INAYAH 51-55

Inayah takasa gane abinda yasa yake kaucewa wannan kuruciyantata,
Maganar auren kowa ba Dr farhat kawaiba shi kansa yasan kaman ya haramta garesane sbd bazai taba iya hada kaunar Inayah da kowa da komaiba saidai Kuma bazai iya kusantartaba a miji sbd tausayinta da ganin rashin qwarinta Dan haryanzu ‘yar Babynsa yake kallonta.
Shiryawa yayi cikin Kaya marasa nauyi yayi zamansa daki tareda Dan Shan maganin ciwon kan ya kwanta idanuwansa a lumshe saidai zaiyi wuya idan zai iya baccin.
Ahakan akai azahar ya tashi ya fita sallah daga can ya fita zuwa wani gurin.
Itama bayan fitar Abbinta bacci tasamu ya dauketa zuciyarta mamaye da farin ciki.
Sai Bayan azahar ta farka lokacin jikinta yayi Dan qwari Kuma zazzabin ya saukar Mata gaba daya sbd allurar da akai Mata da damuwarta data fita ranta sbd dama rayuwarta Inayah bamai riqo bace sbd tun farko haryanzu idanba qaddarar rashin aurenta da ake fasawa batada damuwa komai saita rashin uwa wadda umma yaganah ta cike wannan gurbin tuni barema gurbine da Abbinta Bai bar filiba yacikesa sbd farin cikinta.
Wanka takuma Yi ta fito ta sanya doguwar Riga har qasa amm ko yanzu Mara kauri da nauyi.
Sallah tayi tana gamawa zubbi takawo Mata shayi Mai zafi da white couscous da kidney sauce.
Umma yaganah ce da Anty Hafsat data zo suka ringa Dan lallabata da fira taci abincin bayan Tasha tea din sosai.
Ganin duk sun damu yasata kallonsu cikin sanyi da shagwaba tace”
Umma yaganah kiyi hakuri bazan sakeba,
Anty Hafsat I’m sorry.
Murmushi Anty Hafsat tayi tana cewa”
Ni daidai kikamun ba gashi yanzu zaa taqaita Mana zancen aure auren nanba ana zaune kalau
Inayarmu ko baby ko daya Bata haifawa Abbinta ba wata zatazo ta rigata”
Eh fa Anty Hafsat kiji fa Dan Allah,
Ni wlh nafadawa abbi bazan yardaba nice Zan Haifa Masa yaran da Haj umman keso..
Umma yaganah da mamaki sabo duk da sun saba da bakin Inayah Amma kusan mamakin baya denuwa tace”
Yanzu Inayah haka kika fadawa MAJEED kece Zaki Haifa Masa ‘yayan?
Dan gidanku ta Yaya Zaki Haifa Masa ‘yayan Baki Gama sanin ciwon kankiba kina wannan zubar
Kizo gaban ‘yayan ma kinayi.
Cikin dariya anty Hafsat tace”
Umma yaganah tsaf kuwa Zata Haifa Miki abokan Hira inshallah Nan kusama.
Ahankali tana sanar kallon umma sbd kada ta buge Mata Baki tace”
Inshallah anty Hafsat.
Harara umma tabita dashi tana amsa Kiran umma Hadiza da tun jiya dasuka tafi.
Bawa Inayah wayar tayi sukai magana taji Inayah din ba lefi ta warware sukai sallama tana sake Mata fatan sauki cikin tsananin kauna da kulawa.
Dakin umma yaganah suka koma acan ta kwanta
Haj umma ma tasake zuwa ta dubata,
Anty Hafsat ce ta zauna ta ringa koro Mata bayanai tareda qarasa juya kan Inayah din akan idan ba samun ciki tayiba Haj umma bazatabar maganar auren Nan na AA MAJEED ba…
Hankalin Inayah kasuwa biyu yayi sbd a bakine kawai take fadar cikin Amma cikin ranta tsoro da fargaba takeji na haihuwar sbd tana ganin yanda Mata me haihuwa abin na daga hankalinta.
Juyar Mata da tunani anty Hafsat tayi ta dena kallon wuyar haihuwar sai fashin auren abbin kawai duk da yace Mata baice zaiyiba Amma idan Haj umma ta nace tasan zaiyi.
Anty Hafsat Bata bar gidanba sai bayan ishai,
Bayan ta wuce daki Inayah Takoma bayan taci abinci kadan sbd zazzabin Daya fara dawo mata,
Kasa wanka tayi sbd sanyin datakeji dan haka kayan bacci ya sanya Riga da Wanda masu kauri sosai na Fendi.
Tana kwanciya ta rufa jikinta na qara zafi.
Wayarta ta lalubo ta dauka tareda Nemo numbern Abbi tasaka Kira..
Ringing tayita Yi Bai daukaba Dan haka ta ajiye wayar tareda tashi zaune ta ziro qafafunta ta sauko gadon ta saka slippers ta nufi kofa sbd damuwar ko shima ciwon kansa yayi tsanani ne.
Kowa ya shige Dan haka Kai tsaye palonsa ya nufa tareda budewa ta shiga tana sake saka Kiran wayarsa sbd baya palon tv ce kawai ke aiki ba murya ko kadan sai AC da sanyayyan kamshin turarensa Daya gauraya Dana humidifier dake aiki.
Sake saka Kiran wayarsa tayi saiga wayar na ringin a palon ahankali sbd bayason qarar waya shiyasa yawanci wayoyinsa a silent suke.
Wanka ya fito daureda blue towel yaji dan ringing din wayarsa a Palo
Ya Dan yamutsa fuskarsa ya nufi palon sbd baisan waye zaikirasa a wannan lokacinba kusan 11 na dare.
Yana fitowa wayar na katsewa Inayah Kuma na dagowa…..
Faduwa gabanta yayi da qarfi ganin Abbinta daureda towel a Karo na farko rayuwarta….
Lafiyayyar fatarsa da Lafiyayyan jikinsa Dayake bayyanarda qarfinsa ta kalla zuwa fuskarsa taji gabanta yakuma faduwa Amma Kuma zuciyarta garesa take ingizata sbd fuskarsa kawai ta bayyanarda gajiyarsa.
Kallonta yayi Yana Dan kame fuska ya qaraso ya miqa Mata hannu ta basa wayarsa data dauka.
Bata fuska tayi tana kalar tausayi sbd ganin ya kame fuska lokaci daya.
Kasa miqa Masa wayar tayi tareda sanyaya murya tace”
Abbi na dauka bakada lafiyar ne Naga baka fito kaci abinciba kuma…..
Ringing wayarsa Dake hannunta ne ya datse maganarta ta dago wayar atare sukaga sunan Dr farhat baro baro akan wayar.
Wani bugawa kirjinta yayi take idanuwanta suka ciko da hawaye ta dago ta kalla Abbin Wanda shima mamakin Kiran Dr farhat din ya kamasa Amma Bai nunaba sbd ganin halinda Inayah take kokarin shiga qafafunta tuni suka fara rawa hawayenta suka gangaro ta saki wayar qasa tareda juyawa Zata gudu tabar gurin cikin kuka me tsanani…
Ko takun gudu biyu bataiba ya riqota da sauri Yana Kiran sunanta cikin yanayi na son hanata daga hankalinta sbd sanin daga hankalin kowa gidan dazata iya yanzu ta tada kowa da rigimarta.
Qwacewa takeyi hawaye nabin fuskarta tana cewa”
Ni Abbi kabarni banason ganinka kaje ka dauki wayarta….
Sosai take Rigimar kwacewa taqi yarda ta tsaya ta sauraresa sai kokarin dawo da ita nutsuwarta yakeyi Yana Kiran sunanta Amma taqi.
Jikinta ya sanyata tareda rungumeta Yana cewa”
Ya isa,
Ya Isa,
nace ya Mana
Ba daukan kiranta zanyiba,
Banma San meyasa ta kiraba at this hour….
Aurenta zakayi shiyasa ta Kira Ni kabarni Abbi zuciyata mutuwa zatayi kawai….
Cikin daga murya da tashin hankalin datake neman sakasa yace”
Na fada Miki ba aurenta zanyiba can you shut up and stop being childish.
Dakatawa tayi tareda yin shiru ahankali ta dago daga jikinsa ta kallesa da idanuwanta dake kaca kaca da hawaye ahankali tace”
Da gaske Abbi bazaka auretaba?
Wani numfashi ya sauke tareda juyar da Kai cikin kosawa kafin yadawo da kallonsa kan kyakkyawar fuskarta Yana kallonta da idanuwansa dake cikeda wahalalliyar kaunarta dake wujijjiga rayuwarsa Bai iya cewa komaiba sai rintse idanuwansa da yayi Yana Kai hannu zai janyeta jikinsa ta girgiza Kai tareda sake shige Masa hannuwanta na sake zagaye jikinsa da Babu Kaya sai towel.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/10, 6:01 PM] +234 703 623 7917: 55
Arewabooks@Mamuhgee
Daqyar ya iya bude Baki ahankali can qasan maqoshi yace”
Nace ki Dena maganan Nan…..
Sanyi yaji cikin ranta tareda sake kwantar da kanta kirjinsa Qamshin shower gel dinsa na shiga hancinta..