INAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 51-55

Haka Inayah taqi tafiya daki saida ta dafa tea takai Masa tareda cake Mara zaqi sosai sbd Sam bayason zaqi ko kadan.

Haj umma na kallo Inayah taje palon nasa Kuma ta dauki mintuna sosai kafin ta fito Wanda itakuma tsayawa tayi yafito daga bedroom Amma tayita jira Bai fitoba Dan haka ta tahowarta ta wuce daki jikinta a sanyaye.

Washe gari haka abbin yakuma fitar safe Bai tsaya breakfast ba Kuma Bai dawoba sai dare yauma.

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun abin na Wasa saigashi Abbi ya rage zaman gida Sam Baya Zama he’s always busy Sam yaqi bawa kowannensu time sbd Haj umma tafara tunkararsa da maganar Dr farhat Wanda Inayah Bata saniba batada labari
Umma yaganah ce kawai tasani Kuma taqi barin Inayah taji zancen sbd rigimarta.

Hankalin Inayah tashi yayi fiyeda komai,
Rashin lokacinsu daga Abbinta yasata sukukucewa ta daga hankalinta sbd tsoron ko tayi wani lefin ne tunda itama tasan bataji.

Haj umma ma tashi hankalinta yayi tashiga damuwa tareda Dora lefin akan Inayah tayi masa lefi ne shiyasa yake cikin damuwa Dan kuwa damuwa ta nuna sosai akan fuskarsa.

Jin Abbinta na cikin damuwa yasa hankalinta ninkuwa atashi Dena fita aiki sosai tana Neman hanyar zaunawa da Abbin tabasa hakuri.

A bangare Daya pressure din da Haj umma ke basa akan ya aura Dr farhat yasa ciwon Kai Mai tsanani kamasa qarshe ya Dena fita sbd Yana buqatan kansa ya sake sosai.

Ga Inayah duk yanda taso ta kusantoshi bayaso yanzu sbd matsalar da hakan ke basa
Itakuma ganin hakan saita rikice da damuwa sbd bayason tana zuwa gurinsa sosai.

Dr farhat ce tazo daga gidansu ta dubasa sbd ciwon kan ya tsananta Masa.

Rashin bacci ne da damuwa yake damunsa abinda yafadawa Haj umma.

Hakan kuwa yasa Haj umma yanke shawaran aurawa majeed din Dr farhat Kai tsaye sbd yasamu Mai kulawa dashi,

‘danta yana buqatan kulawar mace
Wadda Zata sakasa farin ciki tabasa kwanciyar hankali Kuma bataga hakan atareda Inayah ba wadda bayan shagwaba datake zuba Masa Babu abinda Zata iya Dan haka bazata zuba Ido ‘danta ya mutu abanzaba ko jikiki Bata samuba.

Anty juwairiyyah takira tanayiwa wannan bayanin akan harta Kira qanin abbansu MAJEED din zaa saka lokaci a je Neman auren.

Umma yaganah damuwa da nata tashin hankalin tashiga Jin hukuncin Haj umma din Wanda Kuma Babu Mai iya takesa tunda itace uwar MAJEED Bayan shi Babu Mai iya tsallake wannan zartarwar.

Hafsat takira a waya tace tazo tana nemanta sbd Dole sufara shawarar yanda Inayah zataji wannan mugun labarin.

Abinda Bata saniba shine MAJEED din ya amince kokuwa? sbd batai maganar dashiba Kuma shima baizo yamataba.

Inayah na asibiti anty Hafsat tazo cikeda damuwa sbd umman tafara Mata bayani a waya shiyasa batazoba Saida ta tabbarda Inayah na asibiti.

Tagumi suka rafka dukkaninsu biyun cikin dakin umma Bayan umma yaganah tagama yimata bayanin abinda yake faruwa ta Dora da cewa”

Hafsat ki kokarta ki sake nutsar da ita tasan abinda takeyi Dan kuwa kishiya da qananun shekarun Nan nata da sangantar datake basune zasu fiddataba Duk kuwa da tsananin son da MAJEED ke Mata idan ya auri wata macen yasamu nutsuwa a gurinta bazata sake gane komaiba.

Numfashi anty Hafsat ta sauke cikin takaici da damuwar maganar tace”

Umma Inshallah Inayah bazata taba wulaqanta a hannun AA ba saidai Zan dage na sake lurar da ita abinda yake gabanta..Amma dai yanzu inaga kada abari tasan Abbin aure zaiyi kusa…….

Inayah dake bakin kofar shigowa dasuka Bari a bude Zata shigo
A Rikice qafafunta na rawa tace”

Aure Kuma?

MAMUH

HOT/LOVE/ROMANCE

MAJEED& INAYAH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/9, 11:49 AM] +234 816 828 4180: 52
Arewabooks@Mamuhgee
Da sauri suka kallo kofar lokaci daya atare cikin mamaki da fargaba.

Anty Hafsat ce tayi saurin tasowa tana kokarin riqo hannunta su qaraso ciki tana cewa”

Yaushe kika dawo Inayah?

Bata amsa tambayar ba sbd batama wani gane me Anty Hafsan ta fadaba qafafuwanta na rawa zuciyarta na bugawa da qarfi tace”

Anty Hafsat abbi ne naji kuna maganar zaiyi aure fa?

Kinga Inayah zauna muyi maganar a natse ba abinda kikaji din bane wata maganar muke……

Kasa Zama tayi ta tsaya tana kallon umma yaganah da duk tayi wani iri sbd damuwa wadda take bayyane qarara a kan fuskarta

Take taji wani mugun tashin hankali da ‘daci na cika maqoshinta zuwa bakinta da qyar ta tattaro yawu tace”

Anty Hafsat fuskar umma yaganah ta nuna tana cikin damuwa
Karki wani boyemin ku fadamun Gaskia idan aure Abbi zaiyi Ni insani..

Yanayin yanda tayi maganar muryarta a harde da tashin hankali da firgici yasa umma yaganah sauke numfashi tana dagowa ta kelleta dakyau cikin sanyi ta janyo hannunta tana cewa”

Zo ki zauna Kuma ki nutsu hafsat Tai Miki bayanin komai banason hayaniya ko tashin hankali iya maganace kawai tunda ba auren aka Riga anyiba.

Wani nauyi kirjinta ya qara Mai tsanani hartaji numfashinta na Neman toshewa daqyar Anty Hafsat ta zaunar da ita suka kalleta su duka atare cikeda damuwa.

Umma yaganah ce taci gaba da cewa”

Kofa nutsu karki jawowa kanki ciwo nafada Miki bakomai bane Dan yaqara auren tunda dama ai kinsan koba yanzu ba Dole MAJEED zaiyi aure wata Rana tunda ke naki auren bawani daukansa aure kukaiba kinata shirmen sagarta da shagwaba kin kasa tsayawa kisan me kikeyi
Mahaifiyarsa kuma ba tsayawa zatayi tana kallonsa Yana garariba Babu aure ga manyanci na Neman cimmasa.

Anty Hafsat ce ya karbi zancen da cewa”

Ko ahaka dai ba komai bane Inayah
Kishiya kaman Dr farhat ai ba Zaki daga hankalinki ba tunda kinsan halinta tasan naki Kuma kaman yanda umma yaganah tace baa dauraba karki saka damuwa tun yanzu……..

Kasa riqe numfashinta dake kokawar toshewa tayi sbd maganganunsu dake fasa zuciyarta tako Ina take idanuwanta suka ringa ganar Mata duhu suna neman rufewa.

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Ke Inayah,
Inayah?
Innalillahi..

Kanta sukayi suna tarota ganin numfashinta na Neman daukewa.

Hankali tashe suka ringa kiran sunanta a rikice suna rasa abinyi Dan kowa bayason Kiran Dr farhat Musamman yanzu da Inayah din tasan abinda ke Shirin faruwa.

Waya umma yaganah ta dauka Kai tsaye takira Dr Abdul tareda sanar dashi suna zuwa asibiti yanzu da Inayah.

Cikin tashin hankalin abinda sukace yace su Kira gashinan zuwa gidan ya dubata.

Lokacinda sukai wayar Yana gida tareda mahaifiyarsa dataqi komawa tayi zamanta a Lagos dama tuntuni MJ Muhammed yafison zamanta a Lagos itace taqi Amma yanzu tunda ‘yarta na garin ta zabi Zama anan su Inna kawai ya rage ataho Mata dasu idan Abdul yaje.

Tareda umma Hadizan suka iso gidan saidai Kuma bayan sun iso suka rasa yanda zasu bawa Abdul Daman shiga har dakin umma duba Inayah gashi abbin yau ya Dan samu sauki ya fita sbd tafiya yakeson Yi ma kwanakin.

Haka dai sukai shahada tunda muharraminta ne suka basa Daman shigowa yaje ya duba Inayah din wadda sosai take neman shidewa da attack din data samu.

Dan taimakon dazai Bata yayi tafara Dan dawowa daidai saidai sbd tashin hankalin data sakawa kanta numfashinta yaqi dawowa daidai haka ya fito ya wuce sbd bazai iya ganinta a wannan hakinba Kuma yasan Inayah Bata samun attack saita Shiga wani mummunan shock na tashin hankali
Koma me akai Mata ya tabbata ya danganci Abbi sbd abinda ya shafesa ne kawai yake saka Inayah cikin tashin hankali Amma Babu abinda yake damunta harta saka arai sbd koyaushe shine kadai Mai mahimmanci agunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button