YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

Mummy daddyne Dan Allah Idan kin dauka kibashi hakuri kigayamasa gobe da safe Zan tafi,,nasan Idan yadawo ya ganni Allah fada zeyimun..

Keni da Allah Bani waya kada ya tsinke,,mummy Na Daga wayan daddy yace,,hajiya Bazan Samu dawowa da wuri ba” 

Ok,,Amma lafiya kace haka,,kaida kake dawowa da wuri?

Nan daddy ya kwashe Duk abinda ya faru ya Gaya mummy,,ai be Ida zancen ba,,mummy ta tuntsire da dariya tare da tafa hannu tana cewa..

Kai Amma Yasmeen ta birgeni”toku me kuke a hospital tinda ance ta rasu Ai shikenan kaga Nima Na yadda kwallan mangwaro Na huta da Kuda..

Ran daddy a mugun bace ya daka mummy tsawa Wanda tasa mashkur firgita ya Tashi zaune,,kafin ya tambaya daddy abinda Ke faruwa sukaga Dr ya fito Yana goge gumin fuskansa,,

Tsaki daddy ya ja tare da katse Kiran suka bi Bayan Dr..

Yana Shiga office daddy yabi bayansa mama da mashkur suka tsaya a tsaye Suna sauraran abinda dr Ke Gaya daddy..

Mashkur Najin dr yace,, nijlah Na buqatar jini ya saki murmushi tare da yin sujjada a qasa Yana godewa Allah’ 

Be jira fitowan daddy ba ya dawo Dakin da aka kwantar da nijlah ya faki idon likitocin ya fada dasaurin gaske..

Yana Shiga ya tafi bakin gadon dasauri,,fuskanshi dauke da murmushi”

Kallan yadda take bacci ya Shiga yi Yana murmushi,, ahankali ya kai hannunsa Kan lallausan gashinta ya Shiga shafawa ahankali ahankali tare lumshe idansa,Wani irin yana Mai wuyar misaltuwa ya ziyarci zuciyarsa,,tare da farin ciki na ratsashi tako Ina ajikinsa.

Cike da shauqin kaunarta yakai bakinsa yayi kissing lips dinta Yana cewa” raguwa daka Dan tabaki Sai langwabewa mutane kama wacce ta Mutu” Sai kuma yayi murmushi Yana shafa lips dinta..

Yana cikin haka yaji an Tura qofan dasauri ya janye hannunsa a Kanta Yana Kallan kofan,,daddyne Sai mama suka shigo Dakin..

Sallamarsu ya amsa tare da Tashi tsaye ya Tura mama kujeran,,mama Bata Iya Zama ba ta tako Har zuwa bakin gadon tana kallan yadda nijlah Ke Jan numfashi ahankali..

Girgiza kai mama tayi ganin kankantan nijlah Amma Duk Da haka Yasmeen ta Iya zage kwanjinta Akan Yar karamar yarinyar”

Addu’a mama ta Shiga tofa nijlah Bayan ta gama ta juyo tana kallan mashkur,, ahankali mama ta Bude baki tana cewa..

Dan Alhaji kuyi hakuri Da abinda ya faru” yarone yanzu ka haifeshi Baka haifi bakinsaba…

Babu komai cewan daddy Yana murmushi” Sai Dai mu godema Allah tinda gashi yarinya da sauran kwananta a gaba”

Hakane sedai Duk da haka Ina Mai Baku hakuri musamman ma kai mashkur sabida kai akayima” Kuma nizan jamata kunne,,Na tabbata Hakan Baze qara faruwa ba..

A ciki ciki Mashkur ya amsa Yana Kallan gefe Dan tinda suka shigo be Daga kai ya Kalli kowa ba..

Idan akwai abinda Ake buqata Sai a gayamin,,inaso zanje gida Na dawo,,inyaso Saina kwana a gurinta basai kun Gaya iyayen yarinyarba???

Bakomai Nima nijlah kyatace zanyi duk abinda ya dace cewar..

Dan risinawa mama tayi tana yiwa daddy godiya tare da cewa nizan wuce tea Na taho dashi Idan ta farka Sai a Bata..

Dasauri mashkur yace” ah ah kibarshi kawai mama hakama Mun gode basai kin dawo ba..

Jikin mama a sanyaye tace kana ganin ba matsala mashkur’ kai tsaye mashkur yace eh babu..

Sallama mama tayi musu ta fita a Dakin jikinta Duk a sanyaye Duba da yadda mashkur yake amsata kama bayaso,,taso ace yabarta ta zauna da nijlah Dan tana ganin zatafi kowa Bata kulawa..

Tana fita daddy ya Hau Kan mashkur da fada ta inda yake Shiga batanan yake fitaba” shidai mashkur be Iya cewa komai ba Banda baqin ciki Babu abinda kecin ransa..

Kaima kanasan Zama mara Kunya kenan’ Koka manta yarta kakesan aure” Amma tana Magana kana sa baki,,kokai Zaka zabi yadda za’a Kula da nijlah..

Ahankali mashkur ya girgiza kai Yana Kallan daddy,,Sai da daddy ya gama kafin mashkur ya Bude baki a hankali yace”

Daddy nibanqi mama ta zauna da nijlah ba sedai daddy abinda Baze taba yiwuwa Kenan ba,,Ina tsoro Kar cikin dare Yasmeen ta qara zuwa inda nijlah take ta illatamin ita”

Gafara can ka rufemin baki,,soqoqon banza kawai,,Ina da Rana tsaka ita Yasmeen tayimata haka,,Kuma a gabanka Baka Iya tsinana komai ba Sai aikin kuka,,ka kirani kagayamin kuna hospital Baka Iya ba Sai dr Jamil ne yagayamin yaganka anan kafin Na baro office nazo..

Turo baki mashkur yayi kama qaramin yaro yace’ to daddy Yaya zanyi da ita nayi nayi ta dagata taqi” 

Kuma kake mana kazauna da ita anan Bayan bakasan yadda zakayi da itaba ita ta sake kawomata Hari?

Daddy ya tambaya”

Sosa kai mashkur yayi Yana cewa Hakan Bama zata sake faruwa ba insha Allah”

To Allah yasa yanzu Sai muje a gwada jininka day nawa Dan likita yace da yiwuwar a qara Mata jini danta zubda jini sosai..

To mashkur yace yana me tausayawa nijlah tare da yinqurin daukan mataki Akan Yasmeen..

Fita daddy yayi mashkur yaqi tafiya Yana Sosa kai” ka tsaya nan kana kallona Ko bazaka Bada jinin bane daddy ya tambaya cikin fada?

Daddy dama Naga ba kowane a Dakin shiyasa nakega kafara zuwa Sai nima naje”

Murmushi daddy yayi ya fita,,Yana fita mashkur ya dawo kusa da nijlah Yana Kallan yadda tayi Rama cikin wuni daya..

Bayan daddy ya dawo mashkur yaje aka gwada jininsa,,anyi sa’a yayi daidai da nata nan aka aka ya dawo Dakin..

Kallan Mashkur daddy yayi Yana cewa” mashkur nizan wuce anjima kaga yanzu karfe Goma yayi gashi haryanzu Bata tashi ba..

Eh daddy ba komai nizan kwanan anan,,Anya mashkur Zaka iya,daka Bari Na turo lateefah saita kwana a nan tinda Bata Riga ta tafi ba..

Dasauri mashkur yace daddy nizan zauna ba matsala” 

Duk yadda daddy yayi da mashkur Akan ya Bari mace tazo ta kwana da Nijlah kiyawa yayi haka daddy ya tafi da niyyan gobe da safe Ze dawo..

Bayan daddy ya fita mashkur ya Shiga toilet ya dauro alwala,,Sallah yayi raka’a biyu ya roqi Allah abubuwa da dama,,ciki Harda samun lafiyar nijlah tare da shiryuwan Yasmeen..

Karfe 12 ya gama komai ya dawo Kan gadon ya janye bargon da aka lullube nijlah dashi’ ahankali ya Shima ya kwanta Kan gadon tare da janyota jikinshi Yana shafa bayanta..

Duk da gadon yamusu kadan,,Amma haka besashi ya hakura da kwanciyaba,,saima qara rumgumeta yake a jikinsa..

Ahaka bacci yasoma daukarsa..

Wayarsace tafara ringin yakai hannu ya dauka Yana lumshe Ido”

Sunan daya ganine Na yawo yasashi Bude Ido da sauri Yana cewa”

Wannan yarinya kuwa tana da hankali yafada Yana Maida wayar silent tare da gyara kwanciyarsa Yana Maida nijlah jikinsa..

Tsaki Yasmeen tayi tana qara juyi Kan lafiyayyan gadonta,,tana cewa Shi Kuma wannan a Ina ya ajiye wayar yakuma San lokacin yin magananmu yayi,, Yasmeen tafada tana qara dealing number..

Wannan Kiran ma be amsaba haka tayi ta Kira tana tinanin abinda ya hana mashkur amsa call dinta,,Dan ita harga Allah ta manta da abinda ya faru Dan Koda mama ta dawo batabi ta Kan kowa ba tafada dakinta ta kulle tana tinanin yadda zata saita yasmeen..

Karfe 1:30 Na dare nijlah tafara Bude Ido ahankali tana Jin Wani azababban zafi Na ratsa Duk wata kofa ta jikinta” kasa Bude Ido tayi Saima rintse idon tayi sosai tana salati a hankali…

Can cikin bacci mashkur yaji yadda nijlah Ke fidda numfashi da sauri dasauri sabanin da, datake fidda numfashi a hankali..

Bude idansa yayi ya safke akanta Yana Kallan yadda take motsa Dan qaramin bakinta tana addu’a sedai Har zuwa yanzu ta kasa budesu balle tasan inda take..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button