RAUDHA Page 21 to 30

“Baby ko in haɗa miki ruwa kiyi wanka ne, zaki fi jindaɗin jikin ki ko?”
Girgiza masa kai tayi tana lumshe idanuwan ta, ita kaɗai tasan abinda take ji ajikin ta, tunda take bata taɓa jin irin wannan ciwon dake yawo can cikin jinin jikin ta ba, takamaime ma bata san ina ne ke mata ciwon ba, ko ina na jikin ta zafi take ji da radaɗi, ga kanta dake uban sara mata kamar zai rabe gida biyu, wasu zafafan hawaye ne suka soma sintiri a face ɗin ta, don ba ta da ƙarfin da zata iya yin kuka ma
Suhaib bawan Allah ya rasa inda zai saka kansa sabida tsantsan tausayin ƙanwar na sa, ya kai ya kawo haka yayi ta yi, sai daga baya ne dabara yafaɗo masa, ya ɗau bargo har guda biyu ya lulluɓe ta ganin yanda take rawan sanyi, heatern ɗakin ya ƙure mata ta yanda ko ina zai ɗau ɗumi, sannan ya dawo kusa da ita ya zauna yana shafa mata gashin kai, hannun sa ɗaya na cikin nata biyu ya ƙanƙame su, ahaka yayi ta lallaɓa ta har sai da yaga tayi barci tukun yasamu nutsuwar zuciya, numfashi ya sauke me ƙarfi kafin ya yatashi yafito tare da jawo mata ƙofa
Ester ya kira yace, “takula da ita zai je yadawo” sannan yafice agidan.
Barcin awa biyu tayi ta farka
Ester na gefen ta, ita ta taimaka mata da taga tana ƙoƙarin tashi
Ƙafafuwan ta kaɗai ta zuro ƙasa tana riƙe da kanta, bata tashi ba sai da tayi kamar mintuna biyar kafin taɗago kanta tana kallon Ester dake gaban ta a tsaye, ahankali cikin dishewar murya tace, “zan yi wanka”.
Ester bata ji me tace ba, sai da tamatso sosai kusa da ita tasake tambayan ta, sake maimaita mata tayi sannan ne taji ta, hannu tasaka tariƙo ta; ta taimaka mata zuwa Toilet ɗin sannan tafito.
Mintuna 20 ta ɗauka aciki kafin tafito ɗaure da towel ajikin ta, gashin kanta da suka manne ajikin ta sai zirarar da ruwa suke yi, ahankali take takawa har zuwa gaban dressing mirror tazauna
Dasauri Ester taƙariso wajen ta tana faɗin “let me help you Ma’am”.
Handrayer ta ɗauka bayan ta soka socket ɗin, tasoma busar mata da gashin kanta, bayan ta gama tasoma shafa mata Lotion a kyakykyawar white skin ɗin ta
RAUDHA bata hana ta ba, har sanda tagama shafe mata hannu da ƙafafu kafin tatsaida ita, miƙe wa tayi tanufi gaban Sip ɗin kayan ta
Ester na biye da ita, ita tabuɗe mata Sip ɗin
Ita kuma RAUDHA tanuna mata kayan da zata ciro mata
Akan gado tazube mata kayan sannan tafice.
Matsa wa gaban gadon RAUDHA tayi ta ɗauki kayan tasoma saka wa, riga da wando ne na sanyi masu tsananin taushi da kauri, kalan ruwan ƙasa, da Zip agaban rigan, Sannan ƙafan wandon da na hannayen Robber ne da ya kamata sosai, hula tasaka na kayan me tuntu a tsakiyan, gashin ta gaba ɗaya ta tusa acikin hulan tarufe har kunnen ta, sai da tasaka Socks kafin takwanta tana rufe jikinta da bargo, ba barci take ji ba but ta rufe idanun ta tayi luf akan gadon, har yanzu da sauran zazzaɓi ajikin ta, ga kuma sanyi da take ji can cikin ƙashin ta wanda gaba ɗaya ya hana ta jin daɗin rayuwan ta.
Ester CE tashigo tayi mata maganar “ko akawo mata abinci ne?”
Sai ta girgiza mata kai alamun “a’a”
Hakan yasa tafice tajawo mata ƙofan.
????????????????????????????????????
Sai gab da magriba aka sallamo su Farida, sai dai likitocin sun haɗa su da magungunan da zasu riƙa ba ma jaririn, sannan zasu riƙa kawo shi ana duba sa sau biyu a sati, har aga abun da hali zai yi kafin yasoma girma.
Maryam da wata Dattijuwar mata me suna Inna Haule, ƙanwa CE wajen mahaifin Farida, tare suka dawo gidan, tunda ita INNA Haule ita ce zata zauna da Faridan har tayi arba’in, ita kuma Maryam zuwa bayan isha’i Mijinta zai zo ya ɗauke ta.
Har a time ɗin RAUDHA na nan a kwance, duk tana jin ɗan hayaniyan su daga ɗakin ta, amma bata tashi ba bare tafito
Suhaib ne yashigo ɗakin, idanun sa akan ƙanwar nasa yaƙarisa wajen gadon yana zama, a tunanin sa barci take yi, don haka sai yaɗaura hannun sa saman goshin ta don yaji jikin nata
Buɗe idanuwan ta tayi tana kallon sa, ahankali tafurta “Ya..ya”.
“Baby kin tashi?”
“Uhmm”. Tace dashi tana ƙoƙarin tashi zaune
Dasauri yasaka hannayen sa ya taimaka mata tatashi zaune, jingina tayi da jikin sa taɗaura kanta saman kafaɗan sa, hannayen ta saƙale a ƙugun sa tasake lumshe idanun ta
Yayinda shi kuma yake shafa mata gashin kanta, yana jin yanda zafin jikin ta ke shiga jikin sa, hakan yasa zuciyan sa sake jin tausayin ta fiye da ko yaushe
“Baby”.
“Umm..”
“Ko mu koma Hospital ɗin ne?”
Girgiza masa kai tayi tana ƙara lafewa ajikin sa
Numfashi kawai yaja yana ranƙwafo da fuskar sa, ya sumbaci gashin kanta kafin ya zame jikin sa yana faɗa mata yana zuwa
Fita yayi, babu jimawa yadawo tare da tiren abinci, shi da kansa yaciyar da ita, sannan ya faɗa mata “Farida ta dawo, ko zasu je taga Baby?”
Gyaɗa masa kai tayi alamun zata je
Shi da kansa ya ɗaga ta, hannun sa na riƙe da nata ta jingina da jikin sa suka fito.
Ɗakin Faridan suka shiga, Suhaib ne kaɗai yayi sallama
Maryam dake zaune riƙe da Babyn ta’amsa mishi idanun ta akan RAUDHA
Zama akan stool ɗin mirror yayi, yayinda RAUDHA ke manne dashi taƙi ta sake shi
Cikin fara’a Maryam tace, “Ƙanwata ya jikin naki?”
Ɗan kallon ta RAUDHA tayi tana son tabbatar wa da itan take yi, ganin tana kallon ta sai ta’amsa mata a hankali
“To Allah ya sawaƙe, Allah kuma ya kiyaye gaba”.
Wannan karon Suhaib ya amsa mata yana tambayan ta “ina INNA Haule?”
Maryam ta sanar masa ta fita zuwa kichen ɗaura ruwan wankan me gejo, kafin ta ƙara da faɗin “to Nima dai yanzu zan tafi tunda Baban Aliyu ya zo, gashi har yanzu Aunty Farida bata tashi ba, idan ta tashi Yaya sai ka sanar mata Ni na tafi”.
Zuwa tayi ta miƙa masa jaririn, kafin ta ɗau jakan ta suka sake sallama tafice
Kichen ta nufa tayi wa INNA Haule itama sallama, sannan ta tafi.
[2/22, 10:55 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????????: ✍️
???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓
???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️
????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????
????.????.????????/
.
???????????? ???????????????????????? ___________________________????
???????????????????????? ???????????????????????? ????????????
_______???? “Baby kin ga me sunan Daddy? Yana kama dake ko?”
RAUDHA da ta ƙura wa jaririn idanu ko ƙifta wa ba ta yi, ko taɓa sa ta kasa yi illa gyaɗa wa Yayan nata kai da tayi
Murmushi yayi don ya san halin ta akwai tsoron ƙananan yara, don ya tsokane ta yace, “ki ɗauke sa mana kar yayi fushi dake”.
Maƙe kafaɗa tayi
“Baby Daddy ne fa, ko ba kya son sa?”
Har yanzu idanun nata akan jaririn yake taƙi dena kallon sa, cikin muryan ta da baya fita ko kaɗan tace, “yaya ka bari sai ya sake girma zan na riƙa ɗaukan sa”.
Dariya kawai Suhaib yayi, yana sake rungume yaron nasa tare da sumbatar sa.