YAR SADAKA Page 21 to 30

Cike da tashin hankali yake magana Yana kallan Yadda nijlah ta rikice ta gigice ta kidime tana kankame jikinta hawaye tuni sun wanke Mata fuska Banda karkarwa babu abinda take tana Kiran sunan Allah”
Yace,,pls Yasmeen ki saurareni,,kinfasan da kaunarki na rayu, kuma haryanzu kina cikin zuciya na babu abinda ya chanzaki” to meyasa kike yiwa babynki haka,, wannan yarinyar kanwatace ki nutsu mana..
Ganin taqi nutsuwa sai zufa take yasashi juyawa inda nijlah take zauna yace”
Nijlah ki gayamata koke ba kanwat…. Be iya qarasawa ba sabida ganin nijlah kwance a qasa Yasmeen ta hau kanta tana Duka..
Bane ni zaka yaudara ko an gayama bansan sunan *’yar sadaka* nijlah ba,,zaka ha’inceni” to wallahi yau koni ko wannan tsinanniyar yarinyar,, Dama akan wannan kake wulaqantani…
Kukama nijlah kasawa tayi Banda Ido babu abinda take rabawa” ta ko ina Yasmeen ke dukanta har Saida numfashin nijlah yafara sarqewa..
Duk Yadda mashkur yayi Dan ganin ya kwaci nijlah ya kasa Dan ba ruqon Wasa Yasmeen tayi Mata ba,,tana dukanta tana surutai..
Rasa inda mashkur zesa ransa yayi Banda tashin hankali da firgice babu abinda yake ji” waiwaye ya riqayi koze Samu Wanda ze ceci nijlah ya Rasa,,sabida layin ba mutane indai ba lokacin sallah yayi kaga suna fitowa ba..
Dabarace ta fadowa mashkur yafara kwalama get man Kira Dan Shi kadai ze iya jinsu adaidai wannan lokacin..
Me gadi na zaune jikin get yasa radio a kunannsa Yana sauraran wani shiri inda yaji labarin governor ganduje ya tsige sarkin Kano Muhammad sinusi ya Dora hannu aka Yana salati,,hakan ne ya hanashi Jin kiranda mashkur ke masa.
Cikin zafin Rai mashkur yayi Kan Yasmeen da Duka ganin Yadda jini ke fita ta Baki ta hanci a jikin nijlah,,Amma Duk da haka yasmeen Bata dena Dukan taba haka Kuma bakinta beyi Shiru ba..
Wallahi Ko Zaka kasheni Saina fara kashe wannan abun tsiyar Idan yaso Sai kayi abinda zakayi..
Yana hawaye yace” shikenan Ai kin kasheta saiki dagata,,kaicona Ni mashkur Dana kasa riqe amanar Dana dauka Yasmeen baki kyautamin ba,,ki dagata Nace kafin nayi qasa qasa dake yanzu..
Ganin yadda hawaye Ke fita a idanshi yasa Yasmeen Tashi Akan nijlah bakinta Na rawa tace”
Baby kuka kake akan Na Daki wannan yarinyar” me Zan gani Ni Yasmeen Sai kuma ta fashe da kuka ta Shiga cikin gida da gudu tana yarfe hannu,,jikin rigarta da hannunta Duka jini ya Bata..
Tana Shiga me Gadi ya yarda radio yayi Kanta yana tambaya,,kallan waje yayi yaga motan mashkur,,dasauri ya fito Yana tambayan yallabai lafiya..
Chak numfashin mashkur ya tsaya ya Dena aiki,fa gudu yayi kan nijlah Yana kuka saikace qarami n yaro ya tattarota jikinsa Yana jinjigata tare da Kiran sunanta,,jikin Na kyarma ya saketa Yana salati..
Daidai lokacin get man ya qaraso Yana cewa yallabai lafiya” ganin mace kwance Bata numfashi yasa qarasawa Yana matsa hancinta..
Baba ta Mutu Ko,, shikenan Yasmeen kin gama da rayuwana,, nijlah naso ki girma naga yaranmu dake,,naso kema ki dandana rayuwa ta Jin Dadi Sai gashi kin rigamu gidan gaskiya” Sai kuma ya chakumi wayan rigar baba me Gadi Yana cewa,
Dan Allah ka dubamin ita Bata Mutu ba Ko??
Girgiza kai baba me Gadi yayi Dan yariga ya tabbata da mutuwar nijlah sedai Baze Iya gayaba sabida Shima mashkur yaga Hakan..
Baba me gadine yayi qoqarin Tashi Ze ciccibi nijlah yasata a Mota Domin aje ayi jana’izarta.
Mashkur yayi saurin Shan gabansa Yana cewa karka taba ta,,nizan sata a Mota da hannuna,,Allah yajiqanki Nijlah,,wayyo Ni mashkur wannan wacce irin ranace na riska..
Yana kuka yasata a Mota ya nufi hospital da ita,,nan likitoci suka Hau Kan Dan ceto rayuwarta,,seda sukayi kusan 30 minutes akanta kafin Naga daya Daga cikinsu yajamata mayafi ya rufe fuskanta..
Jikinsu a sanyaye suka fito.
DA gudu mashkur yayi kansu Yana cewa likita Yaya Bata Mutu ba Ko?
Shafa kansa dr yayi Yana cewa kayi hakuri mashkur…
Be Bari yaqaraji ba ya fizge hannunsa ya Shiga Dakin,,direct Kan gadon da nijlah Ke kwance yace ya Bude ta..
Wani ihu ya saki ganin hancinta da kunnata rufe da adduga,, haryanzu jini bai Dena zuba ba..
Salati ta kurma Yana neman daidaita nutsuwarsa,,sedai be samu damar Hakan ba yayi Baya luuuuuuuu……
Idan kuka qara comments irin Na jiya,Bazan qara posting ba Sai Bayan Sallah Idan Allah yasa muna da raban gani..
Dan Allah ku riqa sharing danayi posting,,banaso ana damuna Akan Na turo,,abin dayawa Idan Na biyeku Bazan Samu lokacin kaina ba..
*Momn sultan ce*✍✍✍✍
???????? *’YAR SADAKA..*????????
*STORY & WRITING BY…*
*BY*
*MOMN SULTAN*
*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*
*SPECIAL GIFT TO…*
*MMN FAREESAH….*
4⃣1⃣&4⃣2⃣
Yayi Baya luuuuuuuu,, dasauri sauran likitocin dake tsaye sukayi nasaran tare sa Suna salati..
Taimakon gaggawa suka Shiga bashi,,cikin Ikon Allah suka Sami damar dawa masa da numfashinsa,,sedai Yana farkawa ya dafe kai Yana hawaye..
Ruwan da aka dauramasa ya fizge tare da Tashi tsaye cikin tashin hankali,,jiyake Shima kama Ze Mutu sabida ya tsara yadda rayuwarsu zata kasance da irin soyayya da zasu gudanar a Duk lokacin da komai ya daidaita..
Daddy ne ya shigo ransa a bace,,Yana tafiya cikin sauri harya qaraso inda mashkur Ke tsaye” mashkur besan da zuwan daddy ba sabida yadda yake acikin tashin hankali.
Motsin dayaji a bayansa ne yasashi saurin zabura a gigice jikinsa Har tsuma yake tsabar tashin hankali Hade da Dana Sani mara musaltuwa ya Bude baki zeyi Magana daddy ya katseshi…
Bakin daddy Na rawa kama ze kifa sabida tashin hankali yace”mezaka gayamin auta,,Ashe Baka da hankali” yanzu mezamu Gaya iyayen yarinyarnan”Yama za’ayi ka dauki ‘yar mutane ka kaita wannan gidan,,Bayan kasan halin mahaifin Yasmeen da Kishin tsiya,,gashi Shi bedauka mataki ba Yasmeen ta dauka,,sun kashe marainiyar Allah wanda bataji ba Bata gani ba..
Kuka me ciwo mashkur ya saki,,da gudu yafada jikin daddy,,cike da matsanancin tashin hankali mashkur yace” daddy Dan Allah kada ta Mutu wallahi banshirya rabuwa da itaba,,daddy inasanta Dan Allah daddy kace ta Tashi..
Ganin da daddy yayi ba’a cikin hayyacinsa yaje ba shiyasa ya rungumeshi Yana shafa bayansa..
Sedai yadau lokaci jikin daddy Yana kuka kafin yafara safke ajiyar zuciya” ganin haka yasa daddy fara Magana a hankali..
Garin Yaya ka tafi da yarinyar mutane Har akayimata irin wannan illar,,kana Ina Hakan ta faru daddy ya jera masa wadannan tambayayoyin?
Bakin mashkur Na rawa yace,,daddy kayi hakuri Nima bansan haka zata faru ba,,kasani cewar daddy tare da tsaresa da Ido” wallahi daddy bansani ba,,Dana sanina Hakan tafaru ba,,nayi nayi tabari Amma Duk da haka Saida ta kashemini ita mashkur yaqare maganar cikin gunjin kuka..
Wallahi inasanta banaso Na rasata,, kuskuren ne Yasmeen ta Riga ta aikata mana,,daddy bansan yazanyi da itaba..
Mama na zaune a falo tana kallo Taji fadowar Abu akanta” dasauri ta dago tana kallan yasmeen,, cike da tashin hankali tafara jera Mata tambayoyi”
Yasmeen meya sameki” accident kukayi,,Ko Yan bindiga dadine suka tareku,, Yasmeen Bata Iya amsa mama ba, Saima kukanta data qara saki tana qara shiga jikin mama..
Tureta mama tayi tana cewa” Dan gidanku ki gayamin,,gaba daya kin Tashi hankali to kodai Yan garkuwane suka tareku a hanya..