YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Mummy kinga abinda nake gayamiki ko,,ninasan baze dauka wayana ba,, ahankali mummy tace ki qara Kira mu gani..

Number aunty Lateefah ta qara dealing akaro na barkatai.

na cikin yimata addua yaji waya Na ringing,,hannu yakai ze amsa taqi bashi tana kuka tana girgiza masa Mai..

Kibani nace,,ko bakiji ana kirana ba,,cikin kuka nijlah tace wallahi ban zagetaba,,ai Bata Ida Magana ba yayi saurin fizge wayar a hannunta..

Hello aunty lateefah,,ba wani aunty lateefah dazaka kirani ka kirani sa lateefah Kawai mara mutunchi,,kana kallo matarka ta zage mana uwa amma kai ko ajikinka baccinkama kake ko mashkur..

Kallan Nijlah yayi da tinda ya amsa wayar ta Tashi da gudu tayi bakin kofa hannunta biyu aka tana kuka..

Tokazo yanzun nan mummy tanasan Magana dakai,,bakinsa na rawa yace gani nan gani nan..

Yana gamawa ya Tashi a fusace yayi kan nijlah,,ai kafin ya qarasa inda take harta zube a qasa tana birgima tana bashi hakuri..

Dan Allah kayi hakuri Handi mu bani,,bazan qaraba Na tuba Dan Allah kada ka dakeni kukan da nijlah ta riqayi Kenan tana ihu..

Hannu biyu ya sarqe a qirjinsa Yana binta da kallo,, yama rasa hukuncin daze yanke akanta,,dukanta zeyi kome,,to idan ma Na daketa ba hucewa zanyi ba,,inaga amfanin dukan..

Karka daketa wata zuciyar ta fada masa kayi mata nasiha shine abinda ze shirya maka nijlah Dan da gani Bata Jin Magana..

Bebi ta kantaba ya fada toilet,,wanka yayi ya fito Yana kallanta a inda ya Barta Sai birgima take kai kace dukanta yayi..

Wardrobe ya bude ya dauko faran shadda,,cikin mintina kadan ya shirya,,wayarsa ya dauka yayi hanyar fita,,da gudu nijlah ta Tashi zata fita ya daka Mata tsawa..

Ke wallahi ki kiyayeni koni sa’ankine,,Bayan aikin kashin dakika sani saikin sakamin da wani tashin hankali ko nijlah,,ina hankalinki da wayanki suke,,to wallahi ki fita a idona..

Safke kai qasa nijlah tayi tana bashi hakuri harya gama ya fita ya Kuma kulleta ta baya..

Cikin sauri ya dauka Mota ya tafi,, restaurant ya shiga ya siyo Mata wainar shinkafa da miya ko noma be bari ansaba ya hadamata da kunun Madara me sanyi..

Dasauri ya koma gidan ya bude dakin da take ya ajiyemata kayan abincin,,gashinan ki Tashi kici kafin naje wani guri yanzu Zan dawo,,idan Kuma naji abinda kika aikata ba daidaiba saina Saba Miki..

Daga haka ya fito sedai wannan Karan be rufe ta a dakin ba,,Yana zuwa bakin get ya Kalla baba Mai gadi yace..

Baba ka tsaya akan aikinka akwai yarinya ciki,,Dan Allah karka bari ta fita,,idan Kuma ka bari wani abu ya sameta nida kaine..

to ranka ya dade cewar get man Yana gyara Zaman hularsa..

Tinda mashkur ya fito gabansa me cigaba da faduwa ahaka har ya iso gida..

A fAlo ya Sami mummy zaune ta hada kai da gwaiwa,,kusa da ita mashkur ya zaune Yana hada hannunsa..

Pls sweet mom Dan Allah kidena irin wannan tinanin,,ki dauka qaddaran da Allah ya dorawa danki,,mummy kinsani banida burun auren wata Diya mace Bayan Yasmeen,, wannan aure daga Allah yake..

Kai rufemin baki,,kana so ka gayamin Shima zagin da kabata waya tayimin daga Allah ne??

Mummy zagi kuma?

Au tambaya kake,, mummy kinji shiko,,wai mu zeyiwa barikanchi,,ki rabu dashi lateefah ni wallahi gani nake kama chanzamin Shi sukayi..

Fuskar mashkur mummy ta riqa shafawa wai a tinaninta wanine suka samishi fuskar mashkur,,Babu abinda ta Ciro Dan haka tasa kuka tana cewa shine,,wallahi shine lateefah..

Dakyar mashkur ya iya hadiye saliva bakinshi,,muryanshi Na rawa yace,,pls aunty lateefah karki hadani da mummy,,kema kinsani bazan taba Bada waya a zagi mummy naba..

Kuma nijlah Bata iya zagiba,,tana da tarbiyya,,tassss tassss lateefah ta dauke mashkur da Mari tana nunashi da yatsa..

Kana nufin Karya mummy tayiwa nijlah kome,,

Tafe kunchinsa mashkur yayi ya kasa magana,lokaci guda hawaye suka wanke masa fuska..

Ita kanta mummy taji Marin sedai bazata iya hanawa ba sabida komai akayi Dan ita ake masa..

Yanzu ina ita nijlah take,,mummy ta tambaya a hankali..

Yana hawaye yace,,tana gida,,wanne gidan qin Bata amsa yayi sabida Yana tsaran kada suje su daketa danyaga alamar Hakan,,tinda Shima Basu barshi ba..

Wai ba tambayarka bakeba ba auta??

Mummy tana gidan abokina ya tsinchi kansa da yimata Karya..

Toka tafi yanzu yanzu inasan Magana daku gaba daya,,kaga gobe auntynka zata bar qasar,,yayanku Shi ya tafi tin safe..

To yace ya Tashi Yana tafiya Yana hada hanya..

Seda yayi hanyar saban gida yaji qaran wayarsa..

Zuciyarsa Na tafasa ya duba number me Kiran,,abban Yasmeen ne..

Nan ya samu guri yayi parking kafin ya daga wayar zuciyarsa na cigaba da halbawa Dan idan akwai abinda ya tsana be wuci a rabashi da Yasmeen ba..

Yana dauka abban yace,, mashkur kana lafiya,,bakinsa Narawa yace lafiya qlau Abba..

Kafin mashkur yaqara Magana Abba yace..

Naji duk abinda yafaru sedai hakan dakayi ya nuna mana kai ka hakura sa auren Yasmeen,,Dan haka nakeso kazo yanzu gidana inasan Magana dakai,,idan an gama komai saika amsa kudinka ka tafi,,nafasa baka Yasmeen..

Wayyo kukane kawai mashkur beba Shima saida yayi na zuci,,ga wani irin faduwa da gabansa yake jiyake kama zuciyarsa zata tsage biyu tabar gangan jikinsa..

Abba dan Allah kayi hakuri bazan iya rabuwa da Yasmeen ba,,ta zama ni nazama ita wallahi Abba badaga ni bane,,haka Allah ya qaddara,,Abba zan riqe Yasmeen amana,,Abba na tabbata babu abinda ze sameta indai tana tare Dani…

Dakata haka mashkur kaida Yasmeen kunyi hannun riga,,niba wannan bayanin na tambayekaba,,kazo nan da minti 5 kafin na fita..

Abba be ajiye wayan ba Yasmeen ta riqe qafafunsa tana kuka,,Abba inasan shi,,bazan iya rayuwa babu shiba,,Abba Dan Allah ka chanza wannan hukuncin yayi masa tsauri…

Murmushi mama tayi tana kallan Yasmeen sedai bata iya magana ba ta tashi tabarsu a falon…

*Kwana biyu kunjini shiru,,kada ku dauka Jan ajiyene,,hakan yafaru sakamakon samun matsalar wayana,,Wanda har yanzu bata gama zama daidai ba*..

Yawan comment yawan typing.

*Momn sultan ce*

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*WASILA….*

3⃣3⃣&3⃣4⃣

Mama na shiga daki ta zauna saman bed tana murmushi..

Da gudu Yasmeen ta shigo ta fada kan mama tana kuka..

Mama dan Allah kigaya Abba kada yafasa aurena,, wallahi mama inasanshi,,zamu shiga wani hali idan har bama tare..

Cike da takaici mama take kallanta sai kuma ta ture ta tana cewa,,ke dai anyi sakarya,mara wayo keda nake gayamiki gaskiya kina toshe kunne,,sai yanzu da kika gama harzuqa abban Baki shine Zaki kawomin Kara,,toki tashi kibani guri ban iyawa..

Kije gurinsa kusan yadda zakuyi,,naga dai kunfi kusa..

Cikin kuka Yasmeen tace Allah mama Abba yadauka zafi akan mashkur kuma ba haka yakamata yayi ba..

To ai saiki gayamasa yadda zeyi kafin mashkur yazo labari yasha babban,tinda yagayamiki baze iya sakin matarsa ba.

Ni Allah seya saketa tinda ba itace zabinshi ba,to ai shikenan ga gurinann daga haka mama ta fita a dakin tabar yasmeen..

Daki Abba ya shiga yana zagaye dakin tare da cije labe,,waini zaa wulaqantawa yarinya,, yarinyar da tintini samari ‘ya ‘yan manya ke bibiyar aurenta Amma taqi ta nacewa wannan yaran,,gashi yanzu abinda ya sakamana dashi,,sosai Abba ya shiga cikin tinani har besan lokacin da Yasmeen ta shigo dakin ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button