INAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 51-55

Lumshe ido yayi tareda zubawa fuskarta Ido yayi Mata kallon kusan mintuna uku kafin ya zame ahankali ya tashi ya wuce toilet.

Brush yafara Yi kafin su alwala yafito ya sauya kayansa zuwa jallabiya ya fice zuwa qaramin masallacin gidan nasu.

Bayan fitarsa bada jimawaba itama ta tashi dayake dama ta saba tashin asuba kan lokaci Kuma shine ya koyar da ita hakan harya Zama jikinta lokacin sallah nayi Zata farka.

A toilet dinsa tayi alwala ta fasa sabon brush tayi ta fito tayi sallarta anan Takoma ta kwantawarta….

Jin rigarta na damunta ta zareta daga saman tabarta a kirji ta shige quilt Takoma baccinta sbd sanin abbinma baya dawowa wasu lokutan da wuri daga masallaci wani lokacin gym yake tsayawa Yi a gym room dinsa.

Koda ya dawo baiyi tsammanin zai sametaba Dan ya dauka Zata koma dakinta kodan nauyin abinda ya faru dasu jiyan.

Bai lura da itaba sbd har lokacin dakin Babu haske sosai Dan haka ya zare jallabaiyarsa dagashi sai dogon wandon kayan baccinsa ya hau gadon tareda shigewa rufa sai kawai yaji mutum aciki..

Hannu yakai Dan tabbatarda ita dince ba zato hannunsa ya sauka kan tattausan kirjinta da rigarta ta zame tabari…..

Dagashi har ita dake bacci wani mummunan shock suka Shiga Musamman shi da kusan bugawa kansa yayi…

Janye hannunsa yayi da sauri Yana dauke Kai daga kallonta ya kwanta Yana lumshe idanuwansa batareda yace komaiba.

Itama idanuwanta ta bude zuciyarta na Dan harbawa sbd hannun Abbinta yasata dukkanin jikinta mutuwa.

Juyowa tayi ta zubawa kyakkyawar fuskarsa datake sake narkar da zuciyarta akan kishinsa ta saki wani qayataccen murmushi Mara sauti tareda matsowa jikin nasa ahankali ta shige tana zura hannuwanta ta zagayesa ahankali tace”

Good morning Abbi.

Bai bude idanuwansa ba ya shafa kanta ahankali cikin kulawa yace”

Morning.

Murmushi takuma sakewa tace”

Best morning ever…

Bude Ido yayi ya saukar akanta Yana kalla batareda yace komaiba sai lumshe ido dayake akai akai.

Bacci takuma komawa abinta shima ahakan yayi bacci Mai Dadi har kusan qarfe goma Basu karfaba Saida wayarsa ta ringa zuba ringing kafin ya tashi..

Wanka yafara shiga Kai tsaye sbd ganin time yaja Kuma yanada baqin dazai gani yau din office.

Yana cikin wanka ta farka Dan haka itama Kai tsaye ficewaa tayi zuwa bedroom dinta sbd yau garau takejinsa Zata iya leqawa asibiti.

Tana fitowa Babu kowa a main Palo Dan haka dakinta ta nufa Kai tsaye ta fada toilet tayi wanka tana Jin farin ciki koina aranta.

Tana fitowa daureda towel brown taji salatin Haj umma na tashi da qarfi hakama umma yaganah kaman suna magana cikin daga murya da tashin hankali.

Kasa tsayawa komai tayi ta fito a rude daureda qaramin towel din tana zaro ido cikin tsoron meke faruwa sbd su gidan Basu Saba da hayaniyaba.

Tana fitowa dukkaninsu idanuwansu suka dawo kanta
cikeda mamaki da tashin hankali suke kallonta Baki sake..

Da sauri umma yaganah da hankalinta yafi na kowa tashi ta kalli Inayah din tace”

Ina kikaje tun daren jiyan Inayah????

Haj umma ce ta karbe da cewa”

Wlh idan Bata fada Inda tajeba yau duka Zan Mata a gidan Nan idan su Basu taba dukankiba sbd gata Ni yau Marinki zantayi sai fuskarnan Taki Takoma jajir sbd bazan iya kallon wannan shirmen dake faruwaba a gidan nan,

Tun tsakar dare yaganah tace taje dubo jikinki Bata samekiba,

Zuwanta uku bakya dakin bakya gidan anduba koina bakyanan,

Yanzu tunda safen Nan ankira Dr Abdul yace bakizoba Kuma baacan kika kwanaba,
Hakama hafsat ankira tace bakizoba,

To Ina kikaje?
Wace rayuwa Zaki saka MAJEED Kuma yanzu da damuwar wannan sabuwar dabiar?????…….

Cikin takaice Inayah ta kalli Haj umman kafin ta juya ta kalli umma yaganah datake kallon MAJEED Daya fito lokacin
Ta sake maida kallonta kan Haj umma tace”

A dakin Abbina na kwana gurinsa meyesa Baku duba canba???

Maida kallonta tayi kan Abbin tana ciko idanuwanta da Hawaye tareda Bata fuska hawayen na saukowa tace”

Abbi Ni ko a Australia na taba kwana ba gida bane?

Haj umma tace saina fada inda nakwana Ni kafada Mata agurinka na kwana…

Dan dafe gashinsa yayi daya fara Masa wani irin nauyin abinda take fada din…..

Ganin haka ta fasa kuka tana kallonsa kafin ta maida kallonta kan Haj umma datai mutuwar tsaye zatai magana cikin kuka tana riqe towel dinta dake Neman faduwa ba tsammani su Haj umma sukaga yayi saurin riqe Mata towel din tareda kallonta cikin Ido a natse da qaramin sauti yace”

Ya Isa menene na kuka anan Kuma?

Ni Abbi ka fada Mata Inda na kwana taji da kanta….

Naji ya Isa kukan kije ki saka kaya sanyi zai kamaki ahaka….

Haj umma ya juyo ya kalla cikin takaita Rigimar yace”

Umma please tayaya zaku fara tunanin Inayah Zata iya zuwa wani gurin ta kwana….

Umma yaganah ya kalla Yana Dan sake kokarin danne ‘dacin da zancen yayi Masa yace”

Tayaya zaku fara wannan tunanin akanta?

MAMUH

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button