ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

Zabura jabir yayi ya duro daga gadon yana fadin”Me kake takama dashi?Kaki? Kai mallam kamar yadda alluran ke yawo ajikinka,haka take yawo ajikina,ko zamu gwada,billahil lazi sai na barar maka da hakoran gaba,karyan zama Shege kake..”yafada yana hararansa fuskarsa ahade,baya Aliyu yaja yana fadin”Ubanka zanji u already know me ko”?yafada yana wucewa jikin wardrope dakin, yana kokarin budewa,da harara jabir ya rakasa yana fadin”wlh an ma Cuci marainiyar Allah,An hadata da Da”n iskan Soja kawai,ai daka tsaya kaga yadda zan sauyama kammanin..”Dariya Aliyu yayi yana fadin”Sai kaje kafadamusu su kwance auren su auramaka tunda kai ba Da’n iska bane,tunda na lura u are jealous,.’ko kallonsa Jabir baiyi ba ya fada Tiolet,yana kunkuni yana fadin zai zane Aliyu da daddaren nan,shiko yana jinsa yamasa banza,sai ma jallabiyansa daya zura ya Shimfida darduma Ya Tada salla,shiko jabir koda ya fito shima Daure da alwal,shima sallar ya tada,kowa yana nashi ko wajen kwanciya sai da suka buga,harda Ture ture agado kamar wasu yara,dat how Captain Aliyu and captain jabir Art when they are together,kuma basu iya rabuwa da juna,ko cikin bariki suna tare,ammh kuma kowanne yanajin kansa awani Shege ne…

     ******** 

    “Ni”ima kuwa cikin mawuyacin hali aka kaita Asibiti,likitoci suka amsheta da gaggawa zuwa emargency Sun ci bakar wahala kafin su daidaita numfashinta,domin jninta yayi bala”in hawa,ga zuciyarta ta buga sakamakon wani Abu dataji wanda yayi matukar razanata,kuma zuciyarta ta Firgita da Abun,yanzu koma miye,ayi kokarin ganin An magancemata matukar ana son Rayuwarta ta Daidaita.

   Bayanin da likita yayi masa su mami kenan da kwamishina,wanda tunda likita ke mgana,zufa ke ketomai sai yanzu nadamar Abunda ya aikata yazomai,sam baiyi Duba da halin da tilon yarsa zata tsinci kanta aciki ba,kawai yana hango kada yabata rayuwar yarsa ne da zuru”arsu,kallon sa Mami tayi tana Tsiyayan hawaye tace”Kaji ko,Haba Ranka shi dade,tayama za”ayi kafara yanke wannan hukunci batare da ka shawarceni ba,ni da ka kirani dana fadama zakayi kuskure domin Ni’ima bazata iya rayuwa babu Aliyu ba,tana mugun sonshi,tariga data sallama ma kanta yau zata zama matarsa,ammh duk ka ruguza komai,na shiga uku ni Jamila,bani da kowa sai ke Ni”ima tabbas bazan zura ido,kishiga wani hali ba,ni zani gidansu Aliyun dakaina na roke mahaifiyarsa yadawo ya aureki..”Tafada tana mikewa,da sauri kwamishina ya rikota yana fadin”Mamin Ni’ima where are u going? kidawo wannan ba mafita bace,infact ma yanzu aka kirani aka shaidamin basu bar wajen ba,Sai da aka Daurama Shi Aliyun Aure,kinga kenan ko kinje bazasu saurareki ba..”Kallonsa tayi hawayenta na zuba tace”Kaji ko? innalillahi wa’inna Alaihirraju’un wake da karfin gwiwan Tunkarar Ni”ima da wannan mganar,nidai bani dashi,wlh bani dashi..”Tafada tana kuka lokaci daya tana sulalewa daga jikinsa,Rumgumeta yayi yana bubbuga bayanta yake fadin”Banyi Tunanin haka,Sulaiman ne,ya dake kan baza”a Daura ba sai Dangin ubansa sunzo,wlh koni rainq babu dadi,shine ya dage,kuma kinga shine waliyinta bai kamata na tsinkashi cikin jama”a ba..”Dago kanta tayi tana fadin”Ka tsinka shi manq,say what,bakai bane gaba dashi ba,ai gashinan ya zugaka ka aikata Abunda yazo ya damemu,an barmu da wahalan zuciya data sarari,wlh Allah sai ya sakamana kan Abunda yayimana,kuma hakkin Ni”ima bazai taba barinshi ba..”Tafada tana fizge jikinsa,ta fito daga office din tana share kwallah,likita kuwa daman Ficewa yayi ya barsu,dafe kansa kwamishina yayi,kunyar Duniya da Nadama sun kamasa,itako Mami tana fita Munari tataso tana fadin”Mami ya jikin Sweetheart? tafada cikin damuwa,Wani kallon Mami ta watsama yan sanda take kare lafiyan kwamishina,lokaci daya suka fashe,ada sun kasa kunne ne suji mai zatace,hannunta Kawai mami takama suka koma suka zauna kantace”Komai ya dagule Muneera,don likita ya gayamana cewa zuciyar Ni’ima tayi Rauni,gashi kuma jninta yayi bala”in hawa,ceto rayuwarta shine bata Abunda takeso..”Dafe kai Munari tayi kantace”To Mami mai zai hana muje gidansu Soja mu gayamusu halin datake ciki ko Allah yasa zasu Taimaka ya aureta yanzu..”Girgiza kai Mami tayi kan tace”Hmm,ai bakin alkalami yari gaya ya bushe,muneera,kuma dama ance oppourninty comes one in life,ko kinmata,wajen su sukazo nema,kuma muka tozartasu gaban dimbin jama”a,Armm amaganar damuke ma yanzu basu tashi taron ba,sai da aka Daurama Aliyu aure,tayaya kike ganin zasu kallemu in mukaje musu da wannan bukatan,ai banajin zamu samu kyakayawan kallo,saboda mu muka saki damarmu..”Sadda kai munari tayi tana sharan kwallah takasa fadin komai,kawai jinjina al”amarin take,tanq ayyana yadda Ni’ima zata karaji matukar taji Sojanta yayi Aure,Mami kuwa tagumi tazabga,tana Tunanin mafita,Shiko kwamishina bai koma gida ba,sai da aka kawo Ni’ima daki na mussaman domin hutu,Mami ta bishi suka koma gida,don ta tahomata da kayanta da kuma tasaka masu aiki suyi girke tataho dashi.

______________

  Azeema bata yi sanyi da jikinta ba,sai da tagama duka aiknta na tsakar gida,kafin takoma ta daura girki Tuwo da miyar kuka,tanayi tana shiga Tunanim yadda makomar rayuwartake,ita gani take kamar amafarki wai itace matar Aure,matar auren ma mata ga yaya Captain? Abun nabata mamaki,ammh sanin bata da wanda zata fadama damuwarta yasa ta ijiye komai gefe daya ta cigaba da aikinta,Ramatu kuwa sau daya ta leko waje,tagani ko Azeema na aikinta samunta tayi lokacin ma tana tsalge,kwafa tayi takoma dakina,tana zaginta ita da Babanta tana fadin”kwadayayyu kawai,watarana sai kwadayi ya kashesu..”itadai ko Tak batace ba saboda inda sabo yaci ace ta saba da Halin Inna Ramatun..

Azeeza kuwa kuryan Daki ta shige ta haye gado tana kuka wurjajan saboda bakin ciki da kishi kamar ya kasheta,gawani tsanar Azeema dayakara tasiri aranta,yanzu ace Tayi shekara da shekaru tana Rainan Soyayyar yaya Captain Aranta,ta wahala akan Sonshi tagama tsara yadda zasu gudanar da rayuwarsu,ammh lokaci daya mafarkinta yatashi abanza,koda Yaya captain zai aure,Ni’ima tayi kuka,ammh zuciyarta bata kusa bugawa ba sai da taji ance Adda Azeema ya aura”Bala”i batajin ko sama da kasa zasu hade zata iya barma Azeema Sojanta,domin tayi alkwarin matukar Tana raye agidan Duniya sai ta Aure yaya Captain koda hakan zaiyi sanadiyar salwartar da rayuwar Azeemar ce ita babu ruwanta,kanta kawai ta sani,Koda Inna Ramatu ta shigo ta ganta tana kuka idanunta sunyi jawur,cemata tayi kanta ke ciwo,jiki na rawa inna Ramatu ta ballo panadol ta bata ta sha takoma ta kwanta lamo tana saka yarda zata wargaza rayuwar Azeema don yanzu ita tafi tsana akan kowa..

Ana kiran sallar mangariba Azeema ta kammallah komai,ta zuzzubama kowa a muhallinshi,tayi alwala tashiga daki takabarta sallah ta idar kenan,taji sallamar Mallam lawal,da hanzari ta fito daga dakinsu tana fadin”Sannu da zuwa Baba..”kallonta yayi sanda take shinfadamai tabarma akofar Dakinsu Baiyi mgana ba,sai da ya zauna yace”Yauwa Azeematu diyar Albarka..”Yafada yana kallon Fuskarta sadda kanta tayi kafin ta mike tatafi randa ta debomai Ruwa cikin wani kofin sulba tazo ta ijiye kafin ta shiga kichen ta daukomai wasu kwanukan sulba na tuwo dana miya,tazo ta ijiye kafin takoma gefenshi ta zauna tana fadin”Baba ga ruwa kasha..”ta fada tana mikamai amsa yayi ya bude murfin ya kwafa kai yasha dayawa kafin yadago ya mikata yana fadin”Alhamdulillah,Allah yayi miki albarka Azeema..”Cikin jin dadi ta amsa da Amin,budemai tuwon tayi,ta zubamai ruwa ya wanke hannu yafaracin Tuwo,wanke hannunta tayi itama tasaka hannu sunacin Tuwon tare,wanda daman ko karfe nawa zai kai baidawo ba,Azeema bata iya cin abinci sai tare dashi,ta riga ta saba tun tana karama,Inna Ramatu tayi bala”in tayi tsiyan ammh duk bataci nasara ba itako Azeeza Abun na cinmata rai,shiyasa take fadin Baban yafison Azeema kuma ba karyabane kowani uba yanason da na gari mai hankali da Natsuwa da tarbiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button