INAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 51-55

Yana barin gurin umma yaganah Haj umma suka kalla itada anty Hafsat sukaga yanda tayi zuru da mamaki dashiga tunanin agaban kowa MAJEED zaiyi mata magana Mai Kama da fada kaman shine uban nata.

Juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma bedroom dinta tanaji wayarta na ringing juwairiyyah na Kira takasa dauka sbd ranta ba Dadi ko kadan bazata iya wani bacin ranba sbd yanzu juwairiyyah Zata sake dorata akan abinda zai quntata ranta.

Anty Hafsat Kuma bayan Inayah tabi zuwa dakinta Dan tausarta Amma rarrashinta duniya tayi Inayah din Taki Dena kuka.

Har bayan magriba suna fama da Inayah din Haj umma dake dakinta tana Dan jiyo yawon umma yaganah da Anty Hafsat gurin rarrashin Inayah din sama sama
tayi banza dasu sbd gabaki daya ganin takeyi su suka Gama lalata Inayah din da bakinta baya tauna magana sam Sam.

Ana gap da ishai haka anty Hafsat ta hakura ta tafi gida tabar umma itama tayi nata rarrashin ta hakura ta zubawa sarautar Allah Ido.

Abincin dare ma kusan daga ita sai Haj umma ne sukaci Inayah taqi fitowa shima MAJEED din baizoba Koda Haj umma takirasa shayi kawai yace akai Masa.

Zubbi ce takai ta ajiye Masa a palonsa ta fito ta dauki da Inayah ma da umma tace ahada Mata takai mata Amma ko motsawa Inayah batayiba tana kwance.

Duk dubara da rarrashin umma yaganah Inayah kin Shan ko tea tayi Dan haka jiki a mace umman ta barta taje ta kwanta.

Zafi da ciwo zuciyarta ke Mata sosai bayan hawaye Babu abinda takeyi sbd bazata taba iya kwatanta Abbinta da wata macen ba,

Wannan zafin datakeji har abbin ma takejin zafinsa akan lamarin.

Kwana tayi da ciwo a Rai da damuwa me tsanani Dan haka Koda garin ya waye da wani zazzafan zazzabi ta tashi Mai qarfi.

Zubbi da umma yaganah ne akanta hankali tashe umma na rage Mata zafin gashinta da farin qaramin towel
Zubbi kuwa chocolate custard me zafi ta hado Mata da farin soyayyan qwai Mara komai aciki.

Kasa Shan komai tayi Saida umma yaganah ta nuna Mata rauninta na itama Zata iya kuka idan Inayahn bataciba kafin Tasha custard din aikuwa ko Gama Sha bataitaba amai ya taso Mata da sauri zubbi ta kamata takaita toilet ta ringa Aman cikin wahala sbd rashin qarfin jiki.

Bayan tagama ruwan zafi zubbi ta hada Mata tayi wanka ta fito umma ta dauko Mata wata qaramar Riga Mara tsayi Mai taushi ta saka Takoma ta kwanta jikinta na tsananta zafi.

Wanke toilet zubbi tayi ta gyare dakin tsaf ta kashe Mata AC ta kunna humidifier bayan tazuba wasu turaruka cika masu dadi suka fice daga dakin har umma.

Umma na barin dakin tana Isa nata ta dauki wayarta ta saka Kiran MAJEED.

Ta jima tana ringin kafin ya daga murya ahankali yace”

Barka da yau umma.

Barka MAJEED,
Yau baka fitoba Allah yasa lfy dai ko?

A natse Yana danne yanayinsa yace”

Lafiya kalau alhmdllh,
Yaya Inayah?
Tana Nan tana Rigimar ko?

Numfashi ta sauke a sanyaye tace”

Tanata rigima tun jiyan gashi yanzu ciwo yashigo ciki sbd zazzabi Mai qarfi takeyi custard ma datakeso Tasha tayi amansa,

Bansaniba ko Dr farhat din zaa Kira tazo ta dubata Amma Kuma wata sabuwar rigamat zatayi tana ganin Dr farhat din.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda cewa”

Ganinan zuwa zanfara dubata kafin Akira likitan.

Kashe wayar umma tayi tareda ajiyewa gefe tana Zama kan kujera tana cewa”

Allah yasa ta tsaya taji maganarka.

Kwance take tanajin zazzabin sosai bacci na Dan daukanta Yana sakinta duk da hakan tunanin Abbinta da aurensa na maqale cikin ranta.

Turo kofar dakin yayi Kai tsaye tareda shigowa a natse sbd shima ciwon Kaine atare dashi.

Fararen Fendi wears ne ajikinsa
yau Qamshin nasa ma ahankali yake tashi daga jikinsa sbd Bai wani saka turareba Qamshin na jikinsane daya dade da Kama Turaren Mai sunyin Dadi.

Cikin nutsuwa ya tako har bakin gadon ya tsaya Yana kallonta ahankali cikin nutsuwa ya lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta cikeda kaunarta Mara sirki da qarfi wadda take gine cikin ransa shiyasa Sam Baya son bacin ranta ko damuwarta Amma tacika rigima yanzu duk akan aurensa dake kanta data dauka ta saka arai.

Bude idanuwanta dasukai nauyi da sauyawa sbd zafin zazzabi Jin mutum akanta tasan Abbin ne sbd qamshinsa daya shiga hancinta.

Maida idanuwanta tayi ta rufe tanajin nauyin kirjinta na qaruwa sai kawai hawaye suka fara gangaro Mata.

Yana ganin hawayen nata yaji jikinsa yaqara sanyi ya zauna ahankali bakin gadon nata tareda Kai hannunsa dakeda sanyin ACn Daya fito ya taba goshin yaji zafinsa sosai

Da kulawa sosai yace”

Da wannan zazzabin naki ajikinki kike sake wani kukan Inayah??

Kinason ciwo ya kwantar dake ne?
Meyasa bazaki Dena kukanba haka?

Juyar da kanta tayi tana sake sakin kuka Mara sauti a wahalce batareda tace Masa komaiba.

Shigowar Haj umma ne tareda Salimat data kawo wasu ruwan da towel Zata rage Mata zafin jikinta da umma yaganah tace zubbi takuma Yi Amma zubin na aikin gyaran Haj umma Dan haka ita takawo.

Haj umma kuwa duba Inayah din tazo yi sbd rashin lafiyarta yasa gidan kaman anyi mutuwa kowa tsit ba walwala tunda princess din gidan ba lafiya.

Salimat na ganin Abbi a dakin ta ajiye ruwan kan bedside drawer ta juya ta fice.

Haj umma ma da ‘yar kulawa kadan tace”

Yaya jikin nata?
Allah yabata lafiya
Amma saita sakawa kanta salama
Wannan kukan Babu abinda zai qara Mata sai ciwon.

Amin”MAJEED ya amsa a taqaice Yana sake taba gashin Inayah din daya zafinsa yaji duk ya daga Masa hankali harya Dena Jin nasa ciwon kan.

Cikin kulawa yace”

Ina Ms Salimat take tazo ta rage Mata zafin jikin kafin Dr farhat tazo ta dubata..

Fadan sunan Dr farhat kawai yayi yasata sake tsananta hawayenta saiga umma yaganah ta bude kofa itama ta shigo da tea me zafi a tray tazo ta ajiye.

Umma yaganah ki rage Mata zafin jikin Nan yayi yawa kafin likita tazo ta dubata jikin nata Yana tsananta zafi sosai…

Cikin kuka ta tashi zaune daga kan gadon tana cewa”

Ni banason Dr farhat ta dubani
A Kira Dr Abdul….

Satar kallon Abbi umma yaganah tayi tana matsowa gurin gadon Zata dauki qaramin towel din Fadi tas

Cikin kuka Inayah tasake cewa”

Ni har rage zafin banason tunda ba zafin danakeji a zuciyata zaa rageba,

Wlh abbi idan kayi wani auren zuciyata bugawa zatayi nidai Dan Allah kacewa Haj umma bakason auren Nan bazakayiba
Banason kowa ta Zama matarka saini kadai…..Ni ko rage zafin banason umma tamun Kai zakamun idan bakaiba banason kowa yamun abarni zafin ya kasheni na mutu na huta bazanga ka aura kowaba…..

Wannan karon salati Mai qarfi Haj umma take saki idanuwanta na rarrabuwa tsakanin umma yaganah da MAJEED taga yanayinsu akan wannan tsabaragen rashin kunyar da iskancin na Inayah Amma saitaga kowannensu yayi shiru kusan itama umma yaganah taji kunyar zancen Amma Kuma majeed yafisu shiga mamakin saidai kaman koyaushe baa cika gane reaction dinsa akan Abu.

Matsowa umma tayi tana kokarin Mata fada a fakaice sai kawai abbin ya miqa hannu ya karbi towel din tareda cewa”

Ba damuwa Zan Mata.

Cikin ruwan ya saka towel din ya Ciro ya matse ruwan ya Dora Mata a goshi har lokacin hawaye takeyi.

Ahankali yace”

Hawayen ya Isa haka tunda gashi inayi.

Riqe hannunsa dake goshinta tayi ahankali jikinta na sanyi da zuciyarta sbd bazata iya fushi da Abbinba
A hankali tace”

Abbi kayi hkr ka yafemun bazan sakeba.

Neman sakewa jikinsa keyi yayi qarfin halin riqe yanayinsa tareda sakar Mata murmushi cikin tsananin kulawa yace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button