YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Zasu rabaki dashi ko dai zaki raba kanki dashi,,Dan wannan halin kadai ya isa yasa mashkur dena kulaki tinda kin Nuna keba me hankali bace…

Turo Baki Yasmeen tayi tana kallan abba tace,,abba kaga mama ko…

Tsakin mama taja ta dauka basket din ta tana kallan abba,,nizan wuce asibiti Naga Rana tayi..

Wallahi babu inda zakije indai nine gaba dake kuma ni nake Baki umarni” akan me zaki dauki abincin gidana ki kaiwa wancan yarinyar,,

Yarinyar data Zama silar kuka da baqin cikin ‘yar Lele…

Amma abba Yasmeen” Amma me? kinga banasan Jin komai daga gareki kifita kawai kibani guri…

Rawa Yasmeen tayi tana cewa yau abbana,,Dama Kai kadai kake Sona nasan mama.

Hararan da mama take matane ya hanata qarasa fadar abinda tayi niyya..

Fita daga dakinan kafin yanzu jikinki ya gayamiki, da kuka Yasmeen ta fita tana qunquni….

Comment & share

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*…..*

4⃣8⃣&4⃣9⃣

Yasmeen na fita abba ya maida hankalinsa kan mama”ransa a bace yake kallanta,,kauda fuska mama tayi tana mejin haushin hanata zuwa hospital dubiyan nijlah..

A gefenshi ta zauna tana magana a hankali” yanzu abban Yasmeen kana ganin rayuwar daka Dora Yasmeen ita ta dace da ita?

Nasan kana da ilimi na boko Dana addiniya Ka kuma San amanarta Allah yabamu,,be kamata mu zuba Mata Ido tana Abu Yadda takeso ba”Dan Allah kayi tinina Ka kuma tinani ‘ya’ya da dukiya amanar Allah ce,,ze tambayemu akansu ranar da gata ko dukiya bazasu mana amfanin komai ba…

Ajiyar zuciya abba ya safke Yana kallan mama” kafin ya iya bude baki yace”

Yanzu ya kikeso nayi?

Sokike na fifita ‘yar wasu akan tawa?

Ba haka nake nufiba sedai inaso kagane Yasmeen tayi laifi Ka kuma hukuntata akan abinda ta aikata..

Cike da zafi abba yace” haba hajiya yanzu duk irin hukuncin da kikayimata be ISA haka ba,,to to to yanzu na gane hausarki,,sabida ke bakisan zafin Zama da kishiyaba shiyasa kike gayar irin wannan maganar,,to wallahi Bari ingayamiki,,daga yanzu ko kallan banza kika qara yimata akan wannan maganar Saina Saba Miki,,Wanda batasan ciwan nata ba,,mtssss abba Yaja tsaki Yana fita a dakin..

Harya fita ya juyo Yana cewa” ban kuma yarda ki qara zuwa hospital ba,,idan ma mutuwa tayi ita da iyayenta sukayi asara Bani ba..

Bakin cikine ya Hana mama magana har abba ya Kada Mata kura ya fita” Yana fita tasa hannu biyu ta zuba tagumi tana girgiza Kai…

Yasmeen ce ta shigo ta zauna jikin mama tana shafa fuskan mama”

Sweet mamana,,waya tabamana ke?

Murmushi mama tayi tana shafa Kan Yasmeen tare da janyota zuwa jikinta tana qare Mata kallo,,zuwa wani lokaci ta bude baki da kyar tana Mata magana cikin nasiha dajan hankali..

Yasmeen yakamat kisan kin girma kidena daukomana magana” kodan kinga mahaifinki be damu da abinda kikeba,,saima goyamiki Baya yake” 

Bata jira amsartaba ta cigaba da magana”

Yakamat ace kingane abinda kika aikata ba daidai bane,,kiduba girmanki da shekarunki ki kuma duba na yarinyar da kika buga.

Kinsani ko baa gayamiki ba nijlah ba sa’arki bace,,ko kina tunanin mashkur ze aureki da haka??

Turo Baki Yasmeen tayi tana cewa to Amma ita tasan yarinyace ta auremin miji.

Mijinki ko mijinta Yasmeen kokin manta yanzu nijlah matar mashkur ce,,ko kuwa fa har yanzu kina matsayin budurwanshi a yanzu yace yafasa shikenan aurenki ya fasu kinga shikenan sai abbanki yaje kasuwa ya siyomiki miji kama mashkur ko?? Mama ta qare maganar ta sigar tambaya…

Shiru Yasmeen tayi zuciyarta na halbawa da sauri dasauri,lokaci daya jikinta ya dauki rawa,,babu abinda take hangowa sai tashin hankali game da rabuwanta da mashkur,,bakinta na rawa tace”

Yanzu mashkur sai yace yafasa aurena?

Sosai ma,,tinda kin Nuna bazaki zauna da matarsa lafiya ba.

Mama Shifa ba Santa yake ba.

Ummmm Yasmeen kenan, haryanzu ke yarinyace kina tinanin namiji ze zauna da mace alhalin Baya santa?

Shiru Yasmeen tayi tana zubda hawaye tana kallan mama sai kuma ta rungume mama tana cewa”

Dan Allah mama ki bashi hakuri bazan qara dukantaba kinga tin dare nake Kiran wayarshi yaqi amsani..

Ya zaayi ya amsaki kodan bake akama wannan dukan ba?

Cikin kuka Yasmeen tace Allah mama nadena ni haushina daya danaga yarinya nada mugun kyau,,wallahi mama duk kyau nijlah ta Fini kyau wannan dalili yasani bugunta..

Dariya mama tayi tana kallan Yasmeen tace” kaji shirmen naki ba,,waya gayamiki yanzu kyau Yana tasiri gurin Maza?

Cike da shagwaba Yasmeen tace toba Naga yanzu kowa man saka fari yake shafawa..

Badai kowa ba kuma a yanzu duk namijin dayasan kanshi Baya zaben kyau,, kyankyawar tarbiyya Ake Zabe gashi ke kin Nuna Baki da ita..

Bakin Yasmeen a gaba tace toba nadena ba” Allah yasa cewar mama.

Yanzu saiki tura masa text message ki bashi hakuri, nasan ze karanta.

To Yasmeen tace ta tashi tana murna Dan ita ta manta da wani text massage”

Zazzafan sako Yasmeen ta tsara tare da turama mashkur.

Zaune yake ya dawo daga restaurant Yana qoqarin hadama nijlah abinci yaji qaran zuwan sako cikin wayarsa..

Be duba ba ya cigaba da abinda yake,,Saida ya Gama hada Mata tea ya dauko ya dawo kusa da ita Yana miqa mata…

Nina koshi nijlah tafada cikin shagwaba”

Amsa kisha banasan musu” 

To tace ta amsa tana sha badan taso ba,,ki dauka wannan abincin Shima ki cinye inba so kike likita yaqi bamu sallama ba..

Batayi magana ba tafara cin abinci tana ci tana yinqurin amai Shi kuma Yana shafa bayanta ahaka harya Samu taci da yawa.

Gefe ya koma Yana qare Mata kallo tare da tinanin ta inda ze dauki matakin daya dace Kan Yasmeen..

Wayarsace tafara ruru nan yasa hannu a hankali yayi picking wayar ta hanyar kaita kunne Hade da sallama..

Daga daya bangaren mummy ta amsa da kyar tace” Auta kana da hankali kuwa,,ko kanaso kace jinyar matarka yafi zuwa Ka gaisheni??

Bakinsa na rawa yace’ kiyi hakuri mummy anjima Zan zo idan ta fito babu Wanda ze zauna da ita,,mummy nijlah na buqatar kulawa sos….

Bata Bari yaqarasa ba tace” rufemin Baki kafin na bigemaka Shi ta cikin wayan” kazo Ka sameni yanzu base anjima ba inasan ganinka,,Ko ita ta haifamin kai dazata riqeka yarinyar da Ko haqqinka bazata Iya saukewa ba Amma kake rawar kai akanta..

Shiru mashkur yayi be qara Magana ba Har Saida mummy ta gama yafara Bata hakuri”mummy kiyi hakuri insha Allahu yanzu Zan zo”kadama kazo auta kadai zauna kana jinyar banza Naga ita tafi karbanka Akan kazo muyi shirye shiryen bikinka…

To kawai yace yana sauraran mummy tagama fada ta katse wayar’ tinda yafara waya nijlah ta kafeshi da Ido tana sauraran abinda yake fada’ Ko Bata tambayaba tasan fada akemasa Wanda Waze wuci akanta Ake abin ba,,Yana gama wayar Shima ya zuba Mata Ido tare da cewa’ Ke Kuma wannan kallan fa?

Dauke Kanta nijlah tayi tana mejin tausan halin da tasashi ciki,,haka nan Taji tanasan ganin kaka,,koba komai Zata rungumeta a jikinta ta rarrasheta yanzu ki bata dame yimata haka sai Wanda Zena mulmula Mata nono Wanda ta dauka hakan a matsayin wahalarwa da hukunci me tsaurin gaske..

Ganin Yadda ta zurfafa cikin tinani yasa mashkur qarasawa kusa da ita Yana cewa” amarya tinanin me amaryana take?

Boye fuska nijlah tayi taqi dagowa,,duk yadda yayi nasan ganin fuskanta taqi yadda yamata wasan harya gaji ahaka wani sakon ya sake shigowa cikin wayarsa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button