ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Shekaran Fatima daya da Rasuwa yan”uwan Mallam lawal suka matsamai sai ya kara aure zama hakan bai yuyuwa,Dole tasa ya sake aure da wata yar saman layin dasuke RAMATU,Ramatu Mai awara ne Sunanta saboda awara take soyawa akofar gidansu tana yawan zuwa wajen mallam lawal siyan kayan miya shiyasa suka saba,Ramatu bazawarace tayi aure Allah yayima mijinta rasuwa,ammh bata haihu ba,Ramatu bata da uwa bata d uba,ahannun kakarta take,gabadaya rayuwarta tataso babu kwaba ne,ballatana tsawawartawa,Komai taga dama shi takeyi babu ruwanta,tunkan Auren ta na farko idonta yake abude,irin matanan ne marasa mutumci,da kamun kai,gata bata da kunya sam,ko mallam lawal din ita fara nunamai alamun so,don haka zata dinga aikamai da awara ko yabata kudi bata amsa,da taganshi zata hau sunne kai kamar munafuka,Ko lokacin dayazo da izinin neman amincewarta batayi gaddama ba Ta amince ko wata ba”ayi ba aka Daura aure tatare agidan mijinta,adakin dake gefen na fatima,dayake gidan,gidan laka ne,dan karami mai dakuna biyu da kichen sai dan filin tsakar gida,sai rijiya dake gefe,gidan babu siminti sai dai tarin kasa,ammh dayake lokacin Fatima nada kokarin tsabtaceshi shiyasa sai kasan ta kwanta kamar an daddadeta,.Satinsu biyu suna cin amarci kamar Abun arziki ammh daga Ranar da mallam Lawal ya fadamata zai dauko Azeema ya kawomata ranar basuyi barci ba,don Ramatu cewa tayi bazata rike diyar da bana nata ba wlh,shikuma yace bata isa ba,gata kuwa bazai barma Baba Ade wahala ba,dole tanaji tana gani ya tattarro Azeema ya dawo da ita gidan da zama,Suwaiba bataso haka ba,domin tuni taji lbrin Ramatu bata da mutumci sam,kuma tasani cewa Azeema bazataji dadin zama da ita ba.

Illai kuwa Domin Tunda Azeema tadawo hannu Ramatu take gana mata azaba,duk da karancin shekarunta domin lokacin tana da shekara biyar ne aduniya tayi girma dayake tana da tsawo,gabadaya aikin gidan nan ita keyinshi,da gari ya waye zata jawo ruwa tacika duka botikan gidan,kafin tazo tayi shara,tare gidan gabadaya takoma dakin mahaifiyarta inda yazama wajen kwananta ayanzu,bayan nan takoma kichen ta hura wuta ta sanya ruwan koko ta dama,ta zubama Babanta da inna Ramatu,kuma bata da ikon sha sai Ramatu taga dama,da kananan shekarunta tasaba da wanki na Ramatu da Babanta duk ita ke wankesu,Mallam lawal baya da yadda zaiyi domin kamar Ramatu tafi karfinsa ne,domin yana mgana zata tasomai kamar zata dakeshi,baya da yadda zaiyi sai ya dinga bama Azeema Hakuri,itako ko afuska bata nuna,bataso mahaifinta ya shiga damuwa saboda ita.

  wajen datake samun sauki guda biyu,daga gidan Baba Ade sai wajen Suwaiba,wanda tazama tamkar mahaifiyarta,Ramatu tunda ta lura Azeema najin dadi in taje gidan Suwaiba sai ta hanata zuwa,inko taje asace Ranar sai ta kusa kasheta,ko wani Abun amfani Suwaiba tabata to Ramatu zata kwace ta saida,da Suwaiba ta fahimci haka sai ta daina bata sai dai in zatayi amfani dashi taje gidan Suwaiban da Dauka,Suwaiba da hannunta ta sanya Azeema amkaranta awata mkrana dake nan garin gombe G.D.S.S.S GOVERMENT DAY SCIENCES SECONDARY SCHOOL GOMBE,mkrantace mai kyan gaske,saboda tana hade da private ce,sakamakon mkrantar ta masu dashi ne,Tana nan a Federal Lowcost layin ministery of Agric,wanda Ramatu bataso Azeema tashiga mkranta ba,taso tayi ta zama tana mata bauta,ammh sai wannan karan,Mallam lawal ya nunamata bata isa ba,harda islamiya Suwaiba ta sakata,karfe hudu zuwa Shida na yammah asabar da lahadi kuma ta sanyata hadda,wanda in tadawo take zuwa Suwaiban na kara biyamata karatun,wannan dalilin shi yadan samama Azeema salama da takuran Ramatu,duk da haryanzu bata daukemata kowani aiki ba,sai tayi shi kafin tatafi mkranta.

Ramatu nada wata uku da zuwa gidan tasamu ciki,shikenan sai Tsurfa da iyayi ya shigo ciki,Allah ne ma yasa za”a haifi jikin lafiya ta haifi yarta mace mai kama da ita,kuwa Ranar suna lawal ya sakama yarinya suna AZIZA tunda Ramatu ta haihu Azeema ke wahala da ita da yarta,Ko duba kankatarta batayi kamar jaka,itace cin kashin Aziza da cin Fitsarinta,kullum zaka ganta goye da Aziza ko itace uwarta sai haka,Haka Rayuwa tacigaba da tafiya da dadi babu dadi,Azeema na girma kullum wahalarta na karu,bata da wajen jin dadi sai wajen suwaiba,wanda haryanzu Aliyu bai dawo ba,yana chan kaduna wajen Kawu bala,sai dai yana Zuwa lokaci bayan lokaci.

  Aziza tafi Azeema jikin girma domin tana shekara goma kamar yar sha biyar,saboda tana da girman gabba,shekaru Biyar ne kwarara tsakaninta da Azeema ammh in kuka ga yadda takema Azeema zakuyi zaton kanwartace takusan ukuma,saboda yadda ta rainata ko agaban waye haka zata dakamata tsawa kamar tsaranta,itako Azeema bata da hayaniya ga hakuri da kawaichi,shiyasa kotayimata wani Abu bata daukan mataki sai dai tafadama Ramatu wacce suke kira da Inna,ammh daga karshe in ma batayi wasa ba ita zataci duka,Gabadaya Ramatu ta lalata Aziza domin ta danneta ta damata arashin kunya da Rashin mutumci,kullum cikin yima yan anguwa take,Azeema bata iya yima Aziza komai saboda tarigaya data raina ta,ko wankinta ita kemata har kuma yanzu ita ke aikin komai agidan,Aziza bata kauda kara suna zaune ita da mahaifiyarta sai dai ta dafa ta basu suci suna zaginta,mallam lawal bai da katabus saboda Ramatu ta zamarmai matar jaraba,har gwara ita Aziza in yayimata mgana tanaji Tunda tasan halinshi bayamata da wasa yanzu jikinta sai ya fadamata,Duk da tanajin Haushinsa acewarta yafi son Azeema akanta,dakuma hudubar mahaifiyarta,Aziza irin yaran nan ne masu shegen kwadayi,tunda ta lura da Abun arzikin da Suwaiba kema Azeema sai takoma shisshigema Suwaiba,ammh sai bata,bata Fuska ba saboda bata mu”amala da yaro mara kunya,uwa uba kuma basu shiri da Ramatu saboda rashin da”anta da kuma yadda take muguntama Azeemar.

    

Suwaiba saboda kar ace tayi sonkai,sai ta sanya Aziza A mkarantar da Azeema keyi,tare da islamiya ammh duk da haka baisa tafita daga bakin Ramatu ba,kullum bata da Abun zagi sai ita,tanabi gidan suna gidan biki tana fadin tana zaman kanta,don ko danta data haifa ba”a san asalin fa,bashi da uba,kilama dan gaba da Fatiha ne,itako Suwaiba kotakan Ramatu batabi saboda ta fahimci jahalici ke damun Ramatun shiyasa,Azeema kuwa tun bayan barin Aliyu gidan batakara sakashi a idonta ba,wani lokacin ko yazo tana gida tana fama da aiki,kuma baya kwana suke juyawa,Ranar dayazo yakwana itakuma tatafi gidan Baba Ade ta kwana tana dawowa goggo ta ce mata yanzu su gadanga suka koma kaduna,sai dai ta ciji yatsa ammh tana so taga yaya Aliyu taga Shin yakara girma ko yananan yadda yake,yanzu yana fara”a kokuwa haryanzu fuskarnan tasa ba Rahama.

   

Shiko Aliyu suna kammallah Command sch Haisam ya tafi BUK KANO yana karantar Accounting,ayayinda Aliyu ya fada ABU ZARIA yana karantar Scicology,yaso yatafi NDA ammh sai Kawu bala yace yafara hada Digerinsa First kafin yatafi,Akuma lokacin ne gwannatin datahau mulki ta bayyana Sunan Kawu bala amtsayin Kwamishinar yada lbari ta jahar kaduna,Babu laifi kawu bala yatara Abun Duniya domin yana gudanar da kasuwancinsa bayan aikin gwannatin,kuma haryanzu yana karantama  gidan radio Nageria kaduna lbrin Turanci da fassaransu na hausa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button