YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 21 to 30

A kunne ya Kara Yana cewa” hello baby..

Uhmn uhmn wai haryanzu Baka zoba inata jiranka” bayan kasan na Gama hada lefen gani kawai zaka zo kayi,,abinda be makaba sai a chanza..

Murmushi yayi me sauti Yana cewa” nasan baby na ta iya Zabe,,karki wani damu nasan kayan sunyi kyau..

Kuka Yasmeen taka tana masa shagwaba,,nan da nan yaji babu abinda yakeso sai ganinta,,tini ya karya akalar motar ta dawo daga hanyar saban gida suwa gidansu Yasmeen…

To to shikenan ki kwantar da hankalinki ina hanya yanzu haka..

Wani tsalle Yasmeen tayi ta katse Kiran tana fadawa cinyar mama..

Seda Mashkur yayi nisa a hanyas ta zuwa gurin yasmeen ya Tina da nijlah dake kwance bacci me nauyi yafara daukanta,,yazo juyawa Amma baze iya ba Dan haka ya tafi da ita a cikin motan….

Comment & share

*Momn sultan ce ✍ ✍✍*

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*SIS NAJA’ART…..*

3⃣9⃣&4⃣0⃣

Tafiya yake Yana Jin farin ciki da annashuwa na qara ziyartar zuciyarsa” tin Yana tafiya anhankali har yaga tafiya bata sauri” gudu ya saki tare da kunna waqar soyayya dadi,,tini ta hade cikin motar da sauti me dadin gaske..

Tafiya yake Yana jinjiga,,kallo daya zaka masa kagane Yana cikin farin ciki..

A Dan firgice nijlah ta Farka sabida Jin iska me zafi tafara kadawa ga qaran kidan dake tashi..

Hannu daya yasa ya tare da,,dayan Yana tuqi dashi,, fuskanshi dauke da murmushi yafara shafa fuskanta Yana cewa”

Keda wa Naga kintashi a firgice” langwabewa tayi a jikinsa taqi tankasa” kodai azumin magana kika dauka,,nan ma nijlah batayi magana sema kwantar da kanta jikin kujeran mota tayi tana lumshe ido..

Uhmn” kema kin iya muskilanci ko,,turo Dan qaramin bakinta tayi tana girgiza masa Kai..

To meya tasheki adaidai wannan kuma,,har kina firgita?

Ahankali nijlah tace” Nima bansani ba..

Shikenan kirinqa addau idan zaki kwanta bacci”

Cike da sanyin jiki irin na Wanda ya tashi a bacci tace”

Aiba da dare bane,,kuma indai Zan kwanta da dare inayi,,kakama tana tofamin..

Waya gayamiki a bacci dare kawai Ake addu’a?

Shiru tayi Dan ba Wanda ya gayamata,,Niko nace wasu manyan ma basa addua lokacin baccin rana,yakuma kamata mu gyara,,sabida addu’a tana taimaka mana gurin kariya daga sharrin shaidan,,katangar qarfece ga duk wani musulmi…

Kinyi Shiru?

Nima bansani ba,,to shikenan saiki kiyaye,,kinga dai abinda yafaru yanzu..

To nijlah tace tana qoqarin komawa vaccinta.

Kingama munzo inda nakesan zuwa” ki zauna a mota nizan Shiga nan gidan yafada Yana Nuna get gidansu Yasmeen..

A hankali ta daga Kai tana kallan gidan gabanta na faduwa tace” kado nan kuma inane waiku Dama a birni kowa gidansa haka yake da ciyawa” kaga Dana zo da saniyana Aida ta Samu abinci,,ba ruwanmu da kaita jeje kiwo ko???

Hararanta yayi Yana cewa” zaki fara shirmen naki ko,,waya gayamiki abincin dabobine?

To menene Shi,,gashinan wani ya girma wani kanana a qasa,,sai ruwan banza Ake bashi tinda bashi da amfani..

Inji waye ta tambayeta Yana tsareta da Ido..

Gashinan na gani..

To wannan Bana saniya bane,,ado akeyi dashi anan bakuma nasan yawan surutu kinji nagayamiki..

Hannu tasa ta rufe Baki tana girgiza Kai alamar ta dena..

Daga haka yafara qoqarin Kiran Yasmeen a waya..

Yasmeen na kwance a cinyar mama tana zubamata shagwaba wayanta yafara ringing dasauri ta daga mama ta vita da kallo..

Hello baby gani na iso” oyoyo ta fada tana kallan mama”

Ganin zuwa’

No kibarshi Zan shigo da kaina kedai kawai ki budemin qofar Baya”

Ni dai ah ah,,Allah nizan shigo dakai tafada tana katse Kiran.

Gefensa ya duba yaga Yadda nijlah ta hade qiran Sama Dana qasa tare da turo Baki gaba..

Gabansa yaji yayi mugun faduwa da kyar ya iya magana cikin sanyin murya yace”

Ke kuma me aka Miki zaki bata fuska ko duk baccin ne”

Kama zatayi kuka tace” ba Kai bane.

Zafi Ido Mashkur yayi Yana kallanta,,

Nikuma me nayi Naga kece me laifi Amma zaki doramin kodan kinga bamu qarasa gida na hukuntaki ba,shiyasa zakimin rigima?

Turo Baki nijlah tayi tana Jin bacin Rai tare da kishi me zafi tace..

Kuma shikenan saika kawoni nan kana waya da wata qatuwa.

Mamakine ya cika mashkur cikin zuciyarsa yace na Shiga uku kaddai ace yarinyar nan kishina take” a fili ko cewa yayi ke wai harkinsan wani Abu kishi?

Koda bansani ba ai bazakayi waya da wata a gabana ba.nijlah ta fada tana murguda Baki.

Rasa Yadda zeyi da ita yayi gashi Yasmeen taqi Yadda ya Shiga ciki,,yasani idan yaqi tsayawa su Shiga tare baza’a Samu hiran arziqiba ta riqa yimasa Mita kenan,,to idan kuma ta fito taga nijlah fa,,Yaya zanyi ya tambaya kansa..

Sai yanzu yake Dana sanin zuwa da nijlah be Ida zancen zuci ba yaji nijlah Na cewa” 

Kaga Ni Idan bazaka kaini gidaba saika budemin nayi wasa acan tafada tana nuna jikin wasu fulawa..

Tsawa ya daka Mata Yana cewa waini sa’ankine zaki riqa magana Dani Yadda kikeso?

Dasauri nijlah tace nadena..

Bangaren Yasmeen ko da sauri ta koma daki ta qara shafe fuskanta da powder ta yasha mayafi ta fito tana tafiya a hankali..

Me aikinsu ta riqa kwala Kira,,dasauri ta fito tana risinawa tace aunty gani.. kingama hada kayan abincin Dana saki,,eh angama suna can falo anshirya komai..

Yasmeen bata qara magana ba ta koma daki ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi,,dakin mama ta dawo tana cewa mama Zan shigo dashi..

ke da Baki shigo dashi tin dazu ba,, murmushi Yasmeen tayi tana boye fuska tace mama ina yimasa kwalliya..

Ke dai Allah ya shiryeki,,Bako kunya kike Bani amsa Yasmeen,,cikin dariya Yasmeen ta fita tana murnar ganin angon nata…

Turus tayi ganinshi cikin mota hannunsa riqe Dana nijlah suna magana’

Wani irin yawu ta hadiye me dacin gaske tana tambayar kanta..

Wacece kuma wannan me kama da ‘ya’yan larabawa,,to kodai ‘ya’yan yayyensane,,Kai ah ah baby be taba zuwa da wani yaro nan ba,,Kai Bama ze Zama sune ba Dan su Bama a qasar suke zaune ba..

To wacece wannan ta sake tambayar kanta” ganin hannunsu sarqe Dana juna yasata saurin qarawa jikin motar tana cewa kambu lallai yau akwai bala’i,,tana Gama fadar tafara qoqarin bude motar da dukan qarfinta,,Banda rawa babu abinda jikinta yake,duk Wanda yaganta yasan bata cikin nutsuwarta”sosai zuciyarta ke bugawa da qarfin gaske,ta dauka aniya a ranta komai zai faru sedai ya faru Amma yau ko ita ko wannan yarinyar me suffar aljanu..

Wallahi yau Sena Baka mamaki baby ..

A firgice mashkur ya janye hannunsa daga na nijlah ya qaqalo murmushin dole Yana aika Mata,, bude kofan yayi Yana cewa amarya”

Dole kace amarya mana’kaga baby ni duk ba wannan ba,,wacece wannan da har kake riqe Mata hannun ta fada cikin tashin hankali da zafin zuciya tana nufo inda nijlah take..

Dasauri yasa hannu ya tare ta Yana cewa” haba Yasmeen meyasa zafin kishinki yayi yawa” kifa rage ina gayamiki..

Cikin fishi tace dole zakace Kaka sabida kaci amanata Ka yaudareni da soyayayarka,,Amma duk da haka na amince da aurenka shine zaka nunamin Bani kadai kakesoba..

Kidai nutsu Saina gayamiki ko wacece” 

Ka gayamin yanzu indai baso kake zuciyana ta Gama bugawa yanzu ba..

Matsowa yayi kusa da ita sosai had suna jin numfashin juna da bugun zuciyar kowannesu yace”hannunta ya kama cikin masa ya riqe sosai Yana shafawa duk Dan yasamu ta dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta,,Amma duk da haka taqi tsayuwa burinta kawai taji kowacece kafin tasan hukuncin dazata yanke akanta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button