INAYAH 51-55
Yana tafiya Dole Dr farhat suka Kira bayan hankalinsu yakuma tashi da hawayen datake Babu kakkautawa cikin yanayi na daukewan numfashin.
Dama yanzu a gidan Kira kawai Dr farhat ke jira Dan haka ana kiranta jiki na rawa ta taho tana nuna damuwa a fili sosai akan meya samu Inayah din Amma Babu wanda ya fada Mata.
Zuwa Dr farhat yasa Inayah Jin wani sabon ciwo a zuciyarta tafara bori batason a dubata abarta ta mutu
Ita mutuwarma takeso ta huta…
Da mamaki suke kokarin tausarta Amma ta tibure ta dinga zuba kuka tana qin Bari ko tabata Dr farhat tayi.
Basu umma yaganah ba ita kanta Dr farhat hankalinta tashi yayi sosai tafara tunanin ko kwakwalwar Inayah tasamu matsalane?
Haj umma da batasan meyake faruwa ihu da tashin hankalin faman da akeyi da Inayah yasata fitowa bedroom dinta cikin fargaba ta iso dakin umma yaganah da aketa zuba tashin hankalin tana cewa”
Innalillahi,
Lafiya?
Meyake faruwa da ita?
Iska ne akanta?
Dama tanada iska ne kome?
Kasa magana anty Hafsat tayi sai umma yaganah ce tace”
Batada iskan komai
Kawai ciwo take takuma qi Bari a dubata sai rigima takeyi….
Mamaki sabone ya Kama Haj umma
Yanzu akan ciwo da batason a dubata take zuba wannan tashin hankalin?
Dr farhat da abin yafara Bata tsoro ganin sosai Inayah ke kuka tana daga musu hankali tace”
Kodai zaa Kira AA ne sai awuce da ita asibiti can zaa iya fin karfinta a dubata sbd tana kokawa da numfashinta dakeson daukewa Amma taqi barin na taimaka Mata.
Hankali tashe umma yaganah ta dauko wayarta ta saka Kiran MAJEED sbd ganin numfashinta yafara sama sama.
A natse ya dauki wayar tareda sallama a hankali.
Cikin kokarin daidaita muryarta ta Dan boye tashin hankalin ta sanar dashi Inayar batada lafiya sosai Kuma takasa Bari Dr farhat ta dubata numfashinta na……
Bata qarasaba taji dib alamar ya kashe ne kokuma network ne batasaniba.
Kokarin sake saka kiransa tayi taji Amma Sam Bai dagaba cikin sabon tashin hankali tace”
Inaga network nada matsalar muje da ita asibitin kawai.
Ko asibitin ma win yarda tayi atafi sbd ganin Dr farhat kawai tsananta toshe numfashinta yakeyi
Gashi zuwa lokacin ta matuqar galabaita Dan haka cikin fada sosai umma yaganah take tirsasata tashi.
Koda umman ke fada batama San me take cewaba sbd idanuwanta dake kokarin rufewa…saiga Abbin ya shigo Kai tsaye zuwa dakin umma yaganah din.
Da sauri duka suka juya suna kallonsa baka gane komai a fuskarsa Amma dukkaninsu suna iya hasaso tsananin damuwar dake ransa na ganinta hakan.
Yana shigowa Kai tsaye gurin ya nufa anty Hafsat na Kira sunanta kada ta rufe idonta.
Tana ganinsa ta maida idanuwanta akansa tana Jan numfashi cikin zafi..
Hannuwansa biyu yasa ya tallafota Kai tsaye daga kan kujera zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta cikin yanayi na kulawa sosai da damuwar meya sameta.
Daqyar taja numfashi tana tsiyayar hawaye ta bude Baki ahankali tace”
Abbi aure zakayi????
Bata fuska yayi cikeda mamakin yanda taji zancen take ransa yayi mummunan baci Amma dayake bakowa ke gane yanayinsa ba duk Basu ganeba.
Ruwan da umma yaganah ke miqowa ya karba ya Kai Mata abaki cikin sanyi yace”
Relax and breath,
Just breath,
Yawwa deep breath,
Sake Jan numfashin…
Yanda yace tayi takeyi ahankali numfashin nata na daidaituwa ahankali ahankali.
Sam taqi dagowa ta kalli kowa dakin sbd haushi da zafin kowa takeji hardasu umma yagananta.
Ganin tadan dawo hayyacinta yasashi juyowa ya kalli Dr farhat dake kallon ikon Allah Dan tasan Inayah itace mafi so da kauna a rayuwar Abbinta Kuma tasan sangarta da shagwaban Inayahn Amma Batasan yaushe tafara boriba haka kokuwa Dan Bata taba rigima bane gabanta?
Qatuwar budurwa na irin wannan tashin hankalin Amma mahaifinta ko damuwa yayi Mata ko ‘yar tsawa baiyiba saima kokarin dawo da ita daidai yakeyi cikin sanyi da nutsuwa tareda boye tashin hankalinsa na ganinta hakan.
Haj umma dake tsaye sake da Baki cikin mamakin dayafi na kullum ya Dan kalla Yana danne yanayinsa kafin ya kuma maida kallonsa kan Dr farhat Kai tsaye yace”
Dr zaki iya tafiya I can handle this,
Thank you.
Juyawa tayi ta kalli Inayah cikin kulawa ta nufeta zatai Mata magana
Inayah tayi saurin fara kokarin miqewa tana kokarin janyewa anty Hafsat ta dafeta tana kokarin tausarta kafin takuma borewa.
Ganin hakan yasa Dr farhat dakatawa tana kallon MAJEED Daya dauke Kai ba annuri ko daya a fuskarsa da duka abinda kowa yayi agidan.
Murmushin yaqe tasaki tareda yimusu sallama ta yiwa Inayah fatan samun sauki ta wuce.
Shiru ya danyi tareda sake hadiye ‘dacin ransa ya juyo ya kalli Inayah dake hawaye sosai har lokacin ta dago ta kallesa take taji wani sabon ‘daci da qunci na cika ranta matuqar Abbinta zai auri wata mace….
Tasowa tana sakin sabon kuka Zata bar dakin umma yaganah ta riqeta tana cewa”
Zan mareki idan bazaki nutsuba
Ba’ason hauka kinji ko??
Sabon kuka Mai qarfi ta saki tana cewa”
Umma yaganah bazan iya nutsuwaba Ni kubarni natafi banason ganin kowa….
Aurenma banayi na fasa bazan zauna da kowaba da Abbina…..
Sai alokacin Haj umma ta fahimci duk wannan tashin hankalin akan meye,
Takaici ne da mamaki suka tarar Mata wato duk wanna daga hankalin jama’ar gida da borin kaman me tashin iska da asthma duk akan ance MAJEED zaiyi aure ne?
Wannan halin na Inayah na shashanci Yana Bata takaici da damuwa Dan haka cikin siqewa tace”
Yanzu dama duk wannan ihun da tashin hankali dakikeyi kika daga hankalin kowa duk akan majeed zaiyi aure ne?
To so kike gabaki daya ya qare rayuwarsa gurin tattali da renonki shi Kuma bazai Gina tasa rayuwarba?
Da Ina tareda shi tunima dayayi auren Dan bazai zauna saidai yaga ‘yaya wasu na tarawaba shine zakizo kina shirmen ihun kuka da……
Cikin kuka Inayah tace”
Ni nace bazan Tara Masa ‘yayan bane?
Ai Nima Zan Haifa Masa idan kika barmu…
Fiddo idanuwa Haj umma tayi cikeda mamaki,
Su umma yaganah da Anty Hafsat ma tsit sukai yau ciwon bakin Inayah yayi musu Dadi duk da duk kunya ta kamasu da sauri umma yaganah ta buge Mata bakin sbd karta qarasa.
Shi kansa abbin kasa magana yayi sbd mamakin bakin Inayah Daya Gama wuce tunaninsa hakama da bacin ran zancen dasuka sanar Mata da wani abin yasameta ayau acikinsu babu Mai abin fada masa sun kashe Masa ‘ya ko me??
Numfashi ya sauke a boye Yana sake kawar da bacin ransa ya kalli Haj umma dake kallonsa jiran abinda zai fada sbd duk suna iya hango zallar bacin ransa duk da boyewar dayake kuwa.
Daidaita kalamansa yayi cikin nutsuwa yace”
Umma Ina dauka maganar auren Dr farhat bamu gama meyasa zaku dagawa Inayah hankali da zancen bayan bawai Kai karshen maganar akayiba.
Umma yaganah da Anty Hafsat ya kalla suma yace”
Meyasa zaku sanar da ita umma tunda kinsan halinta
Yanzu gashi tana neman illata kanta akan hakan,
Maganar aurena da Dr farhat Kar akuma tadasa a gabanta sbd ba……..
Maganarsa tasa Inayah fashewa da sabon kuka tareda juyawa da gudu tabar wajen tana cewa”
Kenan yin auren zaiyi da Dr farhat.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/9, 11:49 AM] +234 816 828 4180: 53
Arewabooks@Mamuhgee
Rintse idanuwansa dasuka Dan sauya yayi tareda juyawa yabar gurin shima Yana kansa na Kuma sarawa dama gashi kwana biyun Yana fama da ciwon kan.