YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Kallan abincin yayi yace ba inda zamuje saikin cinye,,ba musu tajashi gabanta ta fada ci,,bata dagoba Saida ta cinye ta dago tana kallansa..

Lakuce Mata Kai yayi Yana cewa yauwa yarinyar kirki aka nakeso ki riqa Jin magana idan kinaji kin hutan da kanki hukuncina..

To tace ta tashi ta dauka mayafinta..

Kinyi wanka ya tambayeta?

Bakinta na rawa tace ai ban iyaba..

Kina nufin a haka zamu tafi,,eh tace tana saa takalmi”

Dan Allah kazo muje idan naje can zanyi..

Hannunta ya kama yace inaso idan daddy ya tambayeki zaki zauna a gurin mummy ko a gurina kice a wajena zaki zauna kinji amaryata,,bazan qara yimiki hukunci ba kinji..

Daga masa Kai tayi danta qagu su fita,,tasani hankalinta saiyafi kwanciya..

Car keys dinsa ya dauka ya gyara Mata rigar jikinta tare da riqe hannunta suka fara tafiya..

Daya kofar ya budemata ta Shiga yayinda Shima ya zagaya daya kofan ya Shiga nan ya kunna motan suka dauka hanyar gidan mummy…

Minti 30 ya kaisu gidan Dan suna da nisa tsakanin saban gida da nan,,Yana zuwa ya fito Yana jiran ta fito yaji Shiru,,tinawa yayi bata iyaba Dan haka yaje ya bude Mata Yana cewa,,

Idan ma zaki koya bude mota ki koya Danni ba driver bane..

Aunty lateefah dake Sama taji tsayuwar motarsa ta leqo ta window taga duk abinda yayi anan ta fara tafa hannu tana cewa mummy taso kiga abinda auntynki yake,,tin yanzu ya Zama bawan Mata wai wannan jaririyar ke juyashi har Yana bude Mata mota..

Bata Ida magana ba taga mashkur ya daga nijlah Sama ya dorata Saman wuyansa Yana cewa oya fara,,doki sukuta sukuta aka har suka qarasa shigowa falon…

Dasauri mummy da aunty lateefah suka sauko falon qasa Dan ganewa idansu…

Sunyi rashin sa’a kafin su qaraso har mashkur ya safke nijlah Yana murmushi tare da cewa idan har kinyi abinda nace Zan riqa goyaki acan ina Baki wannan abun me sanyi,,ice cream kenan..

Dariya nijlah tayi da kumburanran bakinta tace Allah kado,,Allah kuwa yace Yana Nuna Mata Kan kujera,,kinga zauna anan kafin mummy tazo,,dakinga tazo ki…….

Uwarka zatayimin yaji mummy ta fada tana Nuna nijlah da yatsa,,idan ba mantawa yayina tinda yake mummy bata taba zaginshiba sai yau Dan haka yayi qasa da Kai yasan abin babbane ba qarami ba..

Zauna anan mara Jin magana banace Ka saketa ta koma garinsuba ninace zanyi duk abinda ya dace,,Zan Gina musu gida zanba Yan uwanta kudin da harsu mutu bazasu iya kashesuba,,tinda nasan fulani Basu iya cin me dadi daga kosai sai buredi..

Ahankali yace mummy kiyi hakuri Dan Allah kidena irin wannan maganganun sabida gaba,,bamusan matakin dazata takaba…

Salati latifa ta saki tana cewa shikenan sun hargitsamin kwakwalwar Dan uwa.

Haba aunty lateefah kefa babbace” 

Ah ah Nina haifi duniya mara kunyar banza kawai.

Banza ya Mata ya Shiga ba mummy hakuri tare da yimata wa’azi..

   shikenan ai mummy tace, tinda Ka nace saika zauna da ita anan gidan Dan Baka isa Ka tafi da ita wani guri Ka Barni anan ba..

Kafin mashkur yayi magana daddy ya shigo falon Yana cewa,,idan ta zaba Zama anan din ba,,kinsan dai yakamata afara Basu Dama a matsayinsu na Mata da miji aji tsarinsu..

Cikin fishi mummy tace kajika da wani magana,,su din har wani tsari garesu..

Ita dai nijlah tinda ta shigo Ido ta zuba musu tana kallan bakin kowa,,ta kasa magana sabida tsoran hukunci.

Daddy ne ya kalleta yanasan tambayarta inda takesan Zama danshi bayasan zamanta a gurin mummy,,kafin yayi magana yaga lebenta kumbure sunyi jajir dasu…

Idansa ya safke kanta Yana kallan yanayinta kama Wanda tayi kuka,,tinani yayi kodai dukanta mashkur yayi Dan haka ya juya Yana kallan mashkur yace”

Auta meya faru da yarinyar mutane Naga bakinta a kumbure,,badai dukanta kayi ba..

Girjinsa yaji ya halba da sauri,,nan yaji dabara ta fado masa ya juya Yana kallan mummy Wanda ta tsareshi da Ido,,

Bakinsa na rawa yace uhmn Dama faduwa tayi da zamu Tah……

Kafin ya qarasa yaji muryar nijlah tana cewa,, lah lah lah,,malaminmu yace babu kyau karya..

Zare Mata Ido yayi mummy tayi saurin cewa kaga dena zare Mata Ido ta Fadi gaskiya,,nasan dukanta kayi kanaso ta tafi..

Dasauri nijlah tace ba dukana yayi ba,,Dama Dama bakina da nasa ya hada Yana……..

Sabida firgice da kunya gami da tashin hankali mashkur yayi saurin bige Mata Baki..

Tafi aunty lateefah tafara tana kallan mummy..

Daddy Kam kunyace ta kamashi harya Rasa inda zesa kanshi…..

Yawan comments yawan typing,,kuyi hakuri da rashin amsa comments Baku,,damar hakan ne ban Samu ba,,idan kuka kuka dena Nima Zan dena typing Allah kunji harna rantse..

Pls share.

*Momn sultan ce ✍✍✍*

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*SIS NAJA’ART…..*

3⃣7⃣&3⃣8⃣

Kasa magana daddy yayi Dan baze iya ba daidai wannan lokacin Dan haka ya shige dakinsa Yana murmushi batare da kowa ya Ganshi ba..

Mummy ce tayi qarfin halin cewa,,Kai mashkur Ka Bani amsa mana,,kayi Shiru kana kallona..

Dakyar ya iya bude baki yace” mummy nafa gayamiki faduwa tayi..

Karya kake wallahi idan zaka Fadi gaskiya Ka fada cewar aunty lateefah..

Kinga lateefah rabu dashi,,ke Dan ubanki zonan,mummy ta fada tana kallan nijlah”

Qin zuwa tayi ta zuba mashkur ido,,shiko ya dalla Mata harara tare da yimata kallan Zan kamaki.

Wai ba magana nake Miki ba kin tsareni da Ido,,shegiya mayya me kikaiwa Dana” kunyace takama mashkur Dan haka ya kauda Kai Yana cewa..

Haba mummy me wannan yarinyar zatayimin..

Ka rufemin baki,, ninasan ba lafiya garekaba mashkur,,yo inba mara lafiya ba yama zaka hada Baki da wannan tafada tana Nuna nijlah..

Fakar idan mummy nijlah tayi ta Dan murguda Mata baki,, sedai aduk abinda take akan idon mashkur,,nan yaqara kulewa tare da daukan alwashin koya mata hankali aduk lokacin data sake suka kebe guri daya..

Wai Baka jina?

Cike da kunya yace,,mummy kema kinsan ba haka bane..

To yayane Ubana,,Naga dai a gabanka ta fada..

Hannu mummy tasa ta janyo nijlah tare da zuba Mata rankwashi” tace wai tambayarki nake ba..

Ki Bani amsa mana kinyi Shiru kema kina kallona” cike da tsoro nijlah tafara magana bakinta na rawa” ummmm ummmm dama..

Mashkur yayi saurin bige Mata Baki ta hanyar hanata magana da Ido tare da qif qif ta Mata su….

Yiwa mutane Shiru ko Kai Dana tambayeka Ka Bani amsa,,da zaka hanata magana..

Ina jinki mummy ta fada tana kallan nijlah,,,Dama me??

Bude baki nijlah tayi tana San yin bayani mashkur yace”

Yiwa mutane Shiru”

Bakin nijlah gaba tace” toba tambayana kayiba,,kuma Naga bakace Karna gayaba idan an tambaya cewa kayi nace banasan Zama a gid…

Be Bari ta qarasa ba ya saki tari me rikitarwa,,shiru nijlah tayi tana cewa” sannu kado,,mummy ko haushi ya isheta ganin Yadda suka sata a gaba suna jamata Rai.

Seda nijlah taga mashkur yayi Shiru ya dena tarin tace to mummy in Gaya???

Eh gayamin..

Dama shine ya..

Mashkur yayi saurin katseta”

Wallahi idan naji kin qara cewa uffan anan sai nayi maganinki..

Kama bakinta nijlah tayi tana bashi hakuri” fita anan kafin Saba Miki shashasha mara wayo kawai..

Da gudu nijlah ta fita waje ta zauna tana karkarwa sabida tsabar firgitatan da yayi..

Tana fita mashkur yayi Shiru tare da miqewa tsaye,,zuciyarsa na bugawa da qarfin gaske sabida tsabar bacin Rai,,nan take gumi ya Shiga karyo masa ta ko ina a jikinsa,, iskar ya furzar cike da Jin kunyar mummy yafara satar kallanta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button