ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

  Da hanzari Hajiya Umaima tace”Bangane ba,da wata Azeema aka Daura aure..’?Kai tsaye yace mata”Diyar mallam lawal,shi ya taimakemu ya fitar damu kunya,da bamusan ya zamuyi da tarin jama”ar damuka tara ba..”Ramatu dake gefe ta zaburo tana fadin”Da wata diyar mallam lawal din aka Daura Aure? badai Diyata bako? na Shiga uku ni Ramatu kowa na raba kanshi da hada zuru”a da mugun iri wanda ba”a son Asalinshi ba,ammh kai…”Ke Ramatu..”Mallam lawal ya katseta cikin Fushi yace”Dake ake mgana,wlh zan mugun sabamiki matukar nakarajin bakin ki cikin wannan mganar,Ba da yarki dakike kirarin itace taki na Aurama Aliyu ba,da Diyar kwarai wacce batagaji tsiya ba na basa AZEEMA..”Da hanzari Aziza ta dago tana kallon mahaifinta lokaci daya taji wani Abu ua tsaya mata bisa kokon rai tun lokacin dataji anfara mganar an Daurama Aliyu Aure kamar kunninta sai yajiyemata kamar Sunanta ake ambata da an Daura mata aure da Aliyu,alokacin wani farinciki ya mamayeta domin tunda tataso anguwa daya Da Yaya captain amtsayinsu na makota takamu da matsanancin sonsa,duk duniya kowani Namiji abanza take kallonsa,babu wanda takeso da buri yazama mallakinta irin Yaya captain koda take wani Abun,saboda Ramatu ne,karta fahimci inda ta dosa,ammh sai kuma gashi Mahaifinta yakira Sunan Azeema amtsayin wacce aka Daurama Aure da Yaya Captain dinta,lokaci daya taji jiri na neman kwasheta,sai da tarike hannun Ramatu kamkam tana rintse ido.

Ramatu ta mike tana fadin”Oho yanzu naji mgana Ai wlh da da yatace yanzu nan zaku warware aure nan domin bazan hada irin da Da”n mace ba mara asali ..”Fita kibama mutane waje sakarya mara tunani..”mallam lawal ya katseta yana nunamata kofa Hannun yarta taja wacce ke wani hali tace”Ko bakace ba, zamu tafi,ammh dai an Fadi ba Nauyi kuma duk  wanda yahau motar kwadayi karshensa Tashar Wulakanci..”Tafada suna Ficewa.

Ajiyar Zuciya mallam lawal ya Sauke yanajin wani kunya tare da bakin ciki suna dirar mai lokaci daya dakyar ya iya cewa”Don Allah kuyi hakuri da maganganunta haka take sam bata da Tunani wani lokaci..”Mirmishin yake Goggo tayi kan tace”Bakomai mallam lawal Ai ba yau nake tare da Ramatu ba,ai yakamata nasan hallayanta babu komai kadaina biyemata don Allah,mungode sosai Allah ya saka da alheri bazan manta karamcinka garemu ba,ni da gadanga tun zuwana garin nan kake dawainiya dani,tare da gadanga saboda haka Allah ne,kadai zai biyaka Alherinka garemu..”Takarishe kamar zatayi kuka gabadaya suka shiga bata hakuri,nan kawu bala yace su tattaro suzo su koma gida tunda dai biki ya tashi nan akayi mganar tarewar ita Azeema ammh sai kawu yace abari nan da wani lokaci saboda Samun natsuwar Shi Aliyun,shima mallam lawal din yayi na”am da hakan saboda itama Azeeman yanzu take SS1 a babbar sakandiri,Goggo dai bataso ba,taso kawai Azeemar tatare a shashin da Aliyun ya gyarama Ni”ima,tunda nan zata fara zama,kafin yakoma wajen aiki chan kaduna su tafi tare,ammh babu yarda ta iya,domin bata iya tsallake Umarnin yayanta.

Haisam ne zai bi Su Ummah yakoma gida,domin sunyi sunyi Aliyun ya bude kofa yaki,Ran maza fa ya baci Dole yayi sallama da Jabir yabi su Ummh suka damki hanyar kaduna,dashi dasu madina da mardiya,Jabir kadai aka bari,Sai gobe Sunday zai koma Tunda monday akwai aiki,Dakin Goggo yakoma sukacigaba da tattaunawa akan Batun goggo tana nunamai ita tafi jin dadin wannan Auren,domin dama AZEEMAR yar dakinta ne,nan take komai nata ko kafin ma ayi hakan,shi kanshi Jabir sai yaji zuciyarshi tafi Natsuwa da Azeema domin ya santa sosai yarinyace mai hankali da natsuwa gata da ladabi da biyayyah bata da hayaniya ko kadan,Aliyu dai yana daki kwance,so yake yayi kuka ammh yakasa idanunsa ne,suka kada sukayi jajir,jijiyoyinsa kansa suka fito radau,Lokaci bayan lokaci sai ya naushi hannunsa da bango,goggo ko batabi ta kansa, ba saboda tasan halin dan kayanta,Aliyu gadanga zuciyarsa kamar kuturu in yatashi tsiyarsa sai tafita yammah da hankalinsa kafin suke komawa su daidaita.

**************

Azeema Atsorace takoma gida,tayi zaune cikin dakinsu tana sauke ajiyar zuciya data rufe ido tsawar da Yaya Captain yadakamata ke dawomata,sai tawani zabura kamar yanzu Abun ke faruwa,Ganin bata da mafitane yasata tamike tadauki tsintsiya ta share dan tsakar gidan nasu,domin tasani inda inna ta dawo ta tarar da ita batayi ba,sai na lahira yafita jin dadi,ta gama sharan kenan ta kwaso duka kwanukan wanke wanken duka gidan,amadafi tazo wajen wanken wanken nasu ta zube takarisa gindin rijiya ta zura guga ta dinga jawo ruwa sai da tacika botikai hudu,biyu takai Madafi,biyu kuma ta dauki kujera ta kada klin,tafara wanke wanke,tafara kenan taji shigowar inna Da Aziza,ta dago ido tana kallonsu lokaci daya tana fadin”Sannunku da zuwa…”

Inna Ramatu ta kalleta tana hararanta tace”Ke keda sannu,Tunda ubanki ya kashe miki rayuwa ya aura miki wanda ba”asan asalinsa ba,uwa uba gashi mara tarbiya,…”Da hanzari Azeema ta dago tana kallonta gabanta yana faduwa ta bude baki zatayi mgana kenan Aziza tazo ta wuce ta gabanta fuu ta bangajeta harsaida ta Fado daga kan kujeran datake kai,da kallo tabita harta shige daki,kwallah ta tarun mata a ido ta dago tana kallon Inna Ramatu tana fadin”Inna kinga Aziza ko? Tsaki Inna Ramatu taja kan tace”yo in na ganta mezan mata,dakika ga zata wuce meyahana ki kauce ki bata hanya,ai ke da mahaifinki Kwadayi zai kasheku don nasan kwadayin Abun Duniyane yasa ya bada Aurenki ga Dan mace nan…”Da hanzari Azeema ta mike tana fadin”Ni..Ni..Kuma ba.. ba…”Eh dake fa,saboda kwadayin Abun Duniya iyayan wanchan yarinyar sunce bazasu bashi yarsu ba,saboda ba”a san asalin dangin mahaifinsa ba,ammh dayake shashashan uba gareki wanda zuciyarsa tarigaya ta mutu ya daukeki yabada ke,ban damu ba,tunda kece Tunda kema zuciyarki irin ta ubanki ne,da dai yayi karambanin Auramasa Aziza wlh da anyi yakin Duniya na uku..”Tafada lokaci daya tana Shigewa daki,da wani kallo Azeema tabita kafin ta dafe kanta tana hada maganganun Innar in kunnenta yajiyemata Daidai kamar da ita taji inna na fadin A Dauran mata Aure da Yaya Captain,Saurin Dafe kirji tayi tana karanto Duk addu”ar datazo daga bakinta lokaci daya idanunta na zubo da kwallah,runtse ido tayi tana tuna yadda basu shiri sam da yaya captain saboda halinsa na rashin sakin Fuska da walwala uwa uba mugunta yaya captain baya da wasa kwatakwata ko asojojin shi na dabam, ne,nan da nan ta tuna karonsu na dazu,sai jikinta yahau rawa kasa karisa wanke wanke tayi,sai ta wuf ta wanke hannuwanta tafada dan karamin dakinsu gefen katifa ta zauna ta zabga tagumi tanajin kewar mahaifiyarta,domin da”a ce yau mahafiyarta na raye,da kila ta samu kafadan dazatayi kuka,ta lallasheta,ammh yanzu bata da kowa sai Mahaifinta,wanda kuma komai daga barayinsa ya fito,Har abada bazata taba bata kanta ba,bakuma zata watsama Mahaifinta kasa a idoba,duk duniya bata da wanda ya fishi,Share hawayenta tayi kafin tafice takoma ta cigaba da wanke wankenta lokaci bayan lokaci tana kallon dakin inna Ramatu tana share kwallah…

           #Comment,share and vote#

            #Janafty#

  *ALIYU GADANGA..!*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button