ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Mutane sukayi Tsuru suna kallon kallo,share hawayenta Goggo tayi kan tace”Acigaba da shagalin biki,babu komai..’Tafada kafin ta koma cikin daki,madina da Mardiyya suka kalli juna,suna fatan Allah sa lafiya,  *RAMATU* kuwa da diyarta Shalelenta *AZEEZA* Suka kalli juna cikin sonyi gulma ammh babu dama,Ramatu ce keta kunshe dariyarta tanama diyar tata sigina da ido,suna kallon dakin da goggo ta shiga suna Dariya kasa kasa…

_*Topha,kunji fa yadda Abun yake,kanku ya daure,kun samu rashin Fahimta ko? Hhhhhhh haka janafty tace kowani book dinta tafe yake dawani salo na dabam,kuna so,kuna bukata,to cike Tagging dinki da HOT COMMENTS ..”Nikuma zan himmatu da kokari wajen baku update..Oneluvs Janaf fans*_

          #Comment,share and vote#

          #Janafty…..#

*ALIYU GADANGA..!*

   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12

*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH…,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????,Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer’s asso*✏

_Dis NOVEL is not for sale,plz masu bina pc suna tambaya na siyarwane,nawa zasu biya suyi Rigister,So Cool ur mine Aliyu Gadanga is a special gift to my Real Dota RAHMA????and my mommah shiyasa yazama Free,what are  u  eating na baka is zubowa kasa,????Na kudinfa na nan tafe,tunda naga da gaske kuke u what me to become HAJIYA JAMI????Tanque very much my Real Fans,and a big Tanque to does prople for dere hot comments,Love u Tin Tin????????_

*NOT EDITED*????

*Chapter2*

    “””Gidan bikin sai yakoma gidan gulma da tsegumi,sai cecekuce akeyi kunsan mutananmu,sufa basu raina Abun gulma balle wannan dasuke jiran kiris,itako goggo tana daki tana kuka duk lokacin Data tuna kalaman Aliyu saitaji kuka na kawomata,madina ne ta shigo dakin taga halin datake ciki,ita takira mardiya suka zo suna ta bata baki,nan nema take fadamusu Abunda ya faru,dafe kai madina tayi kan tace”Oh mardiya,mutane ba kyau,to ai Shikenan Allah ma ya sakamai da wacce tafi figaggiyar ni”imar ma,don Azeema tafita komai,uwa uba ga hankali da tarbiya”

mardiya tace”Kwarai ma ko goggo,kibar damun kanki,donta Captain ne,lokaci kadan ne,zai warware..”Suka fada suna kokarin kwantar mata da hankali,dakyar tayi shuru kafin ta wanko idonta ta fito kamar ba ita ba,Ramatu ko da Aziza sunyi iya yinsu su Fahimci meke faruwa ammh Basu samu dama ba,shiyasa suka kara gyara zama har sauran tawagan Daurin Auren su dawo kila sasamu wani lbrin daga barayinsu,duk da tasan mallam ko zata mutu bazai fadamata ba,tunda yace tana da rariyan baki..

*****************

  Ni’imatullahi tana zaune cikin kaawayenta acikin Shiga ta alfarma sanye take dawani ubansu material mai tsada da yarari black and red an mata wani Fitinanne Dinki ajikinsa kanta kuma an dauremata shi da head baki,fuskarta cikin makeup mai kyau da tsari,Ni”ima gajera ce,bata da tswao ammh tana  da kyau sosai domin Farace sosai mai dauke da faffadan Fuska tare da dogon hancinta,tana da jikin mata babu laifi kam ko”ina ya cika,kallo daya zakamata kasan ta fito daga gidan hutu,saboda yadda fatar jikinta ya tsumu ajin dadi,kallon idonta kawai zakayi kafahimci tana da mugun wayewa da budewar idon yan matan zamani sakamakon kaf bayan Primary bata hallarci wata mkranta a Nigeria ba,kasar waje tayi rabi da kwatan Rayuwarta.

Cikakkun kawayenta yan Duniya ya”yan masu dashi,harda diyat gwaannar jahar gwambe mai ci alokacin Falon dai cike da yan gayu na bugawa ajarida,sai shewa ake ana zolayan Ni’ima da fadin Anrigaya da an Dauramata aure Da Captain din nata,kamar yadda take kiranshi,itako sai wani Smiling take,tana wani washe hakoran jin dadi,duk sanda suka ambaci an Daura mata aure da captain dinta,suna cikin wannan Halin ne,wayarta kirar Samsumg gallezy tadauki kara cikin wakan nan U ARE MY LIFE..”Da hanzari ta sanya hannu ta jawota dama tana kusa da itane, LOVELY MUNARI…”Tagani dan tsaki taja don azatonta angon natane Kawartace babbar aminiyarta ma kuwa,wacce fitanta kenan daga falon ta sauka kasa zatayi mgana Da MAMINTA.

Dagawa tayi tana fadin”Ya how far…? Cikin wata murya Munari tace”Swhrt ki sauko kasa yanzu don Allah..”Sororo Ni”ima tayi kan tace”In sauko kasa kuma?uban me zanyi miki in na sauko,kinfa san yanzu matar Aurece ni,so taku daya in zanyi sai da izini in ba haka ba,in Shiga cikin Fushin Allah..”Tafada cikin nuna iya gaskiyarta kenan,Kai munari takama tana kallon yadda falon ya hargitse tun Shigowar Abbah falon da lbrin da suka zo dashi tace”Oh my God..Swhrt kibar mganar nan,ki sauko kiji..”

  Tsaki Ni’ima taja kan tace”mtsewww…Bazan sauko ba,in bazaki fadi Abunda ke bakinki ba to rike kayanki,sai kin hauro..”Tafada tana kokarin yanke kiran”Ajiyar zuciya munari tayi kan tace”Yanzu su Abbah suka dawo..,”Da hanzari Ni”ima ta daga tsalle tace”Da gaske,shikenan na zama matar Aliyuna,plz Friend kutayani murna na zama matar my Captain..”Tafada tana dariya gabadaya falon suka saka mata ihu da tafi,Munari ta dafe kai kan tace”Ke baki da hankali wlh,baki iya tsayawa kiji zence,ba to Abunda nakeso na fadamiki su Abbah sun dawo kuma ba”a Daura Auren ba..”

  Wani Abu mai Nauyi Ni”ima taji ya tsaya bisa kirjinta cikin wani yanayi tace”ban…ga..ne…ba..?”Tafada cikin rawan murya Munari tace”Haka Abbah yace,an fadamiki an dakatar da Daurin Auren sakamakon haryanzu ba”a ga wani daga dangin mahaifin Aliyu ba,shiyasa Abbah yace bazaya bada Aurenki ga wanda ya tashi gaban mace ba,wanda haryanzu ba”a san asalinsa ba.”Ihu kawai Ni”ima ta yanka ko kafin ayi wani Abu ta zube kasa Warwas bata numfashi da gudu kawayenta suka rufu kanta suna Kiran sunanta da hanzari wasu sukayi kasa suka kira mami,wanda tanajin Abunda ya faru ta dora hannu akai,tana fadin”Na Shiga uku ni Hadiza,dama sai da nafada kwamishina wlh Ni”ima bazata iya rayuwa babu Aliyu ba,kada yayi haka,kada ya aikata haka,to gashinan dai Ga Abunda nake gudun  nan ya faru..”

  Take ta fada tana,kuka,kwamishana na gidan da hanzari aka tarairayeta aka wuce da ita asibiti ba yarda take,ai sai gidan biki yakoma gidan kuka,da gulmagulmace,tuni kawayen Ni”ima suka kama gabansu Munera ce kadai wacce da ita aka tafi asibitin, *FEDERAL TEACHING HOSPITAL GOMBE*kowa yaji ba”a Daura aure ba,sai ya Shiga mamaki yana neman jin dalili,Kafin kaceme gida ya watse sai mutanen daba”a rasa ba,wanda dama sun kasance Shakikai ne,ga kwamishina din da kuma Mami Hajiya hadiza.

Wannan kenan

________________

Sai da Su Kawu suka gama sallaman bakinsu kafin su yi ayari Shida tawagarsa da tawagar angon suka nufi gidansu Aliyun,don kawu yace Sauri yakeyi yau din yakeso yakoma Kaduna,har cikin suka shiga suna gaisawa da mutane Hajiya Umaima mata ga kawu Bala wacce suka kira Da Umma ita ta fito tana fadin”Abban Haisam wai meke faruwa ne? Tundazu goggon yara ke kuka,ga Captain chan ya dawo yana wasu maganganu don Allah wai meke faruwa ne? 

Dan mirmishi kawu yayi kafin yace”Bakomai Umaima mushiga daga ciki,mallam Shigo kaima don Allah..”jin haka sai gabadayansu suka dumguma zuwa cikin dakin,Ramatu da Aziza jikinsu haryana kyarma suka rufamusu baya,saboda suna so suji kwakwam,Suna Shiga kawu yasa baki ya kira Gaggo ta fito tana musu sannu da zuwa,Kallonta yayi kan yace”Suwaiba meyasa haka? don Allah kiyi kokarin danne damuwarki,domin kibawa Aliyu kwarin gwiwa,bafa wani Abu dama Allah ya kaddara Ni”ima ba matar Aliyu bace Azeema ce matarsa..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button