RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 21 to 30

Shafa gashin kanta yake yi idanun sa akanta, sai dai tunani yalula me zurfi, sai da yaji kiran sallan isha’i kafin yatashi ya gyara mata kwanciyar ta yafice

Ɗakin sa ya wuce yashiga Toilet, wanka yasoma yi, don rabon sa da wanka shima ɗin tun washe garin ɓatan RAUDHA, sai da ya ɗauro alwala kafin yafito, shirin sa yayi cikin sauri ya ɗau keey ɗin mota ya fice, sai da yatsaya a masallacin layin nasu yayi Sallah tukun ya wuce asibiti.

      A lokacin su Umma duk sun tafi gida, sai Maryam da aka bari wajen ta

Shima ɗin koda ya isa ba wai zama yayi sosai ba, zuwa ƙarfe goma yayi musu sallama yadawo gida tunda Maryam ɗin zata kwana da ita.

      Koda yadawo ya tarar da RAUDHA zaune a Parlour, tana ganin shi tanufe sa tarungume shi tana masa shagwaɓa, shi kuma sai biye mata yake yi

Koda taji Farida ta haihu bata wani nuna murnan ta ba, ba wai don bata yi farin ciki ba

Shima kuma be damu ba, sai yaja hannun ta suka tafi kan dainning suka soma cin abinci, ita kaɗan taci tunda tarigada taci kafin yazo, daga nan Parlour suka koma, ita kwanciya tayi shi kuma aiki yasoma yi cikin Lapton ɗin sa, kasancewar kwana biyu be je Office ba shiyasaka yake ragewa kar su taru mishi

Sai wajen 12:30am. Ya tashi, lokacin tuni RAUDHA tayi barci, sai ɗaukan ta yayi yamaida ita ɗakin ta, yarufe ta da bargo tare da ƙara mata A.C yafice.

     Kamar shuɗewar awa ɗaya RAUDHA tasoma mummunan mafarki irin na ranan nan, gaba ɗaya ta haɗa gumi da zufa sai makyarkyata take yi, kuma har alokacin bata farka ba

Ƙaton maciji ne yake bin ta acikin baƙin dajin me tsananin duhu da sunkuru, kuka take tayi tana gudu tana waigen bayan ta, duk da kuwa bata ma ganin komi acikin dajin sai macijin nan me kamar wuta jikin sa

Sai da ya cafko ta yana ƙoƙarin haɗiye ta tafarka da ihu me tsananin ƙara, babu inda jikin ta baya rawa, ga kanta da yake faman sara mata kamar zai rabu gida biyu sabida dariyan da ya cika ɗakin, lokaci ɗaya numfashin ta yarabu da gangan jikin ta takoma yaraf kan gadon

Kamar wancan lokacin ihun ta babu wanda yaji agidan, har garin Allah ya waye

Zuwa tara Suhaib ya gama shirin sa zai koma Hospital ɗin, ya saka kuku ya haɗa masa Breakfast Wanda zai kai musu can

Ɗakin RAUDHA yashiga, sai dai ganin ta har yanzu tana barci be tashe ta ba yafice.

     Sai ƙarfe 12:40pm. Kafin RAUDHA ta tashi, babu abinda ta tuna na game da mafarkin ta, sai dai yanda gaba ɗaya jikin ta ke mata ciwo ga tsananin zazzaɓi da yarufe ta, yunwa da ishin ruwa duk ya addabe ta, ita kanta mamakin yanda take jin wani irin bahagon yunwa take yi, ga bakin ta gaba ɗaya ya ƙafe daƙyar take iya samun miyau ɗin da take haɗiya

Rarrafa wa tayi tamiƙe tasauko daga kan gadon, sai dai kuma ƙafan ta ya riƙe sosai daƙyar take iya taka wa, zafi sosai yake mata ba kamar yanda ta kwanta jiya dashi ba, lumshe idanun ta tayi sai ga hawaye sun soma sulmiyo mata, hannu ta saka tashare kafin ta ɗingiza ahankali tanufi gaban Fridge, domin ji take yi tamkar zata mutu idan ba tayi gaggawar shan ruwan ba, ga jikin ta dake mata ciwo ko ina, kamar an hau jikin ta an kwana sukuwa a kanta haka take ji

Buɗe Fridge ɗin tayi taciro goran ruwa, tunda ta kafa a baki bata dakata ba sai da tayi rabin ruwan, kana ta zube nan ƙasa da rawan jiki, nan da nan zazzaɓin ya sake rufe ta, ta kwanta tana kuka sai juye-juye take yi.

    Allah ne yakawo mata Ester, ta shigo gyara mata ɗakin, ai kuwa nan hankalin ta yatashi ta nufe ta tana kiran sunan ta, sai dai gani tayi tamkar ba ta numfashi, nan da nan ta sake rikice wa tatashi da gudu ta fice.

.

_plz share and Voting_

_kar ku manta da Comment plz._

[2/22, 10:38 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   ????????????????????????

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

????????????????????????????????: ✍️

              ???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????

®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

         ????.????.????????/

.

  ???????????? ???????????????????????? ___________________________????

        ???????????????????????? ???????????????????????? ????????????????

_______???? Wajen da aka ajiye Telephone a parlour, nan Ester ta ƙarisa tasaka number ta kira Suhaib

Lokacin yana Hospital ne, don haka koda ta sanar masa sai hankalin sa ya ɗugunzuma ya tashi, tare da Doctor suka taho don bazai iya jiran har yaje ya kawo ta asibiti ba, lokacin tuni ta galabaita kenan.

     Suna zuwa kai tsaye ɗakin RAUDHA suka nufa

Ester na tare da ita, har ta shafa mata ruwa a fuska tunda a tunanin ta ta suma ne, sai dai bata sani ba tsaban ciwo ne yasaka ta dena numfashi, idanun ta a rufe sai hawayen dake gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya jikin ta ya saki sai wani irin ciwon da baza ta iya misalta shi ba take ji.

   Kanta Suhaib yayi yana kiran sunan ta, gaba ɗaya ya kiɗime ya rasa ma me zai yi

Daƙyar Doctor ɗin ya kwantar masa hankali, yace masa “ya ɗauke ta ya ɗaura saman gado sai ya duba ta”.

Kamar yanda yace masa ahakan yayi

Ita tuni Ester ta fice a ɗakin ma

Duba ta doctor ɗin ya soma yi, Suhaib na zaune gefen gadon ya gaza motsa wa, zufa duk ya jiƙa masa jiki sabida tashin hankali, duk da kuwa akwai A.c da fan a ɗakin

Sai da Doctor ɗin ya gama duk abinda zai iya yi, kafin ya kalli Suhaib yayi mishi bayani akan “zazzaɓi ne kaɗai ajikin ta”. Sannan yace masa “a bata abinci taci sai a nemo maganin da za’a bata”.

Rubuta magungunan yayi ya miƙa wa Suhaib

Amsa yayi yana kallon Doctorn kamar zai yi kuka yace, “Doctor yanzu babu abinda ka gano sai zazzaɓi? Ni fa hankali na ya tashi, anya babu wani abinda ya same ta? Ba ka ganin yanda take yi ne?”

Murmushi Doctor yayi yana dafa kafaɗan Suhaib ɗin yace, “kwantar da hankalin ka Man, Ni abinda na gani kenan, ba na tunanin akwai abinda ke damun ƙanwar ka, Just zazzaɓin ne yayi mata kamu sosai that’s why tashiga wani hali irin haka, but insha Allahu komi zai zama normal idan aka bata maganin nan, in kuma be sauka ba to sai a dangana ga asibitin”.

Gyaɗa kansa Suhaib yayi cike da gamsuwa, kana yamiƙe tare da yi wa Doctor ɗin godiya

Tare suka fita cikin ɗakin, ɗaya daga cikin ma”aikatan gidan ya aika ya siyo masa maganin a Chamis, sannan ya koma ciki, shi da kansa ya haɗo mata Lunch ɗin da Kuku ya gama akan faffaɗan tiray, ya nufi saman dashi

Yana shiga ɗakin yanufi wajen ta, sai da ya’ajiye tiray ɗin a saman drowan gadon kafin ya zauna, yasaka hannu yaɗago ta yana faɗin “Baby tashi kici abinci kisha magani”.

Langaɓe kanta tayi tana son komawa, nan da nan hawaye suka cika idanun ta, cikin dashashshiyar muryan ta da baya fita sosai tace, “Yaya Sanyi”.

Suhaib duk ya ruɗe ya rasa yanda zai yi da ita, don tuni ta soma masa kuka, aza ta yayi ajikin sa yasoma rarrashin ta cike da tausayin ta, sai da yaga ta nutsu ta dena kukan sannan yamiƙe yashiga Toilet ya ɗauko mata Brush, shi ya taimaka mata ta wanke bakin ta yaje yazubar da ruwan a Toilet, sannan yadawo yamaida ita jikin sa, a haka yayi ta bata abincin tana ci, sai da ta ture hannun sa kafin yabar ta, sannan ya bata drugs ɗin ta tasha, be barta ta kwanta ba duk da kuwa tana ta mishi ƙorafi da shagwaɓan da tasaba yi, sai da ya tabbatar abincin ya narke ajikin ta kafin ya kwantar da ita yana faɗin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button