YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Qin Magana Yasmeen tayi sabida batajin zata Iya furta Koda Kalma dayane sabida bakin Kishin dake Cin zuciyarta,,jitake inama ta Mutu kota Dena Jin abinda takeji a jikin zuciyarta..

Ganin tayi Shiru taqi Magana yasa mama Tashi tsaye tana cewa to Ina Shi mashkur din yake?

Ni ‘yan nan inazansa kaina,,ya Allah ka kawomin dauki” Ke Yasmeen kodai kurma Kika Zama mama ta fada tana kai Mata Duk..

Yasmeen ki Duba jikinki yadda Duk ya baci da jini indai wannan jinin mutum ne to Babu shakka hadari kuka Samu,,da yaushe kuka fita a gidannan baki gayamin ba,,Ina kukaje?

Duk tambayoyin da mama tayi babu Wanda ta Samu amsa,,ita kadai tayi burarinta ta gama,, ganin datayi Yasmeen taqi kulata yasata sakin kuka tare da fitowa waje da gudu tana cewa..

Me Gadi wakaga ya ajiye Yasmeen?

Cikin tashin hankali hankali baba me Gadi yace’ hajiya Ai Yasmeen ce ta kashe wata yarinya da wannan alhajin mashkur yazo da ita,,Nima ina nan inajin radio banji abun ba Sai Daga Baya..

Cike da matsanancin tashin hankali da fargaba mama ta dafe qirji tana cewa” kisa fa kace Malam Audu?

Kwarai kuwa Dan gaskiya yarinya ta Mutu sabida Nida kaina nadubata Kuma kinsan ninake sallar gawa a garinmu kafin Na Samu wannan aiki..

Mama taba idajiba ta Koma ciki da gudu ta dauka waya ta Kira Abba”

Tana kuka tace” Alhaji kayi sauri kazo gida ba lafiya”

What!!! 

Hajiya Karki gayamin Wani Abu ya faru da ‘yar Lele,,Dan Allah ba yadda zanyiba,,kowaye ya tabata Sai inda qarfina ya qare..

Mama batasan lokacin data saki tsaki ba,tana cewa”

To ai shikenan yanzu saika zo kaga abinda kudi da shagwabawa game da sanka suka jama”

Murmushi Abba yayi Yana cewa kedai kullum bakida abokin Kishi Sama da Yasmeen,,yanzu fisabilillahi Idan ban shagwaba lelena ba wazan shagwaba,,da Allah kidena yimin irin haka..

Hawaye masu zafi mama ta goge tana cewa” to ai gashinan abinda gata Yaja Mata” ta kashe “Yar mutane..

Cikin firgice Abba yace” ehhhh hajiya kinko San abinda kike fada,,kisa fa kikace”

A hasale mama tace eh,,abinda Kaji Shi nake fada,,Dan haka yanzu ka dawo gida musan halin da yarinya take ciki,,tana gama fada ta katse Kiran tana zagaye faloon…

Zuwa yanzu ita Kanta Yasmeen hankalinta yatara Tashi Amma Idan ta Tinan ta rabu da damuwanta Sai Taji hankalinta ya kwanta,,Babu abinda Ke Daga Mata hankali illah kukan mama data zauna Kan kujera tanayi tana salati tare da neman dauki gurin Allah.

Ahankali Yasmeen ta matso kusa da mama tana cewa,,pls mama kidena zubda hawayenki Akan wannan banzar,,hawayenki yadena zuba Akan ‘yar sadaka mara Gata..

Tasss tasss tasss mama ta dauke Yasmeen da Mari tana nunata da yatsa’

Yasmeen Karki Bari bakina ya fadi mummunar Kalma akanki” Kuda kuke da kudin ki Kuka ba kanku” to wallah ki Sani Idan Har wannan yarinya ta Mutu Bazan Bari ki zauna a gida kinajin dadiba,,wallahi kema Sai an daureki,,shashasha kawai..

Bani wayarki,,hannun Yasmeen na rawa taba mama wayar’ Cilla Mata wayar mama tayi tana cewa” ubankine Ze budemin day Zaki Bani ita ahaka,,wallahi kikayi wasa kema Saina lakada Miki Dukan mutuwa kinga Sai ayi biyu…

Hannun Yasmeen Na rawa ta dauka wayan ta cire password ta miqa mama”

Number mashkur mama ta Duba ta danne Kiran..

Mashkur dake kwance jikin daddy Yana kuka yaji wayarsa Na ringin kasa dauka yayi Sai daddyne ya amsa Kiran..

Assalamu alaikum,, daddy ya amsa yanasan sanin wacece,,Dan ba Suna yagani jiki ba,,

Bakin mama Na rawa tace,,nice mahaifiyar Yasmeen” Dan Allah a wanne asibiti kuke?

Seda daddy ya rintse Ido kafin yace,, muna standard hospital,,dan Allah yame jikin,,mama ta tambaya cike da Kunya..

Zuwa yanzu bamusan halin datake ciki ba,,dazu Dai harsun fito da ita Sai kuma aka Koma ciki,,Suna qara Duba lafiyanta..

Wani irin dadi mama Taji Dan harga Allah Idan nijlah ta rasu batasan inda zata sa kantaba..

Bata saurari Yasmeen Ko Abba ba ta dauka mayafi ta fita da saurin gaske Har tana hadawa da gudu..

Yau mama da Kanta tayi drive sabida tsabar zauri da yadda zuciyarta Ke azalzata.

Comments & share

*Momn sultan ce*✍✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*SHAFA’ATU UMAR…..*

4⃣3⃣&4⃣5⃣

Mama na fita Abba ya sanyo matarsa gidan Yana tuqi cikin kwanciyar hankali”

Guri me kyau yasamu yayi parking,,nan da nan ma’aikatan gidan suka zubewa Suna kwasar gaisuwa,,sedai yau uban gidan nasu be Iya amsasuba sabida saurin dayake ya Shiga ciki yaga ‘yar lelensa..

Cikin sauri ya Bude qofar falon,,bakinsa da sallama ya Shiga ciki Yana ‘yan Kalle kalle..

Gefe daya Daga cikin kujerun ya hango Yasmeen zaune ta Hada kai da qafa tana kuka a hankali.

Dasauri Abba ya qarasa inda take yana tambaya..

Ke Yar Lele waya tabamin Ke,, zonan ki gayamin kodan kin Daki wancan ‘yar masu yawan jejen kike kuka”

Girgiza kai Yasmeen tayi tana fadawa jikin Abba tare da sakin matsanancin kuka Wanda ita Kanta batasan kona Mene ba..

Hankalin Abba ba qaramin Tashi yayi ba,,nan ya Shiga jera Mata tambayoyi sedai Yasmeen ta gagara amsa Koda guda dayane..

Tashi Abba yayi ya Bude fridge” 

Ruwa me sanyi ya dauko tare da cup ya zuba ruwan ciki” Da kansa ya Shiga Bata Yana shafa Kanta..

Yasmeen Bata Wani sha dayawaba ta janye fuskanta tana turo baki..

Yaya Dai ‘yar Lele kigayamin kodai Wani ya tabamin Ke.

Cike da shagwaba Yasmeen

 Tace”

Ba mama bane hadda cewa zata dakeni” Kuma Shima mashkur tureni ya riqayi Yana min tsawa..

Hmmmm kinga abinda nake gayamiki Ko ‘yar Lele Amma Duk Da haka kin Nace kince Sai Shi Zaki aura,,Bayan Yana nuna banbanci tsakaninki da ‘yar sadaka.

Cike da sangarta da shagwaba Yasmeen tace” Ni Ni fa Nina sanshi,,Kuma nasan daya aureni Ze hakura da ita..

To ai shikenan ita Kuma mama ki barni da ita,,tana ma Ina banji duriyartaba tinda Na shigo?

Abba naji ta Kira mashkur Daga nan ta fita,,inaga asibiti taje Duba wannan shegiyar..

Jinjina kai Abba yayi Yana cewa’ kinga Tashi kije kiyi wannan ki cire wannan kayan da suka baci da jini Ko baki gani ba”

Sai yanzu Yasmeen taga jinin dake jikinta.

Cike da kyankyami ta Tashi tana tafiya kama batasan taka qasa ta Shiga dakinta..

Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta Hada ruwa me dumi ta fada cikin bahun wankan tana ninqaya a ciki” ta jima tana wanke jikinta kafin ta fito,,Bayan tashafe jikinta da Mai tare da turaruka masu kamshi ta Bude wardrobe,,dugawar rigar ta dauka Na material green colour me tsarin orange..

Bayan ta gama shiryawa ta dauka waya ta Hau Kan bed ta fara karanta Daga cikin littattafan momn sultan..

Ahankali mama take tuqi gabanta Na tsanan ta faduwa,,ahaka harta kai hospital,,tana zuwa ta Kira mashkur daddy yasake dauka..

Na qaraso abinda mama tace cikin sanyin murya da kunya’

Nan daddy yayi Mata kwatancen inda suke..

Bata Wani sha wahala ba ta ISA inda suke tana kallan mashkur dake kwance a cinyar daddy,,Har yanzu bai Dena kuka sedai zuwa yanzu ya rage kukan Sai ajiyar zuciya yake safkewa Akai Akai..

Kasa Magana mama tayi ta nemi gefensu ta tsaya tare da rungume hannunta a qirji tana addu’a”

Har wurin karfe 4 na yamma likitoci Basu fito ba,,ganin haka yasa daddy daukan waya ya Kira mummy Yana San sanar da ita..

Mummy na Daki zaune Kan bed yayinda lateefah Ke dauke Kan carpet tana shirya kayanta cikin akwati Dan gobe da sassafe jirginsu Ze Tashi,,mummy Taji wayarta Na ringin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button