YAR SADAKA Page 21 to 30

My baby ya gani nan yayi murmushi tare da duba sakon,,Yana karantawa Yana dariya harya Gama ya rungume wayar a qirjinshi Yana cewa”
Allah yasa haka babyna naji dadi kalamanki sedai bazan iya Baki reply ba har sai matata ta Samu sauqi keda kika dariyana..
Dagowa nijlah tayi tana sauraransa harya Gama magana Dan a fili yake magana” haushi da takaicine suka kamata Dan idan bata mantaba sunan dataji Yana Kiran Yasmeen kenan dashi a lokacin datake kwance Kan ruwan cikinta”mtssss yaji anja tsaki Wanda besan daga inda ya fito ba,,dasauri ya dago kansa Yana kallan nijlah da zuwa yanzu hawaye suka fara cika Mata Ido..
Kasa magana yayi sabida tsabar mamaki wai me wannan yarinyar take nufi Dani,,badai kishi take da baby ba?
Tabdijan indai ko hakane zanga irin zaman da zanyi dasu ahaka,,gashi Bani dasan raba Iyalina…
Yana cikin tinani nurse ta kwankwasa dakin,,firgigit ya dawo daga tinanin tare da bata umarnin shigowa” da sallama nurse ta shigo ta Basu ta kaddatar sallama tare da yiwa nijlah fatan samune lafiya,,da ameen Mashkur ya amsa nijlah ko bata iya magana ba sabida abinda ya tokare Mata maqogwaro..
Nurse na fita mashkur yafara hada musu kayansu,,Saida ya Gama ya juyo Yana Yana cewa,,zaki iya tashi mu tafi idan kuma anan zaki zauna to?
Nijlah bata amsashi ba ta tashi a hankali tana sa takalminta” dasauri ya fita yakai kayan mota ya dawo ya riqe hannunta suka fara tafiya” duk inda suka gifta kallansu Ake kowa na fadar albarkacin bakinsa ahaka har suka Kai mota nijlah na yimasa shagwaba wai ta gaji da tafiya,,be kulata ba ya zagaya ya Bude Mata mota Yana cewa”
Wai Bana gayamiki ki koya yadda Ake Bude Moto ba,,koni driver kine?
Murmushi nijlah tayi tace,Toba gashi can Wani ma Yana budewa matarsa Mota ba,,
Kallan inda nijlah ta Nuna mashkur yayi nan yaga wasu Mata da miji,,mijin ya budewa matar mota ta fito hannunta dauke da baby girl Yar qarama..
Murmushi yayi Dan Shima mutanan sun birgeshi” beyi Magana ba ya zagaya bangaren driver ya Bude,,Yana Shiga itama ta Shiga nan ya tada motan suka fara tafiya..
Seda sukayi Nisa ya juyo Yana kallanta” a hankali yace,,amarya Nima Zaki Iya Bani irin wancan babyn,,Naga kema yarinyar ta burgeki Ko?
Cike dajin Dadi nijlah tace” eh mana Zan Iya” cike da farin ciki Mashkur yasa hannu ya janyota jikinsa Yana shafata yace” yaushe Zaki Bani?
Kai tsaye nijlah tace” Abu me sauqi Duk lokacin da kakeso Allah Zan Baka,,ba ance ana bacci Ake haihuwa ba..
Tinda mashkur yaji abinda nijlah tace haushi ya kamashi anan ya gane batamasan abinda yake fada ba..
Ahaka Har suka qaraso gidan mummy”
Sai da ya daidaita parking motan kafin ya Bude ya fito,,itama ya Bude Mata.
Hannunta ya riqe suna tafiya a hankali Yana aiki yimata sannu” kai tsaye falon mummy ya nufa da ita…
Yawan comments yawan typing.
Share this
[ad_2]