ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

   _(The Story of yuong soldier man)_

Wattpad:Janafnancy12

*Hakkin mallaka:Janaf*

*DEDICATED TO MY MOMMAH..,HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent writer’s asso*✏

*Chapter3*

        *ASALIN TUSHE*

*MALLAM SHEHU AKARAMI* Sharahararren malamin Addini ne wanda yayi suna abangaren koyar da addinin Allah,Shidin ya kasance Basakawwace ne dan Asalin garin Birnin kebbi,akaramar hukumar kangiwa awani gari da”a kekira Arewa local Goverment,karatu da neman ilimi ya barosa daga garinsu,sakamakon duka mahaifanasa Allah ya amshi kayansa,yayi yawon garuruwa inda yayi karatun Allo har zuwa sauka ya karanta littafai babu adadi kafin Allah ya jehosa garin Zaria.

  Agarin na zaria ya samu masaka wajen wani malaminsa wanda ya karisa saura karatun littafai awajensa,sunyi zaman amana tare dashi,Shima malamin ba”arene wato Shima bassakwaceni ,kuma har dangin Shehun yaje,wannan dalilin ne ya saa ya auramasa diyarsa daya tilo Aisha ido,Bayan Aurensu anan zaria suka cigaba da zama,basu dade da Aure ba Allah yayima mahaifin indo rasuwa,baiyi Shekara ba matarsa ta bisa,koda aka raba gado gabadaya dukiyan da gonaki da aka mutu aka barmata duk ta mallakama mijinta Mallam Shehu wanda yagaji mahaifinta ya cigaba da koyar da almajirai karatu daga garuruwa dadama,yakasance mazaunin cikin zaria cityne Akwarbai.

  Gonakin sai yadinga Noma dasu,yana hadawa da kiwon Dabbobi domin dogaro dakai,..Bayan Aurensu sai mtsalan wabi ta biyo baya duk ya”yan da indo ta haifa da anyi suna sai sukoma ga mahallicinsu,sai da tayi takwas basu tsaya wa,har sun Fidda rai sai gashi Sun Haifi Bala,wanda basu ma sakaran zai Rayu ba sai gashi ya rayu,Shekaranshi Bakwai Aduniya Indo ta sake haihuwan Suwaiba,wanda tun daganan bata kara haihuwa ba,sai suka godema Allah bayan sun tattara ya”yansu guda biyu da Allah ya basu suka rikesu..

Koda aka haifi Suwaiba bala ya haddace alqur”ani,itama tana tasowa itama Mallam baiyi wasa da karatunta ba,Bala yayi karatun primary sch dinsa awata makaranta mai Suna Zaria acadmy,anan kuma yayi secondary sch dinsa,yana kammallawa ya fada ABU ZARIA inda yake karantar Political Science,Ayayinda Lokacin Suwaiba take SS1 anan Zaria acadmy din,itama kafin asakata mkrantar boko sai da ta haddace Qur”ani tana biya sauran littafi.

ABDULNASEER TAMBARI BUZU..”Wani Buzu ne wanda ya fado garin zaria akuma gidan Mallam Shehu akarami,Domin neman ilimi,Mallam Shehu ya amasheshi hannu bibbiyu Tunda dama yana amsan baki daga wasu kasashen kusa da Nigaria kamar su cameron da Chadi da Niger din,Babu Abunda mallam ya sani nashi sai Shi din mutamin Niger ne,ayanki agadez Sai kuma Sunanshi da suka sani,wajen shakaransa tara tare da mallam Tuni ya Sauke qur”ani yayi haddansa yakoma yanabin sauran litttafai,Shakuwa tare da sabo Tuni yayi da mallam da iyalansa bala da Suwaiba suna kallonsa ne,amatsayin dan’uwa ba almajirin mallam ba,Shiko mallam Shehu akarami yayi Shaku da Abdulnaseer sosai yakuma jarabasa ta hanyoyi dadama inda ya fahimci yana da amana da hankali bashi da mtsala ko kadan,shiyasa yasaki jiki dashi harda harkan Dukiyansa data iyalansa yana da masaniya,sai yazama shalelen malam Domin ma,sauran almajiran da Dan mallam sukemai lakabi,kwatsam batare da shawara da kowa ba Mallam Shehu Akarami ya Daurama Abdulnasser Tambari buzu Da Diyarsa Suwaiba aure Ranar datayi candy dinta Daurin Aure daya hada mutane biyar cur,daga mallam Shehu sai Abdulnaseer din,sai wani Abokin mallam din sai wasu manya daga cikin almajiran mallam din guda biyu,azauren gidan nasa,wanda mallam din da kanshi ya biya sadakin Auren nasu,Abdulnaseer shikanshi baida masaniyar Auren sai da aka kullashi kana kowa yaji,da farko bala ne dayazo Hutun Semister yaso yayi gaddama game da Aure,duba da Aure ba mganar wasa bace,taya ya za”a bama mutum aure batare da sanin asalinshi ba ko sanin wasu daga ciikin danginsa ba,ammh sai Mallam ya tausheshi da cewa lokaci kadan yake jira zasu dumguma dukkansu zuwa chan Niger din domin ganin ahalin Abdulnaseer din,Duk da bala bai wani gamsu ba,ammh sai ya share,saboda yana daraja mahaifinsa bazai iya sa”insa dashi ba,itako indo bata wani Damu ba,domin mijinta yayimata bayani,ita kuma Duk duniya babu wanda take gani da kima da daraja irin uban ya’yanta Shiyasa tabashi goyon baya dari bisa dari..

    

Abagaren Suwaiba kuwa bata wani ji wani irin ba,lokacin da Mallam yatarasu yake fadamusu,sai ma sunne kai datake tana satan kallon Abdulnaseer din,wanda kwata kwata baya da muni,Fari ne mai kalan ja,dogo ne karkarfan Namiji gashin kansa a nannade kallo daya zakamai kasan buzu ne gaba da baya,yana da kyau na daukan hankali,domin ko a anguwa yana fama da yanmata kai harda zawarawa,ciki harda manya mata wa”inda suka kusa haihuwansa,in suka gansa,kyansa yana Rudansu sukai ma tayi,ammh sai ya taka musu birki,Shima abarayinsa baiji yana kin Suwaibarba Domin bata da muni ko kadan itama doguwa ce,ammh kuma baka ce ita,tana kyanta babu laifi wanda kyan nata mai dauke dawani Sirri ne,sai da wanda yakaremata kallo yake fahimtar haka,Mallam Shi yayi alqawarin gina musu gida su tare nan Filin dake gaban nasu yasa aka tada gini,Ganin haka yasa in akayi abinci sai indo ta umarci Suwaiba data dinga dauka tana kaiwa mijinta adakinsa na zaure,to kusan sha”anin miji da mata,kuma gashi suna son juna,daya nemeta batayi yunkurin hanashi ba tabashi kanta,Ranar da Abun ya faru duk Nuku nukun Suwaiba sai indo ta gane saboda budurci ba wasa bane,ta rude ita da kanta tagasa yarta ammh kuma Abunda ya faru bai mata dadi ba batason mai zatacema Mallam ba,don yana mata fadan barinsu suna kebewa yace yafison koma miyene,in aka kammalla ginin Zasu je chan Niger sukaga dangin Abdulnaseer din in sundawo sai su bashi matarshi koma miye zai faru alokacin babu damuwa..,Indo boyewa mallam tayi bata bari yaji komai ba,balle Ya Fahimci wani Abu,sai dai tayima Suwaibar jan ido,tare da tsoratar da ita,akan tana sake bashi kanta zatayi ciki,kuma in mallam yagani sai ya bata mata Rai,jin haka yasa Suwaiba ta tsorata koda mijin nata yakara nemanta sai tayi gaddama,ammh kusan sha”anin rayuwa,dakuma karfin soyayyar miji da mata,da kanta takai kanta komai ya afku,ammh wannan karan bata bari indo ta fahimta ba,watansu biyu da aure Mallam ya kammallah Shirin tafiya Niger wajen Dangin Abdulnaseer din,sai me Ranar kwatsam Daga mallam ya aiki Abdulnaseer kasuwa da kudade kimanin Dubu dari biyu,yakaima wani abokin kasuwancinsa,zai tafi saro awakai ne,kuma shi ga wannan Tafiyan sai sukayi mgana kan yabashi sakon shi zai je ya siyomai,daman Abdulnaseer ke zuwa,jin haka yasa yabawa Abdulnaseer kudin ya tafi kaima mutumin,Ammh Abun mamaki Tun safe yafita har dare babu lbrinsa,Mallam hankalinsa yatashi yakira Abokin nasa ya tambayesa ko Abdulnaseer yazo,Abunda yabama kowa mamaki cewan dayayi tun safe dayace zai aikosa yake jiransa ammh shuru,hankula fa suka tashi har aka kwana babu lbrin Abdulnaseer Tuni ,Suwaiba ta rasa sukuninta sai kuka takeyi,Abu tun anaganin wasa sai gashi an shafe sati babu lbrin Abdulnaseer duk inda mallam zai saka abincikamai an bincika ammh babu amo babu lbri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button