyarce ta
Nan da nan Suhaib ya sake ruɗe wa, miƙe wa yayi dasauri ya saɓa ta a kafaɗa yana kallon Farida ya ce, “Wifey sallami bawan Allan nan, zan kai ta asibiti aduba mata lafiyan ƙafan ta”.
Be jira cewar ta ba yajuya yafice dasauri, a back seat ya kwantar da ita yashiga mazaunin drever, da wani irin Speed yaja motan yanufi gate yana danna Horn da ƙarfi
Tuni me gadi ya buɗe masa ya fice.
[2/22, 4:27 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON TWENTY FOUR*
_______???? Suna zuwa asibiti aka amshe ta sabida ya saki kuɗi, Doctors sun yi iya yin su don ganin ƙafar RAUDHA ya dawo dai-dai, duk da duk wani bincike da suka yi basu gano matsalan ba, kuma shi ƙafan ba targaɗe ba; ba karaya ba ba komi ba, lokacin da zasu jajja mata ƙafan sai da suka yi mata alluran barci, shiyasa har suka gama duk abun da zasu yi bata san ma suna yi ba
Doctor ɗin da ya jagoranci duba ta, yayi wa Suhaib bayani basu gano komi ba, amma dai sun saka mata magani da yardan Allah ƙafan zai dawo dai-dai, a hasashen da suka yi.
Wajen ƙarfe 03:20pm. Drever yakawo Farida, har da abinci ta taho musu dashi, kuma bata tafi ba sai da ta ga farkawan RAUDHAN
Suhaib ne yayi ruwa yayi tsaki akan shi zai kwana, duk da Faridan tace masa “ya bari zata kwana da ita”. But yaƙi, dole tatafi ta bar shi.
Washe gari alhmadulillah ƙafan nata ya dawo dai-dai, sai dai ba duka ba, kuma tana jin zafi sosai idan ta taka
Anan Suhaib ya tambaye ta abinda ya faru a ranan, domin shi so yake yi ya hukunta waɗanda sukai sanadin shigar ta haka
Sai dai ta kasa tuna komi, abinda zata iya tuna wa kawai zuwan ta club da fitowar ta haraban wajen, sai kuma farkawan da tayi ta ganta gidan Malam Umaru
Da damuwa Suhaib ya kalle ta yace, “Dear ki dai sake tunani ko zaki tuna wani abun?”
Ɓata fuska RAUDHA dake shan ferfesun zabo tayi, tana zaune saman gadon mara sa lafiya tayi ɗai-ɗai abun ta, tana shirin magana ne wayan Suhaib ɗin tayi ƙara
Ciro ta daga aljihu yayi yana kallon screan ɗin wayan da mamaki, domin dai ba kowa ya kira sa ba illa drevern gidan sa
Ɗauka yayi yakara a kunne yana tambayan sa “Lafiya?” Batare da ya jira cewar sa ba, bare kuma su gaisa
Drever’n faɗa masa yayi gasu a asibiti ya kawo Farida babu lafiya
Tashin hankali ne yasake riskan Suhaib, nan da nan ya tashi ya fice batare da ya bi takan RAUDHA dake masa magana ba
Sai ta kwaɓe fuska tana turo baki, ajiye Plate ɗin tayi akan drowan kusa da gadon, ta ziro ƙafafuwan ta da babu takalmi ta sauko, ahankali take taka ƙafan ta tana cije leɓe, da haka ta ƙarisa bakin ƙofa tafice
Ahanya ta haɗu da Suhaib suna tsaye shi da drever sun yi cirko-cirko
Yana ganin ta yataho da sauri yana tambayan ta “meyasa ta fito?”
Kamar zata yi kuka tace masa, “ba kai ne kafito ka bar Ni ba, kuma ina maka magana ka tafi ka bar Ni”.
Riƙe kansa yayi yace, “Oh I’m sorry Baby hankali na ne ya tashi, Wifey aka kawo ba ta da lafiya, yanzu mu je ki koma kar wani abun ya same ki”.
Girgiza masa kai tayi tace, “a’a, Ni gida zan je, a sallame Ni ni dai”.
“To Baby me zaki je kiyi agida bayan duk gamu anan? Kuma kin ga ai Doctor be sallame ki ba”. Yayi maganar yana riƙo kafaɗun ta ganin kamar ta gaji tana shirin faɗuwa
Cikin yamutsa fuska tace, “yaya Ina son in je in Yi wanka ne, Please ka saka a sallame Ni, bana son zama nan”.
Be musa mata ba, yace mata su koma ɗakin, sai yaje ya nemo likitan ya basu sallaman
Shi ya taimaka mata suka koma, sannan ya zaunar da ita ya fito
Ita RAUDHA ta ƙosa taje tayi wanka ne, shiyasaka ta matsa masa sai an sallame ta, gaba ɗaya bata jin daɗin jikin ta sabida tun ranan da tabar gida rabon ta da wanka, ita da take yin wanka sama da sau uku; huɗu a rana, amma gashi kwana uku rabon ta da tayi, ita kanta ƙyanƙyamin jikin ta take yi, musamman ma idan ta tuna gidan da tatashi ta tsinci kanta, da ɗaukan da Malam Umaru yayi mata, sai dai babu yanda zata yi tunda ahalin lalura take a lokacin.
Drever ya kai ta gida, tana zuwa wanka tayi tasaka ƴar shimi tahaye gado sai barci, ko tunanin ma ta koma asibiti taga halin da Farida take ciki bata yi ba.
Can kuwa a asibitin har wajen awanni huɗu babu haihuwar Farida, duk ta galabaita
Lokacin tuni Umman ta da Ƙanwar ta Maryam sun zo, har babban Yayan su da matar sa duk sun zo, gaba ɗaya sun yi jigun-jigun a reception ɗin suna jiran Likitoci
Sai Suhaib ne da Babban Yayan su suke zirga-zirga wajen samo abin da ake nema
Gab da magriba ta haifo ɗan ta na Miji kyakykyawa irin Suhaib sak, kowa yayi murna sosai, barin ma da aka ce musu babu abunda ke damun Farida, sai dai yaron ne tamkar bashi da lafiya don yaƙi yin kuka
Likitoci sun yi duk binciken da zasu yi akai, sannan suka sanar da Suhaib ɗin abinda ke damun yaron
Be da wani ƙoshin lafiya, irin cutan nan da yake mayar da mutum tamkar soko, yayi ta zulalan miyau, kansa yaƙi tsayuwa waje ɗaya, haka yaron yanzu yake yi, sai dai kasancewar sa jariri baza ka ga alamun zub da miyau ɗin nasa ba, sai idan ya girma
Suhaib ya shiga damuwa sosai, amma likitan ya kwantar masa da hankali, zasu ɗaura sa akan magani idan an dace komi zai wuce, da haka Suhaib ya fito Office ɗin likitan da ƙwarin gwiwa, tunda yaji akwai maganin ciwon yaron nasa, wataran kenan yana iya warke wa.
Koda yashiga ɗakin da aka kwantar da Farida duk ƴan uwan ta ne aciki, tana zaune itama tana shan tea da aka haɗa mata, yaron na kwance gefen ta baza ka ce akwai wani abinda ke damun sa ba
Ɗaukan yaron yayi yana kallon sa cike da farin ciki, ya jima yana riƙe da yaron a hannun sa kafin ya ajiye sa, yayi musu sallama akan zai je ya dawo yafice.
Gida ya wuce kai tsaye, koda yashiga parlour’n be tarar da RAUDHA ba, don haka ɗakin ta yawuce yashiga
Tana kwance har yanzu tana barci
Numfashi yasauke ya ƙarisa bakin gadon, ɗaga kanta yayi yacire pilon yazauna sannan ya ɗaura kanta saman cinyan sa, kallon ta kawai yake yi cike da tausayi, Allah ya gani yana ƙaunar ƙanwar tasa fiye da komi na duniya, soyayyar da yake mata baki ma bazai iya faɗan sa ba